30
Jan
Daga FATUHU MUSTAPHA Ma'aikatar Ilimi ta Jihar Bauchi ta bayyana cewa, dalibai daga makarantun sakandare masu zaman kansu a jihar na iya neman gurbin karatu a makarantun gwamnatin jihar don shiga aji hudu (SS1). Kwamishinan Ilimi na Jihar, Dr. Aliyu I. Tilde ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a wannan Asabar. A cewar kwamishinan, "Mun fahimci cewa iyaye kalilan ne da 'ya'yansu ke tafiya makarantun kudi ke da masaniyar cewa 'ya'yansu na da damar neman gurbin karatu a makarantun sakandaren gwamnatin jihar don shiga aji hudu ta hanyar amfani da sakamakonsu na BECE." Ya ci gaba…
