23
Mar
Daga USMAN KAROFI Hukumar yaki da rashawa da sauran laifukan da suka shafi rashawa mai zaman kanta (ICPC) ta sanar cewa za ta kawo tsohon Gwamna Nasir El-Rufa’i gaban kotu a ranar Talata mai zuwa a Kaduna. Rahotanni sun nuna cewa El-Rufai yana tsare tun bayan ya amsa kiran hukumar EFCC a ranar 16 ga Fabrairu, 2026, inda aka yi masa tambayoyi na tsawon awanni 48 kafin ICPC ta ɗauke shi hannunta. Tsawaita zaman tsarewar El-Rufai ya haifar da cece-kuce, inda ƙungiyoyi da mutane da dama suka buƙaci a gurfanar da shi a gaban kotu ko a sake shi. Kakakin…
