ukarofi

12618 Posts
Shari’ar Kyari: Tsoffin fursunoni sun bayyana wa kotu yadda jami’an NDLEA ke taimakon su wajen safarar ƙwayoyi

Shari’ar Kyari: Tsoffin fursunoni sun bayyana wa kotu yadda jami’an NDLEA ke taimakon su wajen safarar ƙwayoyi

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Wasu mutum biyu da aka yankewa hukunci kan safarar miyagun ƙwayoyi, Chibunna Umeibe da Emeka Ezenwanne, sun bayyana a gaban kotu yadda wasu manyan jami’an Hukumar Yaƙi da Sha da Safarar Miyagun ƙwayoyi (NDLEA) suka taimaka musu su tsallake binciken tsaro a filin jirgin saman Enugu kafin jami’an rundunar binciken sirri ta ‘yan sanda su kama su. Mutanen biyu, waɗanda suka riga suka kammala zaman gidan yari na shekaru biyu, sun bayar da wannan bayani ne a cikin wani bidiyon shaidar furuci da aka nuna a gaban Mai Shari’a Emeka Nwite na Babban Kotun Tarayya da…
Read More
Dole a samu na’urar ATM ɗaya ga kowane katin biyan kuɗi 7,500 zuwa 2028 – CBN ga bankuna

Dole a samu na’urar ATM ɗaya ga kowane katin biyan kuɗi 7,500 zuwa 2028 – CBN ga bankuna

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya umarci bankuna da sauran hukumomin da ke fitar da katunan biyan kuɗi su faɗaɗa yawan na’urorin cire kuɗi ta ATM a faɗin ƙasa, inda ya tanadi cewa nan da shekarar 2028 dole ne a samu aƙalla na’urar ATM ɗaya ga kowane katin biyan kuɗi 7,500 da aka fitar. Sabon umarnin na kunshe ne cikin dokokin gudanar da na’urorin ATM a Nijeriya da CBN ta fitar, wanda ke nufin rage cunkoso, dogayen layuka da kuma matsalolin samun kuɗi a bankuna, musamman a manyan birane da yankunan karkara. A cewar dokar, dukkan hukumomin…
Read More
Hauhawar farashi ya ragu a Nijeriya – NBS

Hauhawar farashi ya ragu a Nijeriya – NBS

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Hukumar ƙididdiga ta ƙasa (NBS), ta sanar da cewa hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ta ragu zuwa kashi 15.06 cikin ɗari a watan Fabrairu 2026, daga kashi 15.10 da aka samu a watan Janairu. Rahoton duba farashi na CPI na watan Fabrairu da hukumar ta fitar a ranar Litinin ya nuna cewa hauhawar farashin gaba ɗaya ta sauka da kaso 0.04 cikin zari idan aka kwatanta daga wata zuwa wata. Wannan na nuni da cewa ƙaruwar farashin kayayyaki na ci gaba da raguwa a hankali, duk da cewa matsin tattalin arziki na nan. Sai dai rahoton…
Read More
CBN ya bayyana hanyoyin kare kai daga ’yan damfara

CBN ya bayyana hanyoyin kare kai daga ’yan damfara

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya yi kira ga duk masu hulɗa da bankuna a ƙasar da su kare bayanan kuɗinsu ta hanyar guje wa raba lambar sirri (PIN), kalmomin shiga da sauran bayanan banki masu muhimmanci da kowa, ko wane ne. Bankin ya fitar da wannan gargaɗi ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na hukuma na ɗ (tsohon Twitter), a matsayin wani ɓangare na bikin makon wayar da kan jama’a kan kuɗi na duniya na shekarar 2026, wato Global Money Week. A cewar CBN, wannan faɗakarwa ta zama dole ne sakamakon ƙaruwar damfara…
Read More
Tabaran zamani ya fallasa yadda ake cutar mutane a wasu gidajen mai

Tabaran zamani ya fallasa yadda ake cutar mutane a wasu gidajen mai

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta ya ɗauki hankalin jama’a bayan da ya nuna yadda wani mutum ya bankaɗo zargin yunƙurin damfara daga wata ma’aikaciyar gidan mai, wadda ake zargi da fara sayar masa da fetur daga mitar da ba a mayar sifili ba. A cewar mutumin, ya nemi a sayar masa da fetur na naira dubu ashirin (N20,000), amma sai ya lura cewa mitar famfon ta riga ta nuna N5,501 tun kafin a fara zuba man. Nan take ya ƙalubalanci ma’aikatan, yana zargin cewa ba su sake saita mitar zuwa sifili ba,…
Read More
Duk wani abu da za mu yi na gina KILAF AWARD tare da ‘yan Kannywood mun yi, amma kamar ba su shirya amsar sa ba ne – Muhammad Galadima

