Labarai

Dole sojoji su yi bayani kan maƙudan kuɗaɗen da muka ba su – Osinbajo

Dole sojoji su yi bayani kan maƙudan kuɗaɗen da muka ba su – Osinbajo

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Mataimakin Shugaban Nijeriya Yemi Osinbajo ya buƙaci sojojin ƙasar da su yi wa jama’a bayani a kan irin maƙudan kuɗaɗen da gwamnati ta ba su domin gudanar da ayyukan tsaro a ƙarƙashin shugabancin Muhammadu Buhari. Osinbajo ya ce jama’ar ƙasa na da hurumin sanin irin maƙudan kuɗaɗen da wannan gwamnati ta ware domin tunkarar matsalolin tsaron da suka addabi Nijeriya wanda ke kai wa ga rasa dubban rayuka, don kore shakku dangane da yadda gwamnati ke fuskantar ƙalubalen tsaro. Mataimakin shugaban ƙasar ya ce abin takaici ne kowanne lokaci idan an yi maganar tsaro,…
Read More
Giwa ta halaka mace, kuma ta bi gawar ta tattake ana tsaka da jana’iza

Giwa ta halaka mace, kuma ta bi gawar ta tattake ana tsaka da jana’iza

Ba ɓoyayye ba ne cewa giwaye suna daga cikin dabbobin da suka fi saurin shaƙuwa da mutane a duniyar nan, tare da samun shaidu da yawa na waɗannan halittun da ke nuna farin ciki, baƙin ciki, fushi, tausayi, har ma da ƙauna. Amma sai dai a Indiya wata giwa ta kashe wata mata mai shekara 70 sannan ta je ta tattake gawarta a yayin jana’izarta. Giwar ta tsere bayan ta yi wa matar mai suna Maya Murmu aika-aikar a lokacin da ta ke tara ruwa a ƙauyen Raipal da ke Gabashin Indiya, inji ’yan sanda. Matar ta rasu a asibiti…
Read More
Mai gadin kasuwa ya sace wayoyin maƙudan kuɗaɗe

Mai gadin kasuwa ya sace wayoyin maƙudan kuɗaɗe

Dubun wani mai gadi ta cika bayan ya saci wayoyin hannu da kuɗinsu ya kai Naira miliyan ɗaya da dubu ɗari biyar a kasuwar da ya ke aikin gadi. An gurfanar mai gadin, mai shekaru 25 a gaban kotun Mai Shari’a O. A. Taiwo, na kotun da ke Ikeja Jihar Legas. Ana tuhumar mai gadin da aikata laifuka huɗu, haɗin baki, sata, fashi, da shiga wuri ba da izini ba, amma ya musanta zarge-zargen. Ɗan sanda mai gabatar da kara, Insfekta Raphael Donny, ya faɗa wa kotun cewa mai gadin tare da abokansa sun balla shagon wata ’yar kasuwa mai…
Read More
An gano Naira miliyan 540 a asusun malamar firamare

An gano Naira miliyan 540 a asusun malamar firamare

Wata Babbar Kotu da ke zamanta a Abuja, ta bai wa Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC), umarnin karɓe Naira miliyan 120 daga hannun wata malamar makarantar firamare, Roseline Egbuha, da abokan aikinta da aka samu a asusun ajiyarta na banki. Kuɗaɗen da aka ƙwace, da kuma motoci sun kai Naira miliyan 540 da aka gano a wajen matar, wadda malama ce a makarantar firamare ta Ozala da ke Abagana a Jihar Anambra. Malamar da ke karɓar albashin N76,000 duk wata a lokacin da ICPC ta kama ta a 2020, ta ɓoye Naira miliyan 540 a asusun ajiyarta…
Read More
An sako Dariye da Nyame daga kurkuku

An sako Dariye da Nyame daga kurkuku

Daga BASHIR ISAH An sako tsoffin gwamnonin Jihar Filato da Taraba, wato Sanata Joshua Dariye da Jolly Nyame daga Gidan Gyaran Hali na Kuje, Abuja. Majiyar Jaridar Daily Trust ta ce, an sako tsoffin gwamnonin ne da misalin ƙarfe 2:15 na rana a ranar Litinin. Idan ba a manta ba, a zaman da dattawan ƙasa suka yi watanni huɗu da suka gabata ƙarƙashin agorancin Shugaba Muhammadu Buhari, Majalisar ta amince da yi wa su biyun afuwa. Majiyar ta ce, "An yi musu afuwa ne bisa dalilin rashin lafiya da tsufa da ɗa'ar da suka nuna a zaman kurkukun da suka…
Read More
Kamfanin siminti na BUA ya tallafa wa lauyukan dake maƙwabtaka da shi

