Labarai

Shugaban INEC ya buƙaci Majalisar Tarayya ta dage kan kwaskwarimar dokar zaɓe

Shugaban INEC ya buƙaci Majalisar Tarayya ta dage kan kwaskwarimar dokar zaɓe

Daga WAKILIN MU Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya yi kira ga 'yan Majalisar Tarayya da su yi aiki ba tare da la'akari da jam'iyyar da kowanne ke wakilta ba wajen yi wa Dokar Zaɓe garambawul wanda zai taimaka wajen inganta yadda ake gudanar da zaɓe a ƙasar nan. Yakubu ya yi wannan kiran ne a wajen bikin ƙaddamar da kwamitin haɗin gwiwar ƙwararru na yi wa Dokar Zaɓe kwaskwarima wanda aka yi a Abuja a ranar Juma'a. Kwamitin Haɗin Gwiwar Majalisar Tarayya kan Hukumar Zaɓe da Al'amuran Zaɓe ne ya shirya taron tare da tallafin…
Read More
Kotu ta garqame asusun bankunan dan majalisa a Kaduna

Kotu ta garqame asusun bankunan dan majalisa a Kaduna

Daga ABBA MUHAMMAD, a KadunaBabar Kotun Jihar Kaduna ta ba da umurnin a garqame asusun ajiyar bankuna har guda 14 na dan majalisar jiha mai wakiltar Doka da Gabasawa a Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, wanda shi ne shugaban masu rinjaye na majalisar, Honarabul Haruna Inuwa Dogo Mabo. Kotun ta bayyana cewa ta dauki wannan mataki ne a bisa samun sa da laifin cin amana da zamba cikin aminci da kuma sama da fadi da kunnen qashi da ya nuna wajen qin biyan dimbin basussuka na kudaden da ya amsa a hannun jama’a da sunan bashi.Wannan bayanin ya fito ne daga bakin…
Read More
Ba Allah ne ya jefa Nijeriya halin da ta shiga ba – Obasanjo

Ba Allah ne ya jefa Nijeriya halin da ta shiga ba – Obasanjo

Daga UMAR M. GOMBE, a Abuja A cin wani saqon da ya aike na shiga sabuwar shekara, Tsohon Shugaban Qasa, Olusegun Obasanjo, ya qalubalanci Shugaban Qasa, Muhammadu Buhari da sauran shugabanni da su daina dora alhakin halin da Nijeriya ke ciki kan Ubangiji, su zargi kansu kurum. Obasanjo ya bayyana haka ne a dakin karatun sa mai suna Olusegun Obasanjo Presidential Library dake Abeoluta a Jihar Ogun a wani saqonsa barka da sabuwar shekara da ya saba aikewa a duk qarshen shekara. Tsohon shugaban qasan ya nuna qin amincewar sa cewa, Allah ne Ya qaddara halin talauci da Nijeriya ke…
Read More
Shugaban Majalisar Dattawa ya taya ‘yan Nijeriya murnar sabuwar shekara

Shugaban Majalisar Dattawa ya taya ‘yan Nijeriya murnar sabuwar shekara

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmed Lawan ya taya dukkan ’yan Nijeriya murnan shiga sabuwar shekarar 2021. Yana mai cewa Shekarar 2020 ta zo ma daukacin kasashen duniya cike da kalubale na tattalin arziki, tsaro, lafiya da sauran fannunuka. “Amma Alhamdulillah duk da haka, wadannan kalubalen ba su karya mana gwiwa na ganin samun kyakykyawar makoma a matsayin mu na mutane da kuma kasa ba. A matsayin mu na majalisar dokoki, mun dade da tsara yadda zamu tunkari abubuwan da shekarar 2020 ta zo da su ta hanyar yin dokokin da za su tabbatar da gudanar da kyakykyawan mulki da cigaban…
Read More
El-Rufa’i ya sake killace kan sa bayan bullar cutar korona a gidan sa

El-Rufa’i ya sake killace kan sa bayan bullar cutar korona a gidan sa

Daga ABBA MUHAMMAD a Kaduna Sakamakon samun wasu daga cikin manyan ma'aikatan gwamnatin Jihar Kaduna da kuma mutum biyar daga cikin iyalin sa da kamuwa da cutar korona, Gwamna Nasiru Ahmad El-Rufa'i ya sake killace kan sa har sa har sai an yi masa gwaji. Gwamnan ya bayyana haka ne a daren Juma'a a cikin wani bidiyo mai tsawon minti 1:15. Wannan shi ne karo na biyu da ya killace kan sa bayan tabbatar da ci-gaba da hauhawar kamuwa da cutar a Jihar Kaduna da sauran jihohin Nijeriya. A bidiyon, gwamnan ya ce, "Ana ta ci gaba da kamuwa da…
Read More
Darajar naira ta daga, ta koma N470 a kan dala 1 a kasuwar ‘yan canji

Darajar naira ta daga, ta koma N470 a kan dala 1 a kasuwar ‘yan canji

DAGA IRO MAMMAN Darajar naira ta karu a cikin wannan makon bayan ta samu mako biyu cikin karaya idan an canza ta da dala a kasuwar 'yan canji. A ranar Laraba ta samu karin N20, ta koma N470 a kan dala 1. Kafin wannan lokaci, naira ta karye da N30 a kan dala, domin canjin ta a kasuwa ya tashi sosai zuwa N500 a kan dala 1 daga ranar Litinin, 30 ga Nuwamba zuwa N470 a dala 1 a ranar Juma'a, 20 ga Nuwamba, 2020. To amma sababbin ka'idojin da Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya fito da su a ranar Litinin,…
Read More
Sojojin Ruwan Najeriya 203 sun samu Karin girma

Sojojin Ruwan Najeriya 203 sun samu Karin girma

A yau ne aka yi wa kimanin sojojin ruwan Najeriya 203 ƙarin matsayi a Najeriya. Sanarwar da rundunar sojin ruwa ta aike wa manema labarai ta ce an ƙara wa jami’an muƙamin ne a ranar Laraba. Masu muƙamin Laftanal kwamanda 122 aka ƙara muƙami zuwa Kwamanda, yayin da kuma masu muƙamin Kwamanda 38 aka ƙara masu matsayi zuwa Kaftin. Masu muƙamin Kaftin 25 kuma aka yi wa ƙarin matsayi zuwa Kwamado.
Read More