ukarofi

12715 Posts
Ƙungiyar Izala a Katsina ta horar da marayu 300 kan sana’ar hannu

Ƙungiyar Izala a Katsina ta horar da marayu 300 kan sana’ar hannu

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina An gabatar da wannan horarwa na koyar da sana'o'i ga marayun ƙarƙashin ƙungiyar Jama'atu Izalatil Bidi'a Wa Ikamatis Sunnah ta Jihar Katsina haɗin gwuiwa da Gidauniyar Sautus Sunnah Charity Foundation. A jawabin sa wajen bikin shugaban ƙungiyar Izalatul bidi'a wa Ikamatul sunnah reshen jihar Katsina Sheikh Yakubu Musa Hassan Sauttus sunnah ya bayyana cewa Sanata Sadiq Yar'adua ya miƙa wannan cibiya ga kungiyar Izala ta jihar wanda ita kuma bisa wannan ne ƙungiyar ta yi haɗin gwiwa da Sautus-Sunnah Charity Foundation domin koyar da marayu matasa maza da mata sana'o'in hannu "domin a taimaki marayun…
Read More
Ƙungiyar Malaman jami’ar UMYU a Katsina ta tsunduma yajin aiki

Ƙungiyar Malaman jami’ar UMYU a Katsina ta tsunduma yajin aiki

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Ƙungiyoyin malamai da ma’aikatan Jami’ar Ummaru Musa Yar’adua (UMYU) a Katsina sun tsunduma yajin aiki “sai badba ta gani” daga yau Litinin, 3 ga watan Nuwamba. Yajin aikin ya shafi dukkan malamai da ma’aikatan jami’ar, sakamakon wasu matsalolin da suke zargin gwamnati ta yi biris da su. Daga cikin ƙorafe-ƙorafen da suka gabatar sun haɗa da; Rashin ingantaccen jin daɗin ma’aikatan jami’ar, Matsalar ƙwace ikon gudanar da shafin (portal) na makaranta. Sauran sun haɗa da ƙarancin kuɗaɗen gudanarwa, da kuma batun walwalar ɗalibai. Sai dai a nata ɓangaren, Gwamnatin Jihar Katsina ta yi watsi da…
Read More
Yadda haƙowa da cinikin zinare ke ƙarfafa ta’addanci a Arewa maso Yamma

Yadda haƙowa da cinikin zinare ke ƙarfafa ta’addanci a Arewa maso Yamma

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD An ƙiyasta cewa, Nijeriya tana yin asarar sama da Dala biliyan tara duk shekara saboda haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba — inda kaso mafi yawa ya ta’allaƙa ne da haƙar zinariya. Wani bincike da jaridar Daily Trust ta gudanar ya gano cewa babbar kashi daga cikin zinariyar da ake haƙowa a Arewa maso Yamma tana komawa hannun masu ta’addanci don su riƙa samun kuɗaɗen sayen makamai ne. A ƙarƙashin ƙasar Zamfara mai arzikin zinariya, wani ɗan bindiga mai suna Kachalla Mati, wanda ya gaji gawurtaccen shugaban ’yan ta’adda Halilu Sububu, ana zargin yana tara fiye…
Read More
Dangote ya zama ɗan Afrika na farko da ya mallaki Dala biliyan 30

Dangote ya zama ɗan Afrika na farko da ya mallaki Dala biliyan 30

Daga MAHDI MUSA MUHAMAMD Attajirin Afirka, Alhaji Aliko Dangote, ya kafa sabon tarihi bayan ƙididdigar Bloomberg Billionaires Indeɗ ta nuna cewa dukiyarsa ta kai Dala Biliyan 30.2, wanda ya fi kowanne mutum a nahiyar Afirka. Rahoton ya nuna cewa, Dangote ya ƙara dala biliyan 2.25 cikin shekara guda — ƙaruwa da kashi 8% – sakamakon ribar da ya samu daga harkokin siminti, man fetur, da takin zamani. Bloomberg ta bayyana cewa dukiyarsa ta ƙaru da dala miliyan 89.2 cikin sa’o’i 24 kacal, lamarin da ya tabbatar da matsayin sa a matsayin mutum na 75 mafi arziki a duniya. A matakin…
Read More
An cire Nijeriya daga jerin ƙasashe masu aikata almundahanar kuɗaɗe

An cire Nijeriya daga jerin ƙasashe masu aikata almundahanar kuɗaɗe

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Shugaban Nijeriya, Bola Tinubu ya bayyana cewa, an Nijeriya daga jerin ƙasashen da aka fi saka wa ido saboda yawan aikata zamba da kuma halasta kuɗaɗen haram a duniya. ƙungiyar kula da irin waɗannan laifuka ta 'Financial Action Task Force' (FATF) mai hedikwata a Faransa ta bayar da sanarwar cire ƙasashen biyu mafiya girman tattalin arziki a Afirka yau Juma'a bayan taronta. Ta kuma cire ƙasashen Burkina Faso da Mozambiƙue daga jerin nata na ƙasashen da take bayar da shawarar tsaurara saka ido a kan su saboda ayyukan masu damfara da halasta kuɗin haram. A shekarar…
Read More
Kotu ta ci tarar DSTV kan katse wa kwastoma sabis

