Labarai

Atiku ya naɗa Dino Melaye da Daniel Bwala a matsayin kakakinsa

Atiku ya naɗa Dino Melaye da Daniel Bwala a matsayin kakakinsa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP kuma tsohon mataimakin shugaban ƙasar Nijeriya, Atiku Abubakar ya naɗa Sanata Dino Melaye da Dakta Daniel Bwala a matsayin masu magana da yawun ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a yaƙin neman zaven shugaban ƙasa mai zuwa. A cewar sanarwar da mai baiwa Atiku shawara kan harkokin yaɗa labarai, Paul Ibe ya sanyawa hannu, naɗin na biyu ya fara aiki nan take. Malaye ɗan siyasa ne kuma ɗan majalisar dattawa ta 8, wanda ke wakiltar mazaɓar Kogi ta Yamma. Ya fito daga Ayetoro Gbede da ke ƙaramar hukumar…
Read More
Rundunar Sojojin Nijeriy ba ta ɓangaranci ce ba – Janar Ali

Rundunar Sojojin Nijeriy ba ta ɓangaranci ce ba – Janar Ali

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Manjo Janar Ibrahim Ali, Kwamandan Operation Safe Heaven (OPSH) mai wanzar da zaman lafiya a Filato da kewaye, ya ce, sojoji za su kasance na al’umma da kuma yin adalci ga kowa wajen tabbatar da tsaron ƙasa. Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa, tawagar ta OPSH tawaga ce da ke da alhakin tabbatar da tsaro da rayuka da dukiyoyi a Filato da Bauchi da kuma wasu sassan kudancin Kaduna. An kafa ta ne a shekarar 2010 kuma ta ƙunshi Sojojin Nijeriya na Ruwa, Sama, Jami'an ’yan sanda, jami'an NSCDC da jami'an tsaro na farin…
Read More
Ya kamata gwamnati ta ƙara wa’adin rajistar zaɓe, cewar ’Yar takarar kansila a Sakkwato

Ya kamata gwamnati ta ƙara wa’adin rajistar zaɓe, cewar ’Yar takarar kansila a Sakkwato

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato An bayyana buƙatar da ke akwai ga Gwamnatin Tarayya da ta duba yuwar ƙara wa'adin ci gaba da rajistar masu zaɓe, da hukumar INEC ta dakatar. Wata 'yar takarar kansila a mazaɓar Sanyinnan dake Ƙaramar Hukumar mulkin Tanmbuwal Hajiya Daraja Shehu Sanyinnan ce ta yi wannan kiran cikin wani bayani da ta fitar. Ta bayyana cewa ƙara lokacin rajistar masu zaɓen zai bayar da dama ga waɗanda suka kai munzalin jefa ƙuri'a yankar rijistar domin su samu damar jefa ƙuri'a a babban zaɓen gamagari da ke tafe. Haka ma Daraha Shehu ya yaba wa matar…
Read More
Sakkwato za ta kashe Naira biliyan 12 wajen sanya na’urorin kiwon lafiya a asibitin koyarwar jihar

Sakkwato za ta kashe Naira biliyan 12 wajen sanya na’urorin kiwon lafiya a asibitin koyarwar jihar

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato Gwamnatin Jihar Sakkwato ta bayyana cewa a mako mai zuwa ne za a soma sanya kayan aiki ga asibitin koyarwa ta Jami'ar jihar. Kwamishinan Lafiya na Jihar Sakkwato Dr. Ali Mohammad Inname ne ya sanar da haka a yayin gudanar da wani taro da wakilan kamfanin da aka bai wa aikin Thomat Company Nigeria Ltd, taron da ya gudana a harabar asibitin. Dr. Muhammad Ali Inname, ya ce wannan ya biyo bayan amincewar Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na cefano kayakin tare da sanya su, kuɗin da suka kai kimanin Naira Biliyan 12. A cewarsa, za…
Read More
Harin jirgin ƙasa: Har yanzu ni masoyin Buhari ne, inji fasinjan da ya kuɓuta

Harin jirgin ƙasa: Har yanzu ni masoyin Buhari ne, inji fasinjan da ya kuɓuta

Daga SANI AHMAD GIWA Ɗaya daga cikin mutanen da suka kuɓuta daga hannun 'yan bindigar jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna, Barista Hassan Usman, ya ce har yanzu shi masoyin Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ne. A ranar 28 ga watan Maris, wasu ‘yan bindiga suka kai hari kan wani jirgin ƙasa da ke kan hanyar Kaduna, inda aka kashe mutane da dama, aka kuma yi awon gaba da wasu. Hassan na daga cikin fasinjoji huɗu da aka sako daga hannun masu garkuwar a ranar 25 ga watan Yuli. Da yake magana a wata hira da ICIR, ya ce duk da cewa…
Read More
2023: INEC za ta yi amfani da dokokin zaɓe ba tare da tsoro ba – Yakubu

