Buhari zai kai ziyarar aiki ta ƙarshe a Saudiyya

Ranar Talata idan Allah Ya kai mu ake sa ran Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari zai kai ziyara ƙsarar Saudiyya.

Ziyarar aikin wadda za ta kasance ta ƙarshe da Buhari zai yi a ƙasar a gwamnatinsa, za ta tabbata ne daga Talata, 11 zuwa 19 ga Afrilu, 2023.

Mai magana da yawun Shugaban Ƙasa, Garba Shehu, shi ne ya bayyana hakan cikin sanarwar da ya fitar ranar Litinin.

Shehu ya ce yayin ziyarar tasa a Saudiyya, Buhari zai gabatar da Hajjin Umara.

Kuma hadimansa ne za su yi masa rakiya yayin ziyarar, in ji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *