Labarai

An karrama Janar Gusau da lambar NIPR

An karrama Janar Gusau da lambar NIPR

Daga BASHIR ISAH A ranar Larabar da ta gabata aka karrama Muƙaddashin Darakta na Sashen Labarai na Tsaro, Brigadier General Ismaila Gusau, Ph.D. mni, da lambar yabo ta NIPR. Cibiyar Hulɗa da Jama'a ta Ƙasa ita ce ta karrama jami'in da wannan lamba ta yabo. An karrama Gusau ne saboda hazaƙarsa wajen ƙoƙarin sauke nauyin aiki da ya rataya a wuyansa. Kuma an karrama shi ne tare da wasu a wajen taron wanda cibiyar da ta ɗauki nauyin shiryawa ta saba shiryawa duk shekara. 'Yan jaridu da jami'an hulɗa da jama'a daga sassa daban-daban na daga cikin waɗanda cibiyar ta…
Read More
Za a ɗage dakatarwar da aka yi wa Ningi ba da daɗewa ba – Akpabio

Za a ɗage dakatarwar da aka yi wa Ningi ba da daɗewa ba – Akpabio

Daga BASHIR ISAH Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya bayyana cewa, nan ba da daɗewa ba za a ɗage dakatarwar da aka yi wa Sanata Abdul Ningi (PDP, Bauchi ta Tsakiya) a Majalisar Dattawa. Ya bayyana hakan sa'ilin da yake amsa wa manema labarai tambayoyi a wajen wani taro da aka shirya ranar Juma'a a Geneva, Switzerland. Wannan na zuwa ne sa'o'i 24 bayan da Ningi ya yi wa Akpabio kan cewa zai ƙalubalanci dakatar da shi da aka yi a kotu muddin ba a janye dakatarwar ba a cikin kwana 7. An dakatar da Ningi daga majalisar ne biyo…
Read More
Tsohon Mataimakin Gwamnan Kwara, Peter Kisira ya rasu yana da shekara 74

Tsohon Mataimakin Gwamnan Kwara, Peter Kisira ya rasu yana da shekara 74

Daga BASHIR ISAH An bayyana rasuwar tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Kwara Peter Kisira. Gwamnatin jihar ce ta tabbatar da rasuwar marigayin cikin rasanarwar da ta fitar da safiyar Asabar ta bakin Babban Sakataren Yaɗa Labarai, Rafiu Ajakaye. Marigayin ya bar duniya yana da shekara 74. Kisira ya yi mataimakin Gwamnan Jihar ne a zamanin Gwamna Alhaji Abdulfattah Ahmed, daga watan Mayun 2011 zuwa Mayun 2019. Tuni dai Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya bayyana alhininsa kan rasuwar tare da miƙa ta'aziyya ga 'yan uwan mamacin.
Read More
Yadda aka sace wani limami a Jihar Kogi

Yadda aka sace wani limami a Jihar Kogi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace babban limamin yankin Iyara da ke Ƙaramar Hukumar Jimu a Jihar Kogi, Sheikh Quasim Musa. ’Yan bindigar sun kai farmaki gidan malamin ne a ranar Litinin 25 ga Maris, 2024, inda suka yi awon gaban da shi kuma har yanzu babu amo ballantana labarinsa. Bayanai sun ce ‘yan bindigar sun fara harbe-harbe, jim kaɗan da isa gidansa da ƙarfe 10 na daren ranar Litinin. Jami’in hulɗa da jama’a a ƙungiyar ci gaban Iyara, Mista E.K. Adebayo ya ce ’yan bindigar sun…
Read More
Hukumar Kare Haƙƙin Mallaka ta maka shugaban MTN a kotu

Hukumar Kare Haƙƙin Mallaka ta maka shugaban MTN a kotu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Hukumar Kare Haƙƙin Mallaka ta Nijeriya, NCC, ta gurfanar da Kamfanin Sadarwar MTN da wasu mutane huɗu a gaban kotu bisa zarginsu da keta haƙƙin mallaka. An shigar da aarar mai lamba FHC/ABJ/CR/111/2024 a babbar kotun tarayya da ke Abuja ranar Litinin. Sauran mutane huɗu da ake tuhuma a shari’ar su ne; Karl Toriola, shugaban MTN na Nijeriya, Nkeakam Abhulimen da Yahaya Maibe. A cikin tuhume-tuhume uku, NCC ta yi zargin cewa waɗanda ake tuhumar, a tsakanin shekarar 2010 zuwa 2017, “sun amfani da fasahar da ba tasu ba”, sun keta ayyukan waƙa na wani mawaƙi,…
Read More
Harin Mairuwa: Gwamnan Raɗɗa zai tallafa wa iyalan waɗanda abin ya shafa