Duk wani abu da za mu yi na gina KILAF AWARD tare da ‘yan Kannywood mun yi, amma kamar ba su shirya amsar sa ba ne – Muhammad Galadima

Daga MUKHTAR YAKUBU  Taron bikin bajekolin finafinai na Afirka wato 'Kano Indigenous Languages of Africa Film Market and Festiɓal' wanda aka saba gudanar da shi a garin Kano a duk shekara, wanda a bana zai kasance shi ne karo na 9 tun daga lokacin da aka fara shiryawa. Babu shakka wannan taron ya kasance taro na farko da ake shiryawa a masana'antar finafinai ta Kannywood da ya shafe tsawon shekaru ana gudanar da shi ba tare da ya tsaya ba.  Kuma wannan wani abin alfahari ne da Kamfanin Moɓie Image bisa jagorancin Malam Abdulkarim Muhammad ya samar ga ci gaban…
Read More
Taron APC na ƙasa zai nuna haɗin kai da ɗa’a – Idris

Taron APC na ƙasa zai nuna haɗin kai da ɗa’a – Idris

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce babban taron jam’iyyar APC na ƙasa da za a yi zai nuna haɗin kai, ɗa’a, da sadaukarwa ga cigaban Nijeriya. Idris ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a Abuja a lokacin ƙaddamar da Kwamitin Yaɗa Labarai na Babban Taron APC na shekarar 2026. Ministan shi ne ɗaya daga cikin shugabanni biyu na kwamitin. Yayin da ya bayyana taron a matsayin “wani babban mataki” ga jam’iyyar mai mulki, Idris ya ce wannan dama ce ta ƙarfafa tsarin dimokiraɗiyya a cikin jam’iyyar da…
Read More
Ina kuɗin tallafi ke shiga? – ADC ta ƙalubalanci gwamnati kan taɓarɓarewar al’amura

Ina kuɗin tallafi ke shiga? – ADC ta ƙalubalanci gwamnati kan taɓarɓarewar al’amura

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Jam’iyyar ADC ta jefa tambaya kan yadda ake amfani da kuɗaɗen da aka ce an samu bayan cire tallafin man fetur, tana mai cewa farashin mai ya ƙaru da kusan kashi 500 cikin 100 tun bayan rantsar da Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a shekarar 2023. Sakataren Yaɗa Labarai na ƙasa na jam’iyyar, Bolaji Abdullahi, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a ranar Lahadi, yayin da yake mayar da martani ga sukar da jam’iyyar APC ta yi wa ADC.  A martaninta, APC ta zargi jam’iyyar adawa da yaɗa bayanan ƙage kan danganta ƙaruwar talauci zuwa…
Read More
2027: Tinubu ya bada wa’adi ga masu riƙe da muƙaman siyasa su yi murabus

2027: Tinubu ya bada wa’adi ga masu riƙe da muƙaman siyasa su yi murabus

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya umarci dukkan masu riƙe da muƙaman siyasa a gwamnatinsa da ke da niyyar tsayawa takara a zaɓen 2027 da su ajiye muƙamansu kafin ko a ranar 31 ga Maris. Umarnin ya dogara ne da tanadin Sashe na 88(1) na Dokar Zaɓe ta 2026, tare da jadawalin da INEC ta fitar domin shirye-shiryen zaɓen fidda gwani na jam’iyyun siyasa. A wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume, ya sanya wa hannu wadda Babban Sakatare na GSO, Ibrahim Kana, ya fitar an bayyana cewa umarnin ya shafi dukkan nau’ikan masu…
Read More
APC ta musanta amfani da ‘yan daba wajen kai hari ga ‘yan NNPP Kwankwasiyya a Kano

APC ta musanta amfani da ‘yan daba wajen kai hari ga ‘yan NNPP Kwankwasiyya a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano  Jam’iyyar APC a jihar Kano  ta musanta zargin da ake yi mata cewa tana da hannu a harin da aka kai wa mambobin NNPP a mazabar Ruwan Bago da ke ƙaramar hukumar Rogo. Hakan ya biyo bayan zargin da NNPP ta yi cewa wasu ’yan daba da ake zargin suna goyon bayan APC ne suka kai wa mambobinta hari yayin wani taron siyasa da aka gudanar a yankin. A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi, reshen APC na jihar Kano ya bayyana zargin a matsayin marar tushe, yana mai cewa NNPP na…
Read More