19
Nov
Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe Wata gobara ta tashi a daren Talata zuwa safiyar Laraba a kasuwar tsofaffin ƙarafa da katako da ke Gombe, inda ta ƙone shaguna fiye da 30 tare da lalata dukiya mai darajar miliyoyin naira. Shugaban ƙaramar hukumar Gombe, Barista Sani A.A. Haruna, ya ziyarci wurin tun lokacin da wutar ke ci, inda ya bayyana lamarin a matsayin babban rashi ga al’umma. Ya jajanta wa waɗanda abin ya shafa, tare da tabbatar musu da cewa hukumar ƙaramar hukumar za ta ci gaba da tallafa musu. Haruna ya kuma yaba wa mazauna unguwannin da ke kusa…