Harin Mairuwa: Gwamnan Raɗɗa zai tallafa wa iyalan waɗanda abin ya shafa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamna Dikko Umaru Raɗɗa na jihar Katsina ya yi Allah wadai da harin da ‘yan bindiga suka kai a garin Mairuwa da ke Ƙaramar Hukumar Faskari a jihar, inda ya bayyana hakan a matsayin rashin tausayi. Harin wanda ya afku a yammacin ranar Asabar ɗin da ta gabata a lokacin sallar magariba a watan Ramadan da muke ciki, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane biyu tare da yin garkuwa da wasu biyu. Gwamna Raɗɗa, ta bakin sakataren gwamnatin jihar Barista Abdullahi Garba Faskari ya yi Allah wadai da harin tare da jajantawa. Ya kuma yi…
Read More
Gwamna Inuwa ya ƙaddamar da rabon abinci karo na 17 a Gombe

Gwamna Inuwa ya ƙaddamar da rabon abinci karo na 17 a Gombe

Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya na Jihar Gombe ya kaddamar da rabon kayan abinci a karo na 17 ga marasa galihu da nakasassu kimani dubu ɗari biyu da sha huɗu da ɗari biyar. Za a yi rabon kayan abincin ne a rumfunar zaɓe guda dubu 2,218 da ke mazaɓu 114 a faɗin jihar. Gwamnan ya ce, ya fara ba da irin wannan tallafin ne tun a zangonsa na farko, inda ya raba sau 15. Ya ce a yanzu bayan dawowarsa wannan shi ne karo na biyu kuma jimilla na 17 idan an haɗa da wanda…
Read More
Abinda ya sa ba a cika satar ɗalibai ba a Borno — Zulum

Abinda ya sa ba a cika satar ɗalibai ba a Borno — Zulum

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya bayyana riko da tsarin nan na “safe school initiative” a matsayin sirrin da ya sa ba cika samun labarin satar ‘yan makaranta ba a jihar. Tsarin na “safe school initiative” dai wani shiri ne da ya wajabta gina katanga da ɗaukar ma’aikata masu ɗauke da makamai domin kare lafiya da dukiya a makarantu. Zulum ya bayyana ne Fadar Gwamnatin Nijeriya jim kaɗan bayan fitowarsa daga wani taro na shuwagabanni a ƙasar nan. Zulum ya ce “Mun kai akƙalla shekara bakwai zuwa takwas da ƙaddamar da tsarin…
Read More
Yadda gayyatar da jami’an tsaro suka yi min ta gudana — Sheikh Gumi

Yadda gayyatar da jami’an tsaro suka yi min ta gudana — Sheikh Gumi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shahararren malamin addinin Musluncin nan da ke Kaduna, Sheikh Ahmad Mahmud Gumi ya bayyana cewa jami’an tsaron Nijeriya sun gayyace shi ya amsa wasu tambayoyi cikin girmamawa. Duk da cewa, Sheikh bai bayyana waɗanne ɓangare na jami’an tsaron ba ne suka gayyace shi, ya tabbatar da cewa an gayyace shi sun tattauna cikin mutunci da sanin ya kamata. A ranar Litinin ɗin da ta gabata ne dai Ministan Labarai na Nijeriya Mohammed Idris ya bayyana cewa babu wanda ke gaba da doka sai dai wanda bai yi laifi ba. “Gwamnati ba za ta yi…
Read More
Babu batun rage farashin fetur da gas, inji NNPC

Babu batun rage farashin fetur da gas, inji NNPC

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Kamfanin Man Fetur na Nijeriya, NNPCL, ya musanta rahotannin da ake yaɗawa ya cewa ya rage farashin man fetur da iskar gas. NNPCL ya mayar da martanin ne kan wasu rahotanni da wasu kafafen watsa labaran Nijeriya ke yaɗawa cewar ya rage farashin man fetur da gas. Babban jami'in sadarwa na kamfanin Olufemi Soneye ne ya yi watsi da jita-jitar a wata sanarwar da ya rabawa manema labarai. Ya kuma buƙaci jama'a da su yi watsi da rahotannin. Sanarwar ta ce, "Kamfanin NNPCL na so ya yi wa al'umma ƙarin haske kan wasu rahotannin da ke…
Read More