30
Mar
Daga MAHDI M. MUHAMMAD Babban Bankin Nijeriya ya ɗaga darajar manufofin hada-hadar kuɗi da aka fi sani da 'kuɗin ruwa' da kashi 200 cikin 100 zuwa kashi 24.75 daga kashi 22.75 cikin 100 a ƙoƙarin da ake na magance hauhawar farashin kayayyaki. Gwamnan babban bankin ƙasar CBN, Olayemi Cardoso, ne ya bayyana hakan a ranar Talata a wajen taron manema labarai na kwamitin kula da harkokin kuɗi karo na 294 a Abuja. Sabon kuɗin ruwa shi ne kashi 2% daga kashi 22.75 cikin dari da MPC ta sanar kusan wata daya da ya gabata da kuma hauhawar farashi na biyu…
