Labarai

Cutar korona: NOA ta bukaci ‘yan Nijeriya su ba da hadin kai game da allurar riga-kafin korona

Cutar korona: NOA ta bukaci ‘yan Nijeriya su ba da hadin kai game da allurar riga-kafin korona

Daga FATUHU MUSTAPHA Hukumar Wayar da Kan 'Yan Kasa ta yi kira ga 'yan Nijeriya da su daina yarda da ra'ayoyi mara tushe da ake yadawa dangane da allurar riga-kafin cutar korona kan cewa maganin na tattare da wasu illoli.  Babban Daraktan hukumar, Garba Abari ne ya yi wannan kira a lokacin bayanin kore zargin da wasu ke yi cewa ana so a yi amfani da allurar ne wajen takaita yawan al'umma, lamarin da Abari ya ce ba gaskiya ba ne. Yana mai cewa, "Babu wata allurar riga-kafin da za a bari a shigo da ita Nijeriya ko a yi…
Read More
Kotu ta dage shari’ar El-Zakzaky zuwa 8 ga Maris

Kotu ta dage shari’ar El-Zakzaky zuwa 8 ga Maris

Kotu ta dage shri'ar El-Zakzaky zuwa 8 ga watan Maris Daga AISHA ASAS A Talatar da ta gabata babbar Kotun Jihar Kaduna da ke shari'ar jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya Ibrahim El-Zakzaky da matarsa  Zeenat, ta dage ci gaba da shari'ar ya zuwa ranar 8 da 9 ga watan Maris mai zuwa. Kotun ta dage shari'ar ne biyo bayan hukuncin da Alkali Gideon Kurada ya yanke dangane da neman kotu ta ba shi lokaci da lauyan El-Zakzaky Mr Femi Falana ya yi a bisa wakilcin Mr Eddie Inegedu, domin ba shi damar nazarin wani bidiyo da wasu shaidu biyu suka…
Read More
Matsalar Tsaro: Makarfi ya gargadi ‘yan Nijeriya

Matsalar Tsaro: Makarfi ya gargadi ‘yan Nijeriya

Daga Aisha Asas Tsohon gwamnan Jihar Kaduna Sanata Ahmed Mohammed Makarfi, ya ja hankulan 'yan Nijeriya a kan su daina barin son zuciyarsu yana tasiri wajen daukar matakai wanda hakan ka iya haifar da rikici. Makarfi ya nuna bukatar da ke akwai 'yan Nijeriya su fahimci cewa matsalar tsaron da ke addabar kasar nan aba ce da ke bukatar a yi mata taron dangi domin dakile ta. Yana mai cewa, "Wannan matsala ce da ta shafe mu baki daya." Makarfi ya yi wadannan bayanan ne a wata sanarwa da ya fitar inda ya nuna damuwarsa kan tabarbarewar sha'anin tsaron Nijeriya.…
Read More
Rikicin FCC: Kwamishinoni sun ja shugabar hukuma zuwa ICPC

Rikicin FCC: Kwamishinoni sun ja shugabar hukuma zuwa ICPC

Daga jaridar Manhaja Kwamishinoni masu wakiltar jihohi 36 na kasar nan hada da birnin tarayya Abuja, tare da Hukumar Kyautata Da'ar Ma'aikata ta Kasa (FCC) sun rubuta takardar korafi a kan shugabar hukumar FCC Dr. Muheeba Fraida Dankaka zuwa ga Hukumar Yaki da Rashawa da Laifuka Masu Alaka da Rashawa (ICPC) bisa zarginta da yin ba daidai ba da matsayinta. Takardar korafin mai dauke da kwanan wata 18/1/2021 wadda ta sami sa hannun Sir Augustine Wokocha da Abdul Wasiu Bawa-Allah, ta nuna yadda shugabar FCC ta mamaye komai na hukumar sannan ta karbe ayyukan kwamishinonin tana mika wa daraktocinta tare…
Read More
‘Yan-bindiga sun kai hare-hare a sassan Neja

