ukarofi

12715 Posts
Cocin ERCC Solution Centre Masaka ta yi bikin cika shekaru 10

Cocin ERCC Solution Centre Masaka ta yi bikin cika shekaru 10

Daga JOHN D WADA a Keffi Shugaban Cocin Evangelical Reformed Church of Christ da aka fi sani da (ERCC) a turance Rabaran Dave Denji, ya jaddada muhimmancin haɗin kai tsakanin mambobin cocin gaba ɗaya domin samun cigaba da bunƙasar cocin. Ya bayyana hakan ne a jawabin sa a wajen wani gagarumin bikin cika shekaru 10 na ERCC solution centre dake garin Masaka a ƙaramar hukumar Karu Jihar Nasarawa ranar Lahadi. Wakilin mu ya ruwaito cewa anyi bikin ne domin tunawa da shekaru 10 da kafa majami'ar inda mambobin cocin da baƙi suka fito fili da tufafin su masu kyau suna…
Read More
Sanusi kaɗai muka sani a matsayin Sarkin Kano — Kwankwaso

Sanusi kaɗai muka sani a matsayin Sarkin Kano — Kwankwaso

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP a zaɓen 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya sake jaddada cewa Muhammadu Sanusi II shi ne kaɗai Sarkin Kano da aka amince da shi, yana mai cewa duk wasu da aka naɗa “daga Abuja ” ba su da wata karɓuwa a idon Kanawa. Kwankwaso ya yi wannan batu ne a yayin bikin yaye ɗalibai karo huɗu da Jami’ar Skyline University of Nijeriya ta gudanar a Kano ranar Asabar, inda ya ce gwamnatin jihar da al’ummar Kano sun amince da Sanusi shi kaɗai Sarki, sauran kuma “masu ikirari ne…
Read More
Gidauniyar Jihar Katsina ta kashe Naira miliyan 81 domin tallafa wa harkar Ilimi

Gidauniyar Jihar Katsina ta kashe Naira miliyan 81 domin tallafa wa harkar Ilimi

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Babban Sakataren Gidauniyar Alhaji Ahmed Ibrahim karfi ya faɗi haka a wajen bikin raba wasu kayan karatu da na gine gine ga wasu makarantun islamiyya da na alumma a jihar. Ya ce gidauniyar ta kashe waɗannan kuɗaɗe ne ga makarantun boko da na addini tun daga kafuwarta zuwa yau, a ƙarƙashin shirin tallafin ilimi na musamman. Ibrahim karfi ya bayyana cewa a wannan zangon tallafin na 2025, gidauniyar ta raba littattafan Islamiyya, tabarma (rubber mats), kayayyakin gini da kuma littattafan nuni ga makarantun Islamiyya, Alƙur’ani da na al’umma guda 12 da aka zaɓa daga kowace…
Read More
Matsalar Tsaro: Kalubalen malamai da fastoci

Matsalar Tsaro: Kalubalen malamai da fastoci

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Wani rahoto da kamfanin dillancin labarai na ƙasar Faransa (AFP) ya fitar ya bayyana yunƙurin da wasu shugabannin addini daga ɓangaren Musulmi da Kirista a Ƙaramar Hukumar Mangu da ke Jihar Filato, a shiyyar Arewa ta Tsakiya, suke yi don dawo da zaman lafiya da kyakkyawar zamantakewa a tsakanin al'umma a yankin. Sakamakon wani mummunan rikicin addini da ya auku a wannan ƙaramar hukumar a shekarar 2024, wacce mazauna cikinta ke da daɗaɗɗen tarihin zaman lafiya. Mazauna yankin na ganin hanyar samar da ɗorewar zaman lafiya ta dogara ne ga yadda malaman addini suka ba da…
Read More
Cin zafarin mata a masana’antun fim: Al’ada ko ɓata suna

Cin zafarin mata a masana’antun fim: Al’ada ko ɓata suna

Daga AISHA ASAS Cin zarafin mata a masana'antun fina-finai wani labari ne da ba ya tsufa, kuma yake yawan taka rawa lokaci zuwa lokaci, wanda a duk lokacin da ya taso yakan yi amon da za a ajiye komai a ba shi masauki na ɗan lokaci kafin a koma kan wasu ababen na daban. Kuma abinda ke ɗaure kai shi ne, a duk lokacin da ya taso a wata masana'anta sautinsa kan kai ga takwaranta ta wani ɓangare na duniya har ido ya kai can wanda zai yi wuya ba a samu wani koke a ɓangaren ba. Da wannan wasu…
Read More
Kungiyar Marubuta Labarin Wasanni ta bada babbar lambar yabo ga wakilin Manhaja, Abdullah Tanko