Kotu ta ci tarar DSTV kan katse wa kwastoma sabis

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Hukumar Kare Haƙƙin Masu Saye da Masu Amfani da Kayayyaki ta ƙasa (FCCPC) ta bayyana gamsuwa da wasu sabbin hukuncin kotu da suka ƙarfafa kare haƙƙin kwastamomi a faɗin Nijeriya, tana mai cewa, wannan cigaba ne mai ƙarfi wajen tabbatar da gaskiya da ladabi a kasuwar Nijeriya. A wata sanarwa da darektan hulɗa da jama’a na hukumar, Ondaje Ijagwu, shugaban hukumar Tunji Bello ya yaba wa kotuna bisa yanke hukunci da suka tabbatar da aiwatar da dokar Federal Competition and Consumer Protection Act (FCCPA) ta 2018, tare da ƙarfafa ’yan ƙasa su nemi adalci idan an…
Read More
ADC ta zargi gwamnatin Tinubu da yin amfani da siyasantar da yunwa

ADC ta zargi gwamnatin Tinubu da yin amfani da siyasantar da yunwa

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Jam’iyyar ADC ta zargi gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da rashin gaskiya kan iƙirarin da take yi na cewa ana samun ƙaruwar samar da abinci a cikin gida, tana mai cewa rashin tsaro da gudun hijirar manoma musamman a Arewacin Nijeriya sun tabbatar da cewa wannan magana ba gaskiya ba ce. A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar na ƙasa, Bolaji Abdullahi, ya fitar, ADC ta bayyana damuwa cewa gwamnati na “yaɗa labaran ƙarya kan saukar farashin abinci”, tana mai cewa wannan “manufar siyasa ce da ake amfani da ita wajen cutar…
Read More
Wata mata ta kai zafin rana ƙara ofishin ’yan sanda a Legas

Wata mata ta kai zafin rana ƙara ofishin ’yan sanda a Legas

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Wata mata da ba a bayyana sunanta ba ta haifar da abin mamaki a jihar Legas, bayan ta shiga ofishin ‘yan sanda na Panti domin kai ƙara kan zafin rana da ta ce ya yi tsanani sosai. Rahotanni daga wani mai amfani da shafin ɗ (tsohon Twitter) mai suna Olamide (@Olamide0fficial) sun bayyana cewa matar ta ɗauki motar haya ta Uber daga Lekki zuwa Panti, inda ta ce za ta kai ƙara saboda yanayin zafi ya yi “tsauri fiye da kima.” Sai dai bayan isarta ofishin ‘yan sandan, matar ta ƙi biyan kuɗin shatar motar na…
Read More
Abin kunya ne babu ƙasar Afirka mai kujerar dindindin a Majalisar ɗinkin. Duniya – Guterres

Abin kunya ne babu ƙasar Afirka mai kujerar dindindin a Majalisar ɗinkin. Duniya – Guterres

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Sakataren Majalisar ɗinkin Duniya (MDD), Antonio Guterres, ya bayyana cewa lokaci ya yi da za a yi gyaran fuska a manyan majalisun duniya, musamman Majalisar Tsaro ta Majalisar ɗinkin Duniya, domin su dace da yanayin siyasa da tattalin arzikin duniya na yanzu. Yayin wata tattaunawa ta musamman da aka shirya a ranar Litinin don tunawa da cika shekaru 80 da kafa Majalisar ɗinkin Duniya, Guterres ya bayyana rashin samun kowace ƙasa ta Afirka a matsayin memba mai kujerar dindindin a Majalisar Tsaro a matsayin abin kunya da ke buƙatar gaggawar gyara. Ya ce, tun bayan kafuwar…
Read More
Kwankwaso ya soki matakin Donald Trump na Kiran Najeriya matsayin ƙasa mai matsala ta musamman

Kwankwaso ya soki matakin Donald Trump na Kiran Najeriya matsayin ƙasa mai matsala ta musamman

Daga RABIU SANUSI a Kano Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma jagoran jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP), Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana damuwa kan matakin Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, bayan da ya ayyana Najeriya a matsayin “ƙasa mai matsala ta musamman” (country of particular concern). Kwankwaso ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Lahadi, inda ya ce kalaman Trump abin damuwa ne, tare da kira ga gwamnatin Amurka da ta rungumi hanyar haɗin kai da taimako maimakon fitar da kalamai da za su raba kawunan ‘yan Najeriya. “Abin da…
Read More