Kamfanin siminti na BUA ya tallafa wa lauyukan dake maƙwabtaka da shi

Daga AMINU AMANAWA minu a Sakkwato A wani mataki na tallafawa ƙauyukan dake maƙotaka da shi, kamfanin sarrafa siminti na BUA ya samar da asibiti, makaranta, rijiyar burtsatse dama masallaci ga lauyukan Gidan Boka da Gidan Marafa dake a Ƙaramar Hukumar Mulkin Wamakko. Da yake hannun ta kayan ka al'ummomin ƙauyukan shugaban kamfanin, Yusuf Binji ya bayyana cewa wannan ƙoƙari da kamfanin ya yi na daga cikin irin gudunmawar da yake bayarwa ga al'ummomin dake maƙotaka da shi. Binji wanda shugaban sashen hulɗa da jama'a na kamfanin Sada Suleiman ya wakilta, ya bayyana cewa baya ga wannan sama da ƙauyuka…
Read More
Gwamna Tambuwal ya yi sauye-sauye a majalisar zartarwarsa

Gwamna Tambuwal ya yi sauye-sauye a majalisar zartarwarsa

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya aminta da aikewa da sababbin kwamishinan da ya naɗa a ma'aikatun su tare da yin garambawul ga wasu dake kai. Sababbin mambobin majalisar zartaswa ta jiha da gwamna ɗin ya tura a ma'aikatun su sun haɗar da Dahiru Yusuf Yabo, da aka tura ma'aikatar kula da albarkatun ruwa ta jiha, Akibu Dalhatu yaɗa labarai da wayar da kan al'umma, da kuma zai kula da ma'aikatar matasa da wasanni kari da ta farkon, Bashir Muhammad Lambara, albarkatun ƙasa, yayin da Abdullahi Abubakar Dange, aka aike da shi a ma'aikatar kula da…
Read More
2023: Zan bada kaso 40 na muƙamai ga matasa da mata – Atiku

2023: Zan bada kaso 40 na muƙamai ga matasa da mata – Atiku

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato Ɗan takarar shugabancin Nijeriya na Jam'iyyar PDP a zaɓen 2023 kuma tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya bai wa matasan Nijeriya tabbacin barin kyakkyawan tarihi gare su, idan aka ba shi damar jagorantar al'amuran ƙasar. Atiku Abubakar ya bada wannan tabbaci ne lokacin da ya karvi baƙuncin tawagar shugannin PDP sabon ƙarni ƙarƙashin jagorancin babban daraktan ta Audu Mahmud a gidansa dake Abuja. Ɗan takarar shugabancin ƙasar ya sake jaddada aniyarsa kamar yadda ta ke ƙunshe cikin kundin manufofinsa, na bai wa matasa dama a gwamnatinsa ta hanyar ware musu kaso 40, inda kuma…
Read More
Bankin Duniya da Hukumar Ƙidaya sun horar da ’yan jarida kan yawan al’umma don inganta rayuwa

Bankin Duniya da Hukumar Ƙidaya sun horar da ’yan jarida kan yawan al’umma don inganta rayuwa

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Legas Bankin Duniya da Hukumar Ƙidaya ta Nijeriya (NPC) sun shirya wa wasu zaɓaɓɓun ’yan jarida horarwa kan kula da yawan al’umma, don inganta rayuwar ’yan Nijeriya. An shirya horon na kwana uku ne a otel ɗin Lagos Intercontinental da ke Birnin Ikko a ranakun Litinin, 17 zuwa Laraba, 21 ga Yuli, 2022. A ranar Litinin an fara da gabatar da maƙasudin taron ne, inda shugabannin jami’an Bankin Duniya da na Hukumar NPC suka gabatar da jawabai tare da tattaunawa da mahalarta taron kan alƙiblar da ta kamata ’yan Nijeriya su sanya a gaba kan…
Read More
Ƙungiyar NAF ta yi martani ga matasan Arewa masu yekuwar a tsige Janar Monguno

Ƙungiyar NAF ta yi martani ga matasan Arewa masu yekuwar a tsige Janar Monguno

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja Ƙungiyar Arewa Ina Mafita ta yi kakkausan martani ga wata ƙungiyar matasan arewa mai suna ‘Arewa Youth Assembly bisa kira da suka yi na murabus ɗin mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsrao, Janar Babagana Mongonu. Rahotanni sun ruwaito kakakin ƙungiyar, Mohammed Danlami ne ya yi wannan kira a wata takardar sanarwar manema labarai da ya rattaba wa hannu a ranar Litinin ɗin da ta gabata, inda ƙungiyar tasu ta nemi Janar Monguno da ya yi ritaya ko Shugaba Buhari ya tsige shi. Sai dai a yayin mayar da martani ga wannan matsaya…
Read More