14
Oct
Daga BELLO A. BABAJI Wata babbar mota ta take wasu ma'aurata da wani mutum ɗaya a hanyar Sagamu-Ogijo da ke Jihar Ogun wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwar su . Lamarin ya auku ne a lokacin da mamatan ke cikin wata mota ƙirar Wagon da wani babur na Bajaj. Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, Omolola Odutola ta tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Lahadi cikin wata sanarwa da ta fitar, inda ta bayyana mijin mai suna Moses Ekpolo ɗan shekara 25 da matarsa, Josephine Ekpolo mai shekaru 19 da kuma wani Kolawole Moshood waɗanda likitoci suka tabbatar da mutuwar su…
