ukarofi

12715 Posts
Next Moonshot: Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da shirin bai wa ɗalibai masu ƙirƙira tallafin miliyan N50

Next Moonshot: Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da shirin bai wa ɗalibai masu ƙirƙira tallafin miliyan N50

Daga IBRAHIM HAMISU Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta ƙaddamar da sabon shirin tallafa wa ƙirƙire-ƙirƙiren ɗalibai da ake kira Student Venture Capital Grant (S-VCG), wanda ke bayar da tallafin Naira Miliyan 50 ba tare da ɗaukar kaso daga jarin kamfani ba. Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa, ne ya sanar da hakan a wani taron manema labarai a Abuja, inda ya ce shirin na daga cikin ginshiƙan Renewed Hope Agenda na gwamnatin Shugaba Bola Tinubu domin farfaɗo da harkokin ƙere-kere a jami’o’i da kwalejojin ƙasar. Shirin zai baiwa ɗalibai da ke da ƙirƙira a fannoni kamar kimiyya, fasaha, Injiniya, lissafi da…
Read More
Shugaban ƙaramar hukumar Katsina ya ƙaddamar da aikin ginin asibitin yara

Shugaban ƙaramar hukumar Katsina ya ƙaddamar da aikin ginin asibitin yara

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina A mataki na tabbatar da ingantacciyar kula da lafiyar al’umma, shugaban ƙaramar hukumar Katsina, Hon. Isah Miqdad AD Saude, ya ƙaddamar da aikin gina asibitin yara da mata masu juna biyu a mazaɓar Wakilin Arewa A. Shugaban wanda ya sami wakilcin shugaban majalisar kansilolin ƙaramar hukumar Katsina, Hon. Ishaq Tasi’u Modoji, ya bayyana cewa aikin gina wannan asibiti na daga cikin manufofin gwamnatin ƙaramar hukumar wajen sauƙaƙa wa mata masu juna biyu da ƙananan yara wajen samun kulawar lafiya a kusa da su ba tare da dogon tafiye-tafiye ba. Shima kansilan mazabar wakilin Arewa A,…
Read More
JIBWIBS a Katsina ta ƙalubalanci naɗin sabon shugaban hukumar zaɓe na ƙasa

JIBWIBS a Katsina ta ƙalubalanci naɗin sabon shugaban hukumar zaɓe na ƙasa

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina A wata takardar sanarwa ɗauke da sa hannun shugaban ƙungiyar Izalatul bidi'a wa Ikamatul sunnah reshen jihar Katsina Sheikh Yakubu Musa Hassan Sauttus sunnah ya sanya hannu, ƙungiyar ta nuna mamaki da damuwa dangane da naɗin Farfesa Amupitan Joash. Sanarwar ta ce ƙungiyar ta nuna kaɗuwar ta akan naɗin saboda maganganu marasa tushe da makama da yayi a shekarar 2020 inda ya gabatar da wata ƙasida da ya buga mai taken "LEGAL BRIEF". Sheikh Yakubu Musa ya bayyana cewa Farfesa Joash yayi zarge zarge marasa tushe da suka ƙasƙantar da cin mutuncin Musulmin ƙasar. Ya…
Read More
Shin akwai ra’ifin hadisi a cikin Sahihul Bukhari?

Shin akwai ra’ifin hadisi a cikin Sahihul Bukhari?

Daga ALI ABUBAKAR SADIQ Wannan ce tambayar da na ci karo da ita a majalisin limamin masallacin Al-Furqan, Dr Bashir Aliyu. Tashin farko ya fara bayar da amsar cewa babu ra’ifin hadisi a cikin Bukhari, amma idan wani na ganin da akwai, to, ya kawo. Sannan ya ɗora da cewa, shehin malamin hadisi, Al-Juwayni, wanda aka fi sani da Imamul Haramain, ya ce, idan wani ya rantse akwai hadisi ra’ifi a Bukhari, to matarsa ta saku sakamakon wannan furuchi. Wannan Makala zata yi nazarin wannan da’awa. Jamhurun Musulmin Duniya, idan ban da ‘yan Shi’a da mabiya Qur’ani zalla, duk sun…
Read More
Bankin Standard Chartered zai rufe asusun ’yan Nijeriya marasa ajiyar miliyan N7.5

Bankin Standard Chartered zai rufe asusun ’yan Nijeriya marasa ajiyar miliyan N7.5

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Bankin Standard Chartered ya sanar da cewa daga ranar 28 ga Fabrairu, 2026, ba zai ci gaba da mu’amala da abokan hulɗar da ba su da aƙalla Naira miliyan 7.5 a cikin asusunsu ba — bisa wani sabon tsari da bankin ya ƙaddamar mai suna 'Emerging Affluent Segment'. A wata sanarwa mai taken “Muhimmin Sanarwa: Sauye-sauye a Rassa da Tsarin Hulɗar Abokan Ciniki," bankin ya bayyana cewa asusun da ba su kai wannan ƙa’ida ba za a rufe su kai tsaye daga ranar da aka ƙayyade. Bankin ya bayyana cewa ya cire sashen 'personal banking', wanda…
Read More
Lauya ya bayyana tsarin da zai haɓaka Nijeriya zuwa Naira kwadriliyan 1.5

Lauya ya bayyana tsarin da zai haɓaka Nijeriya zuwa Naira kwadriliyan 1.5

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Shahararren lauya kuma masanin tattalin arziki, Dokta Olisa Agbakoba (SAN), ya bayyana wani shirin sauyi na dogon lokaci da zai iya haɓaka darajar tattalin arzikin Nijeriya zuwa fiye da naira kwadriliyan 1.5 cikin shekaru goma zuwa goma sha biyar masu zuwa, idan aka aiwatar da shi yadda ya dace. A cikin wata wasiƙa da ya aike wa Ministan Kuɗi kuma Mai Tsara Tattalin Arziki, Agbakoba ya yi kira ga gwamnati ta faɗaɗa damar samun bashi, ta ƙarfafa ingantaccen aikin gona na zamani, tare da yin gyaran dokar amfani da aasa (Land Use Act) domin buɗe sabbin…
Read More
Adadin masu amfani da lantarki ya ƙaru zuwa miliyan 11.96 – NERC

Adadin masu amfani da lantarki ya ƙaru zuwa miliyan 11.96 – NERC

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Hukumar Kula da Lantarki ta Nijeriya (NERC) ta bayyana cewa, adadin masu amfani da wutar lantarki a ƙasar ya ƙaru daga miliyan 11.89 a watan Yuli zuwa miliyan 11.96 a watan Agusta 2025. NERC ta sanar da hakan ne a sabon “Metering Factsheet” da ta wallafa ta shafukanta na ɗ (Twitter) da Instagram a ranar Litinin, inda ta ce sabbin bayanan sun haɗa da dukkan kamfanonin rarraba wuta 11 da ke faɗin ƙasar. A cewar hukumar, masu amfani da na’urar mita sun kai miliyan 6.58, abin da ke nuna cewa an kai kaso 55.01 na masu…
Read More
Yanzu muna da ƙaƙƙarfar dokar gurfanar da masu haddasa rushewar bankuna – NDIC

Yanzu muna da ƙaƙƙarfar dokar gurfanar da masu haddasa rushewar bankuna – NDIC

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Hukumar Inshorar Masu Ajiyar ta ƙasa (NDIC) ta bayyana cewa yanzu tana da ƙaƙƙarfan doka wacce za ta ba ta damar gurfanar da masu hannu a rushewar bankuna cikin ƙwarewa da ƙarfi, bisa sabon tsarin doka da aka amince da shi. Shugaban hukumar, Thompson Oludare Sunday, ne ya bayyana haka lokacin da yake karɓar tawagar ƙungiyar Masu Kula da Farfaɗowar Kasuwanci (BRIPAN) ƙarƙashin jagorancin shugaban ta, Chimezie Victor Ihekweazu (SAN), a hedikwatar NDIC da ke Abuja. A cewar Sunday, sabuwar dokar NDIC mai lamba 30 ta shekarar 2023, tare da dokar Bankuna da ƙungiyoyin Kuɗi ta…
Read More
Kamfanonin lantarki sun sanya mitoci 70,888 ga sabbin kwastamomi a Agusta – NERC

Kamfanonin lantarki sun sanya mitoci 70,888 ga sabbin kwastamomi a Agusta – NERC

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta ƙasa (NERC) ta bayyana cewa Kamfanonin Rarraba Wuta (DisCos) sun sanya mitoci ga aƙalla sabbin abokan ciniki 70,888 a watan Agusta 2025. Hukumar ta bayyana hakan ne a cikin rahoton “Metering Factsheet” na watannin Yuli da Agusta 2025, wanda aka wallafa a shafinta na yanar gizo a ranar Litinin a Abuja. A cewar rahoton, sabbin mitocin da aka sanya a watan Agusta sun ragu idan aka kwatanta da 76,783 da aka saka a watan Yuli, alamar ci gaba a ƙoƙarin samar da mitoci a cikin masana’antar wutar lantarki ta Nijeriya…
Read More
Jami’ar Bingham ta yi bikin cika shekaru 20 da kafuwa

Jami’ar Bingham ta yi bikin cika shekaru 20 da kafuwa

Daga JOHN D. WADA a Lafia Babbar jami'ar nan mai zaman kanta da ake kira Bingham University da ke Auta-balaifi a ƙaramar hukumar Karu jihar Nasarawa ta gudanar da taron cikar ta shekaru 20 da kafuwa tare da babban bikin yaye wasu ɗaliban ta waɗanda suka kammala karatun digiri din su da waɗanda suka kammala na gaba da digiri da PhD da sauran su karo na shida wato convocation ceremony kenan a turance. An gudanar da bikin ne a ranar Asabar na mako da ya gabata a cikin babban ɗakin taro na jami'ar da ake kira University Chapel kuma an…
Read More