‘Yan-bindiga sun kai hare-hare a sassan Neja

Daga jaridar Manhaja 'Yan-bindiga sun kai hare-hare a wasu kauyukan karamar hukumar Paikoro da ke Jihar Neja, inda suka hallaka mutum shida tare da yin garkuwa da mutum biyar sannan suka jikkata sama da mutum 20. Bayanai daga jihar sun nuna 'yan-bindigar sun soma ta'addacinsu ne daga Asabar da ta gabata zuwa washegari Lahadi da rana. Wani mazaunin daya daga cikin kauyukan da harin ya shafa mai suna Abubakar Azaido, ya shaida wa Manhaja ta tarho cewa sama da mutum 20 da suka jikkata a harin aka kai babbar asibitin Kafin Koro. Ya ce, akalla mutum 3000 ne suka tsere…
Read More
Miyetti Allah ta koka kan halin da Fulani ke ciki a Oyo

Miyetti Allah ta koka kan halin da Fulani ke ciki a Oyo

Daga jaridar Manhaja Shugaban Kungiyar Miyetti Allah na Jihar Oyo Ibrahim Abubakar Jiji, ya yi korafin halin da ake ciki mambobinsu na zaman dar-dar ne a jihar biyo bayan harin da wasu matasa da ba a san ko su wane ne ba suka kai wa Sarkin Fulani Salihu Abdulkadir a yankin Igangan, a Juma’ar da ta gabata. Wannan na faruwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Jihar Ondo ta bai wa Fulani makiyaya a jihar wa’adin kwana 7 a kan su fice mata daga dazuzzukanta. Gwamnatin Jihar Ondo ta ci gaba da kallon matakin da ta dauka a matsayin abin…
Read More
Za a yi zaben gwamnan Anambara ran 6 ga Nuwamba – INEC

Za a yi zaben gwamnan Anambara ran 6 ga Nuwamba – INEC

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta bayyana cewa a ranar 6 ga Nuwamba, 2021 za a yi zaben gwamnan Jihar Anambara. Hukumar ta bayyana jadawalin ranar zaben da abubuwan da za a aiwatar ne a cikin wata sanarwa da ta bayar a ranar Talata a Abuja. Shugaban Kwamitin Yada Labarai da Wayar da Kan Masu Zabe na hukumar, Mista Festus Okoye, wanda ya bada sanarwar, ya ce hukumar ta yi wani zama a ranar Talata inda ta tattauna kan zaben na Anambara. A cewar sa, za a yi zabubbukan share fage tare da warware duk wani sabani da ka iya…
Read More
Zaɓe: INEC za ta shigo da sababbin hanyoyin fasaha kafin 2023

Zaɓe: INEC za ta shigo da sababbin hanyoyin fasaha kafin 2023

Daga WAKILIN MU Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta ce ta na nan ta na sake nazari kan hanyoyin fasaha da ta ke amfani da su a wajen zaɓuɓɓuka, da nufin shigo da waɗansu sababbi waɗanda za su inganta zaɓuɓɓukan da za a yi daga yanzu zuwa shekara ta 2023. Daraktan Wayar da kan Masu Zaɓe da kuma Sashen Yaɗa Labarai na INEC (VEP), Mista Nick Dazang, shi ne ya bayyana haka a wajen wani taron ƙara wa juna sani na sashen nasu mai taken “Sake Duban Kundin Wayar da kan Masu Zaɓe na Ƙasa" wanda aka yi a garin…
Read More
Sadiya Umar Farouq na so a kula da naƙasassun Nijeriya kamar yadda ake yi a wasu ƙasashen

Sadiya Umar Farouq na so a kula da naƙasassun Nijeriya kamar yadda ake yi a wasu ƙasashen

Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta samar wa da naƙasassun da ke Nijeriya hanyoyin da za su riƙa bi a dukkan gine-gine da wurare na gwamnati irin su filayen jirgin sama, tashoshin jirgin ƙasa da na mota da makarantu. Ministar ta yi kiran ne a lokacin da ta gabatar da Shugaba da membobi da Babban Sakataren Cibiyar Naƙasassu ta Ƙasa ga Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Alhamis a fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja. Hajiya Sadiya ta gode wa Shugaban Ƙasa saboda yadda ya amsa kiran naƙasassun…
Read More