25
Mar
Daga USMAN KAROFI Hukumar yaƙi sa cututtuka masu yaɗuwa ta Najeriya (NCDC) ta bayyana cewa cutar sanƙarau na ƙara ƙamari a jihohin Arewacin ƙasar, inda masana kiwon lafiya ke gargaɗin cewa alluran rigakafin da ake da su a yanzu ba sa bayar da cikakkiyar kariya ga nau’in cutar serogroup C da ke yaɗuwa cikin sauri. Rahotanni sun nuna cewa yara masu shekaru daga ɗaya zuwa 15 su ne suka fi kamuwa da cutar, yayin da cunkoson jama’a da iska mai ɗauke da ƙura a lokacin rani ke ƙara haɗarin yaɗuwar cutar a yankunan da ke cikin meningitis belt na Afirka.…