Kungiyar Marubuta Labarin Wasanni ta bada babbar lambar yabo ga wakilin Manhaja, Abdullah Tanko

Daga UMAR GARBA a Katsina  Kungiyar Marubuta Labaran Wassanni ta ƙasa (SWAN) ta bayar da mafi girman lambar yabo ga tsohon shugaban ƙungiyar reshen jihar Katsina kuma Wakilin Blueprint Manhaja, Kwamred Abdullah Mohammed Tanko.  Sakatariyar ƙungiyar ta ƙasa ce ta shirya bikin bayar da lambobin yabon a Abuja don girmama 'yan jarida na ɓangaren wasanni waɗanda suka ba da gudunmawa a lokuta daban-daban ga ci gaban ƙungiyar. Shugaban SWAN na Jihar Katsina, Kwamared Nasir Gide, wanda ya wakilci Abdullahi Tanko a bikin, ya miƙa masa lambar yabon ne a wani biki da ya gudana a Katsina. Ya bayyana gudunmawar Kwamred…
Read More
Kungiyar NUEE ta yi allawadai da matakin AEDC na sallamar ma’aikata 800

Kungiyar NUEE ta yi allawadai da matakin AEDC na sallamar ma’aikata 800

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Kungiyar Ma’aikatan Wutar Lantarki ta ƙasa, wato National Union of Electricity Employees (NUEE), ta yi ƙarin bayani tare da nuna rashin amincewa da matakin Kamfanin Rarraba wutar Lantarki na Abuja (AEDC) na sallamar ma’aikata 800, a ƙarƙashin tsarin sake fasalin kamfaninsu. A wata sanarwa da muƙaddashin babban sakataren ƙungiyar, Dominic Igwebike, ya fitar a Abuja, ƙungiyar ta bayyana cewa matakin na AEDC ya saba da yarjejeniyar da aka cimma tsakaninsu da mahukuntan kamfanin, wadda ta ta’allaƙa ne kan amincewa da juna da adalci a tsarin aiki. Kamfanin AEDC dai ya bayyana a shafinsa na yanar gizo…
Read More
Zuwan soshiyal midiya ne ya ƙara ruguza kasuwar littafi – Shamsiya Kaduna

Zuwan soshiyal midiya ne ya ƙara ruguza kasuwar littafi – Shamsiya Kaduna

"Babu bangon da muryar rubutu ba ta iya fasawa ba" Daga AISHA ASAS  Manazarta da dama na ra’ayin cewa, marubuta mata ne ƙashin bayan duk wani cigaba da aka samu a duniyar rubutun litattafan adabin kasuwar Kano. Jajircewa da sanin abin da makaranta ke buƙata ne ya sa suka yi wa maza marubuta zarra, har ta kai ko maza 'yan uwansu sun fi karɓar rubutun na mata fiye da nasu. Duk da an tabbatar da cewa, mazan ma ba wai an bar su a baya ba ne, kusan za mu iya cewa, marubuta mata tsintar dami suka yi a kale,…
Read More
Ka ji tsoron Allah, ba Trump ba – Shawarar Sarkin Iwo ga Tinubu

Ka ji tsoron Allah, ba Trump ba – Shawarar Sarkin Iwo ga Tinubu

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Sarkin Masarautar Iwo, wato Oluwo na ƙasar Iwo da ke Jihar Osun, Oba Abdurosheed Akanbi, ya shawarci Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu da ya mayar da hankalinsa wajen tsoron Allah fiye da tsoron kowanne mutum, ciki har da Shugaban Amurka, Donald Trump. Ya ce, idan shugaba Tinubu zai miƙa wuya ga Allah da gaske — wanda shi ne ya halicci Trump — to babu abin da zai tsoratar da shi. Da yake jawabi a bikin shekara-shekara na Olodumare da aka gudanar a garin Iwo a ranar Lahadi, Oluwo ya bayyana cewa garinsu bai taɓa fuskantar yaƙi…
Read More
Ba zan lamunci haka ba, inji Wike bayan taƙaddama da soja

Ba zan lamunci haka ba, inji Wike bayan taƙaddama da soja

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya bayyana rashin jin daɗunsa kan abin da ya kira da “mamayar sojoji” kan wani fili da ake rikici a kansa a Abuja. Wike ya kai ziyara kai tsaye zuwa wurin a ranar Talata bayan samun rahoto cewa wasu sojoji sun kori jami’an hukumar raya birane ta FCTA da ke aikin hana gini ba bisa ka’ida ba. Yayin da yake magana da manema laɓaria bayan faruwar lamarin, Wike ya gargaɗi masu amfani da ƙarfin soja don hana gwamnati aiwatar da doka, yana mai cewa ba zai lamunci irin wannan…
Read More