Labarai

Shugaba Buhari ya yi alƙawarin mutunta umarnin kotu don cigaba da amfani da tsofaffin takardun kuɗi

Shugaba Buhari ya yi alƙawarin mutunta umarnin kotu don cigaba da amfani da tsofaffin takardun kuɗi

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya (AGF) kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, ya ce shugaban ƙasa Muhammadu Buhari zai mutunta umarnin da Kotun Ƙolin ƙasar ta bayar a kan ƙarar da wasu gwamnonin jihohi uku suka shigar inda kotun ta dakatar da aiwatar da wa'adin daina amfani da tsofaffin takardun kuɗi na naira 200 da 500 da kuma 1,000. Gwamnonin jihohin Kaduna da Kogi da kuma Zamfara ne suka shigar ƙarar inda suke ƙalubalantar wa'adin. Da sabon ci gaban da aka samu, ’gan Nijeriya na da damar zuwa ranar 15 ga watan Fabrairu su yi amfani da tsoffin…
Read More
Majalisar Ƙasa ta amince da sake fasalin Naira

Majalisar Ƙasa ta amince da sake fasalin Naira

*Ta buƙaci CBN ya ba da himma wajen samar da wadatattun sabbin takardun Naira Daga BASHIR ISAH Majalisar Ƙasa ta amince da sake fasalin takardun Naira na 200, 500 da kuma 1000 da Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya yi. Majalisar ta nuna amincewarta ne yayin zaman da ta yi ranar Juma'a a Fadar Shugaban Ƙasa ƙarƙashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari. Ta kuma shawarci CBN da ya ba da himma wajen aiwatar da sabbin tsare-rsarensa domin rage wa 'yan ƙasa wahalar ƙarancin kuɗi da suke fuskanta. Da yake zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan taron, Babban Lauyan Ƙasa kuma Ministan…
Read More
Ambaliya ta jawo asarar biliyan 700 a harkar noma – Rahoto

Ambaliya ta jawo asarar biliyan 700 a harkar noma – Rahoto

Daga AMINA YUSUF ALI Wani rahoto da hukumar faɗaɗa harkar noma da bincike (NAERLS) ta bayyana cewa, ambaliyar ruwa a Nijeriya ta lamushe Naira biliyan 700 na kuɗin da aka zuba a harkar noma a ƙasar. A yayin da yake miƙa wannan sakamakon rahoton ga Ministan Noma da raya karkara, Daraktan zartaswa na NAERLS, Farfesa Emmanuel Ikani ya bayyana cewa, ambaliyar ruwan ta lalata filayen noma, ta lalata amfanin gona abinda ya jawo ƙarancin amfanin gonar da kuma asara ga manoma. Ya ƙara da cewa, bincike ya nuna cewa, an samu zaizayar ƙasa a wurare fiye da 300 a jihohi…
Read More
Hukumar Alhazan Jihar Kano ta soma bitar mako-mako ga maniyyata

Hukumar Alhazan Jihar Kano ta soma bitar mako-mako ga maniyyata

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Hukumar jin daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta ƙaddamar da fara gudanar da bitar mako-mako ga maniyyatan aikin Hajjin bana. Da yake jawabi a yayin taron, Kwamishinan ayyuka na musamman, Hon. Kabir Muhammad Tarauni da ya wakilci Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Ganduje, ya ce irin kulawa da Gwamnan Kano ke bai wa cigaban addini ya sa ake tsara bitar da wuri. Ya ce bitar ta ilmantar da da maniyyata ne dukkan nauyi da ya ɗoru a kan su na ibada da za su aiwatar don kyautata aikin Hajji da za su je. Kabiru Muhammad Tarauni…
Read More
Gobe Kwalejin Kimiyyar Lafiya ta FAMSAS za ta yi bikin rantsar da sabbin ɗalibanta

Gobe Kwalejin Kimiyyar Lafiya ta FAMSAS za ta yi bikin rantsar da sabbin ɗalibanta

Daga JOHN D. WADA a Lafiya Shugaban Kwalejin Kimiyyar Lafiya ta FAMSAS mai zaman kanta dake garin Keffi, hedikwatar Ƙaramar Hukumar Keffi a jihar Nasarawa, Alhaji Mohammad Idris Lukumbogo ya ce a ƙoƙarinta na cigaba da samar wa al’ummar jihar da qasa baki ɗaya ingantataccen ilimin kiwon lafiya na zamani, Kwalejin ta FAMSAS ta kimtsa caf don gudanar da wani gagarumin taron ta mai muhimmanci mai kuma ɗimbin tarihi wato na rantsar da sabbin ɗalibanta da suka samu damar fara karatu a kwalejin na zangon karatun shekarar 2023 da ake ciki a gobe Asabar 11 ga watan Fabrairun shekarar 2023…
Read More
Girmama matasa da ba su dama zai kawo ci gaban Nijeriya – Farfesa Adamu Tanko