2023: INEC za ta yi amfani da dokokin zaɓe ba tare da tsoro ba – Yakubu

Daga SANI AHMMAD GIWA a AbujaHukuma Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, za ta yi taka-tsan-tsan wajen aiwatar da dokoki, musamman Dokar Zaɓe ta 2022, ba tare da tsoro ko son rai ba, don tabbatar da sahihin zaɓe, gaskiya da adalci a 2023. Shugaban hukumar ta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka a ranar Laraba a Abuja, a wajen taron tunawa da Marigayi Darakta Janar na Cibiyar Zaɓe, TEI, Farfesa Abubakar Momoh, wanda ya rasu a ranar 29 ga Mayu, 2017. Mista Yakubu ya samu wakilcin Farfesa Abdullahi Zuru, kwamishinan ƙasa kuma shugaban hukumar zaɓe ta ƙasa.…
Read More
‘Yan sanda za su fara kai samame dazuka da gine-ginen da ba kowa a Abuja

‘Yan sanda za su fara kai samame dazuka da gine-ginen da ba kowa a Abuja

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 'Yan sandan Birnin Tarayyar Nijeriya Abuja sun fara hai samame dazuzzuka da gine-ginen da babu kowa a cikin gari da unguwannin bayan gari. Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan Josephine Adeh ne ya faɗi hakan a ranar Laraba, kamar yadda kafar yaɗa labaran Channel ta ruwaito. A yayin da take ƙaryata jita-jitar cewa akwai mafakar masu garkuwa da mutane a cikin Abuja, ta ce a kwanaki masu zuwa mazauna birnin za su ga an tsaurara matakan tsaro. Harin ya zo ne ƙasa da sa'a 24 ba bayan da rundunar 'yan sanda ta yi…
Read More
An yi jana’izar Kwamishinan Ciniki da Masana’antu na Jihar Jigawa, Alhaji Salisu Zakari

An yi jana’izar Kwamishinan Ciniki da Masana’antu na Jihar Jigawa, Alhaji Salisu Zakari

Daga WAKILINMU A ranar Asabar da ta gabata ɗaruruwan mutane daga sassa daban-daban na faɗin ƙasar nan suka halarci jana'izar Kwamishinan Ciniki da Masana'antu na Jihar Jigawa, Alhaji Salisu Zakari (Cigarin Haɗejia) a fadar Mai Martaba Sarkin Haɗejia. Jana'izar da aka gudanar da ƙarfe 11 na safe ta samu halarta manya 'yan siyasa da masu sarauta da sauran al'ummar garin Haɗejia. Rasuwar marigayin ta jijjiga al'umma gani irin gudunmawar da yake bayarwa a sarautar ƙasar Haɗejia da ma cigaban Jihar Jigawa. A shekarar da ta gabata Masarautar Haɗejia ta naɗa shi sarautar Ci-garin Haɗejia na farko biyo bayan ɗimbin nasarorin…
Read More
Kashi 35 na gonaki a Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma sun fi ƙarfin manomanmu – Iliyasu Ishakh

Kashi 35 na gonaki a Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma sun fi ƙarfin manomanmu – Iliyasu Ishakh

Daga BABANGIDA A GORA a Kano Da yawan gonakin manoma mazauna Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas sun gagari masu su wajen nomasu a cikin shekarun da matsalolin tsaro suke ƙara ta'azzara a Nijeriya. Hakan ya fito ne daga bakin wani matashi mai suna Mista Iliyasu Ishak da ya ke kan gaba wajen koya wa manoma hanyoyi da dabarun noma da ma fahimtar da su sirrin tsirrai a kusan yankin Arewa a wata zantawa da manema labarai a Kano. Ishak wanda ya ce babu abinda zai iya kawo cigaba a wannan harka ta noma face masu ruwa da tsaki…
Read More
An kama mutum shida kan zambar mutane a shafin masu auren jinsi a Nijeriya

An kama mutum shida kan zambar mutane a shafin masu auren jinsi a Nijeriya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 'Yan Sandan Jihar Nasarawa a Arewa ta Tsakiyar Nijeriya sun kama mutum shida da ake zargin suna amfani da wani shafin intanet suna zambar mutanen da suke auren jinsi ɗaya. An ce waɗanda ake zargin suna amfani da shafin ne don neman amincewar mutane kafin daga bisani su zambace su. Kamen ya zo ne bayan wani da abun ya shafa ya ce an ɗauki hotunan tsiraicinsa, kuma an yi masa barazanar yaɗa hotunan idan bai ba da kuɗi ba. An ce lamarin ya faru ne a unguwar Masaƙa, a Ƙaramar Hukumar Karu da ke…
Read More