ukarofi

12618 Posts
Kotu ta bada lasisin  ɗaukar bidiyon ’yan sanda a bakin aiki

Kotu ta bada lasisin  ɗaukar bidiyon ’yan sanda a bakin aiki

Daga MAHDI MUSA MUHAMAMD Kotun Tarayya da ke zamanta a birnin Warri na Jihar Delta ta yanke hukunci mai matu ƙar muhimmanci, inda ta tabbatar da cewa ’yan Nijeriya na da cikakken ’yancin Kundin Tsarin Mulki na zaukar hoto ko bidiyo na jami’an ’yan sanda yayin da suke gudanar da aikinsu a wuraren jama’a. Al ƙali mai shari’a, Mai Shari’a H. A. Nganjiwa, ya bayyana hakan ne yayin yanke hukunci a ranar Talata a shari’ar mai lamba FHC/WR/CS/87/2025. A cewarsa, wajibi ne jami’an ’yan sanda su ri ƙa sanya katin suna a fili tare da nuna lambobin su na aiki,…
Read More
Yunƙurin kafa ’yan sandan jihohi ya ƙara ɗaukar hankali a Majalisar Dattawa

Yunƙurin kafa ’yan sandan jihohi ya ƙara ɗaukar hankali a Majalisar Dattawa

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, ya karɓ i ba ƙuncin kwamitin jagoranci na Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya da aka kafa domin tsara tsarin kafa ‘yan sanda na jihohi. An bayyana hakan ne a lokacin wata ziyarar girmamawa da kwamitin ya kai masa domin neman shawarwari da gudunmawar Majalisar Dattawa kan wannan muhimmin aiki na  ƙasa. Tun a ranar 4 ga Maris, 2026, Babban Sufeto Janar na ‘yan sanda, Olatunji Disu, ya aaddamar da kwamitin mutum takwas da aka  ɗora wa alhakin tsara yadda za a kafa ‘yan sanda na jihohi a Nijeriya. Kwamitin,  ƙar ƙashin…
Read More
Rigakafin  ƙanjamau: Nijeriya ta karɓi allurai guda 11,520

Rigakafin  ƙanjamau: Nijeriya ta karɓi allurai guda 11,520

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Nijeriya ta karɓi kashin farko na allurai 11,520 na maganin Lenacapavir, wani sabon magani mai  ɗorewa da ake amfani da shi wajen rigakafin kamuwa da cutar HIV , wanda Asusun Global Fund ya bayar. An gudanar da bikin mi ƙa maganin ne a ranar Laraba a Babban Ma’ajiyar Kayan Lafiya ta Tarayya da ke Oshodi a jihar Legas. Lenacapaɓ ir magani ne da ake yi sau biyu kacal a shekara, kuma Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta amince da shi a matsayin wani  ƙarin zaɓ i a cikin hanyoyin rigakafin HIɓ . Ana sa…
Read More
Sallah: Sojoji sun yi gargaɗi kan ƙaruwar hare-haren ta’addanci a Arewa

Sallah: Sojoji sun yi gargaɗi kan ƙaruwar hare-haren ta’addanci a Arewa

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Rundunar haɗin gwiwa ta sojojin Nijeriya a yankin Arewa maso Gabas, Operation Hadin Kai, ta fitar da muhimmin gargaɗi ga al’umma kan yiwuwar ƙaruwa hare-haren ta’addanci yayin bukukuwan ƙaramar Sallah bayan kammala azumin watan Ramadan. Wannan gargaɗi ya biyo bayan wasu hare-haren ƙunar baƙin wake da suka faru a birnin Maiduguri, Babban Birnin Jihar Borno ne, inda suka shafi yankin Kasuwar Litinin, yankin Ofishin Gona (Post Office) da kuma ƙofar Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri. A cikin wata sanarwa da Jami’in Yaɗa Labarai na rundunar, Laftanar Kanal Sani Uba ya rattaba wa hannu, sojojin sun bayyana…
Read More
Sallah: FRSC ta ƙaddamar da shirin tsauraran sintiri domin daƙile haɗurran mota

Sallah: FRSC ta ƙaddamar da shirin tsauraran sintiri domin daƙile haɗurran mota

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Hukumar Kiyaye Haɗurra ta ƙasa (FRSC), ta sanar da ƙaddamar da wani gagarumin shirin sintiri na musamman domin bukukuwan ƙaramar Sallah na shekarar 2026, a wani mataki na ƙara tsaurara matakan tsaro da rage haɗurra a manyan hanyoyin ƙasar. Babban Kwamandan Hukumar, Shehu Mohammed, ne ya bayar da wannan umarni, inda ya buƙaci a tura jami’ai da kayan aiki zuwa sassan ƙasar baki ɗaya daga ranar 17 zuwa 22 ga watan Maris domin gudanar da wannan aiki na musamman. Ya bayyana cewa, wannan mataki na daga cikin ƙoƙarin da hukumar ke yi na rage yawan haɗurran…
Read More
Me zai iya biyo bayan ƙaurace wa taron APC da sanatocin Kebbi suka yi?

