23
Dec
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Babbar tashar talabijin ta duniya, wato France 24 ta ƙulla alaƙar aiki tsakaninta da Qausain TV dake nan Nijeriya. Shugaban Qausain TV, Malam Nasir Musa Idris (Albani Agege) ne ya bayyana haka a wannan makon, jim kaɗan bayan amsa gayyatar da tashar ta France 24 ta yi masa. Nasir Albani wanda yanzu haka yana ƙasar Faransa domin kammala shirye-shiryen fara aikin, ya ce: "A halin yanzu Ina ƙasar Faransa, bayan da muka samu tagomashin gayyata zuwa birnin Faris (Paris), inda babban gidan talabijin mai ƙololuwar daraja wato France 24 ya ba ni kujerar zama…