Girmama matasa da ba su dama zai kawo ci gaban Nijeriya – Farfesa Adamu Tanko

Daga MUHAMMADU MUJJITABA a Kano Mataimakin Shugaban Jami'ar BUK, Farfesa Adamu Idris Tanko, ya ce akwai buƙatar dattawan Nijeriya, da shugabanin Nijeriya, kowa ya yi karatun tanutsu ta hanyar cewa wannan ba zamaninka ba ne ka bar wa yara matasa ka zama uba malami mai karantarwa da shawarwari ga matasa kamar yadda shugabar ƙasar Naizland, ta sauka da kanta, ya ce wani ya riƙe qasar ta yi iya nata ƙoƙarin, saboda kishin al'umma da ƙasar ta a lokacin da yake ganawa da manema labarai a harabar jami'ar dake birnin Kano a wannan lokaci. Haka kuma ya ce, "baiwar matasan Nijeriya,…
Read More
Lafiya lau za a yi zaɓukan 2023 ba tare da rikici ba – Monguno

Lafiya lau za a yi zaɓukan 2023 ba tare da rikici ba – Monguno

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Mai Bai wa Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin tsaro, NSA, Manjo-Janar Babagana Monguno (mai ritaya) ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa za a gudanar da zaɓen 2023 ba tare da rikici ba. Monguno ya bada wannan tabbacin ne yayin ganawarsa da Hukumar Zave Mai Zaman Kanta ta Ƙasa INEC da kuma shugabannin hukumomin tsaro a ƙasar. Ya shawarci 'yan Nijeriya da su yi watsi da duk wani nau’i na ɓata-gari, labaran ƙarya da fargaba kan yadda za a gudanar da babban zaɓen 2023, yana mai cewa za a gudanar da zaɓen cikin kwanciyar hankali.…
Read More
Zaɓe: Gwamnatin Tarayya ta rufe jami’o’i na makonni 3

Zaɓe: Gwamnatin Tarayya ta rufe jami’o’i na makonni 3

Daga WAKILINMU Gwamnatin Tarayya ta bai jami’o’in Nijeriya umarni kan su rufe daga ranar 22 ga Fabrairu zuwa 14 ga Maris saboda zaɓuɓɓukan da za a gudanar ran 25 ga Fabrairu da 11 ga Maris, 2023. Gwamnati ta ba da umarnin ne domin bai wa ɗalibai, malamai da saunran ma'aikata a jami'o'i damar kaɗa ƙuri’a a lokacin zaɓukan. Umarnin na ƙunshe ne cikin sanarwa mai ɗauke da kwanan wata 3 ga Fabrairu wadda Hukumar Kula da Jami’o’i ta Ƙasa (NUC) ta aike wa jami’o’i a faɗin ƙasa. Cikin sanarwar mai ɗauke da sa hannun Mataimakin Sakataren NUC, Dakta Chris Maiyaki,…
Read More
Dubun masu tiransifa ta ƙarya ta cika a Kano

Dubun masu tiransifa ta ƙarya ta cika a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU, a KANO Rundunar ‘yan sandan jiyhar Kano ta kama wasu mutum biyu da ake zargi da damfarar wani mai shago a Sharaɗa da ke Ƙaramar Hukumar Binni ta jihar. Rahotanni sun nuna an kama waɗanda ake zargin, Mujihid Kabir da Abdu Imam da laifin damfara, sata da kuma kutse. Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya tabbatar da kama su a ranar Talatar da ta gabata, Ya ce, “Mun samu kiran gaggawa a ranar 2 ga watan Fabrairu daga Sharaɗa cewa wasu mutum biyu sun sayi shinkafa a wani shago inda suka…
Read More
Kotun Ƙoli ta dakatar da hana amfani da tsohuwar Naira na wucin-gadi

Kotun Ƙoli ta dakatar da hana amfani da tsohuwar Naira na wucin-gadi

Daga BASHIR ISAH A ranar Laraba Kotun Ƙoli ta dakatar da yunƙurin Gwamnatin Tarayya na daina amfani da tsohuwar Naira daga ranar 10 ga Fabrairu, 2023. Tawagar alƙalai bakwai ƙarƙasbin jagorancin Mai Shari'a John Okoro ne suka yanke wannan hukuncin biyo bayan ƙarar da gwamnonin Kaduna da Kogi da Zamfara suka shigar. Kowacce daga jihohin da lamarin ya shafa ta shigar da ƙara inda ta nemi kotu ta dakatar da Gwamnatin Tarayya ta hannun Babban Bankin Ƙasa (CBN) ko kuma sauran bankuna daga matakin da aka ɗauka na daina karɓar tsohuwar Naira (200, 500 da 1000) daga ran 10 ga…
Read More