Me zai iya biyo bayan ƙaurace wa taron APC da sanatocin Kebbi suka yi?

Daga JAMIL GULMA a Kebbi  Sanatoci uku da suka yi gudun hijira, don neman mafaka da matsayi a Jam'iyyar PDP bayan da Jam'iyyar APC ta fatattake su a fakaice kafin babban zaɓen da ya gabata a shekarar 2023, waɗanda kuma bayan PDP ta karɓe su hannu biyu, inda ta ba su takara kuma suka ci zaɓe, sannan suka sake dawo wa APC, sun ƙaurace wa taron zaɓen shugabannin jam’iyyar na jiha da aka gudanar a Birnin Kebbi, babban birnin jihar, ranar Talatar makon jiya. Sanatocin dai sun haɗa da Adamu Aliero mai wakiltar Kebbi ta Tsakiya, Yahaya Abdullahi mai wakiltar…
Read More
Nijeriya ba ƙashin yarwa ba ce, inji Sarki Charles

Nijeriya ba ƙashin yarwa ba ce, inji Sarki Charles

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Ziyarar aiki ta tarihi da Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya kai ƙasar Birtaniya ta kai ƙololuwa a ranar Laraba, yayin da shi da Sarkin Birtaniya, King Charles III, suka gabatar da muhimman jawabai a wata babbar liyafar gwamnati da aka shirya a Fadar Windsor da ke Ingila, inda sarkin ya bayyana Nijeriya a matsayin ƙasar da ba ƙashin yarwa ba. Rahotanni sun nuna cewa taron, wanda ya samu halartar manyan ‘yan gidan sarauta ciki har da Sarauniya Camilla da Yarima William tare da Catherine, Yariman Wales, ya sake jaddada dangantaka mai ƙarfi da tarihi tsakanin…
Read More
A wata ɗaya na aurar da marayu 24 — Sarauniyar Hausawan Afirka

A wata ɗaya na aurar da marayu 24 — Sarauniyar Hausawan Afirka

Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano Sarauniyar Hausawan Afirka, Amb. Dakta Hajiya Umaimatu Muhammad, wacce aka fi sani da Uwar Marayu, ta bayyana cewa a cikin watan Disamba da ya gabata kaɗai ta aurar da marayu guda 24, a wani ɓangare na ƙoƙarinta na tallafa wa marasa galihu a cikin al’umma. Ta bayyana hakan ne yayin da take jawabi kan yadda ake inganta rayuwar marayu da masu ƙaramin ƙarfi, inda ta ce har yanzu ba ta da ƙididdigar adadin marayun da take tallafawa, amma tana ci gaba da taimaka musu gwargwadon iko. A cewarta, “Wannan hidima ta marayu tana ba ni…
Read More
Kammala azumin Ramadan dama ce ta addu’a don kawo ƙarshen gobara a Kano — Sarkin Kasuwar Beirut

Kammala azumin Ramadan dama ce ta addu’a don kawo ƙarshen gobara a Kano — Sarkin Kasuwar Beirut

Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano Sarkin Kasuwar Wayar Beirut da ke Kano, Alhaji Muhammad Inuwa Labaran, ya bayyana cewa kammala azumin watan Ramadan wata babbar dama ce ga al’umma su ƙara dagewa wajen yin addu’o’i domin samun kariya daga bala’o’i, musamman yawaitar gobara a kasuwannin jihar Kano da ma sauran sassan ƙasar. Ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga manema labarai, inda ya ce addu’a ita ce hanya mafi inganci wajen magance irin waɗannan matsaloli da ke addabar al’umma. Ya kuma miƙa sakon jajensa ga waɗanda gobara ta shafa a kasuwannin Sabon Gari, Dakata da kasuwar waya, tare…
Read More
Sallah: NSCDC ta tura sama da jami’ai 3,400 domin samar da tsaro a Kano

Sallah: NSCDC ta tura sama da jami’ai 3,400 domin samar da tsaro a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano  Hukumar tsaron fararen hula da kadarorin gwamnati ta ƙasa (NSCDC) reshen jihar Kano ta tura sama da jami’ai 3,400 a faɗin jihar domin tabbatar da tsaro kafin, yayin da kuma bayan bukukuwan Eid-el-Fitr. Kwamandan hukumar a jihar, Hassan Mohammed Agalama, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Talata, inda ya ce matakin na daga cikin shirye-shiryen da aka yi tun da wuri domin kare muhimman kadarorin ƙasa da kuma tabbatar da zaman lafiya a lokacin bukukuwan a jihar. A cewarsa, an jibge jami’an a wuraren sallar Idi, wuraren shakatawa,…
Read More