Labarai

An sace ‘yan Chana da kashe jami’an tsaro a Jihar Neja

An sace ‘yan Chana da kashe jami’an tsaro a Jihar Neja

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wasu 'yan bindiga sun kai hari wata mahaƙar ma'adinai a Jihar Neja, inda suka sace ma'aikata 'yan ƙasar Chana aƙalla huɗu, tare da kashe jami'an tsaro aƙalla shida wazanda suka ƙunshi 'yan sanda da sojoji da kuma 'yan sintiri na bijilante. Kwamishinan 'yan sanda na jihar Bala Kuryas, wanda ya tabbatar wa manema labarai, ya ce tuni aka tura jami'ai domin ganowa tare da ceto waɗanda aka sace a wani yanki na Ƙaramar Hukumar Shiroro. Sai dai kuma wata majiya ta shada wa BBC, cewa sojoji 4 da 'yan sandan sintiri 4 da kuma…
Read More
Ansaru ta haramta harkokin siyasa a Birnin Gwari

Ansaru ta haramta harkokin siyasa a Birnin Gwari

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ƙungiyar Ansaru ta haramta duk wasu harkoki da ke da alaqa da siyasa a yankin Ƙaramar Hukumar Birnin Gwari ta Jihar Kaduna. Ƙungiyar cigaban masarautar yankin ta ce, yanzu haka ƙungiyar ta shimfiɗa wasu sharuɗɗa da suka dace da salon shugabancinta, kuma duk wanda aka samu da saɓa su, yana iya fuskantar hukunci mai tsanani. Bayanan da BBC ta tattara sun bayyana cewa, ƙungiyar ta raba wa jama’a wani saƙo da ke ƙunshe da dukkan manufofinta, ciki har da na kawo ƙarshe tsarin dimukraɗiyya da kuma harkokin siyasa a yankin bakiɗaya. A yanzu dai…
Read More
Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 82 a Zamfara

Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 82 a Zamfara

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Hedikwatar Tsaro (DHQ) a ranar Alhamis, ta bayyana cewa, wani farmakin da rundunar sojin sama ta 'Operation HADARIN DAJI' ta kai ta sama ta kashe ’yan ta’adda aƙalla 82 yayin da wasu da dama suka samu raunuka daban-daban a ƙauyen Ƙofar Ɗanya da ke ƙaramar hukumar Bukkuyum a Jihar Zamfara. Rundunar sojin ta kuma ce, an kama ɓarayin mai 26 da dakarun 'Operation DAKATAR DA BARAWO' da 'OCTOPUS GRIP' suka kama a yankin Neja Delta na ƙasar nan. Daraktan ayyukan yaɗa labarai na tsaro, Manjo Janar Benard Onyeuko ne ya bayyana haka a lokacin da ya…
Read More
Ƙara wa’adin rijistar zaɓe dama ce ga al’ummar Yobe – Hon. Shariff Abdullahi

Ƙara wa’adin rijistar zaɓe dama ce ga al’ummar Yobe – Hon. Shariff Abdullahi

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN a Damaturu Ɗan takarar kujerar Gwamnan jihar Yobe a ƙarƙashin inuwar Jam'iyyar PDP, Hon. Shariff Abdullahi ya yaba da matakin da Hukumar Zaɓe mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta ɗauka na ƙara wa'adin rijistar katin zaɓe zuwa ƙarshen watan Yuni, 2022. Tare da kira ga ilahirin al'ummar jihar Yobe da qasa baki ɗaya su yi amfani da wannan dama. Ya sanar da hakan a takardar manema labarai mai ɗauke da sa hannunsa tare da bayyana cewa, "mun yaba wa matakin da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta ɗauka na ƙara lokacin rijistar zaɓe…
Read More
Majalisar Dattawa ta tabbatar da sabbin ministocin Buhari

Majalisar Dattawa ta tabbatar da sabbin ministocin Buhari

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Majalisar dattawa a ranar Laraba ta tabbatar da naɗin ministoci bakwai da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya miƙa mata a makon jiya. Waɗanda aka tantance sun haɗa da Ikoh Henry Ikechukwu daga jihar Abia da Umana Okon Umana daga jihar Akwa Ibom da Ekumankana Joseph Nkama daga jihar Ebonyi da kuma Nana Opiah daga jihar Imo . Sauran sun haɗa da Umar Ibrahim El – Yakub daga jihar Kano, Adenola Adewole Adegoroye daga jihar Ondo da Udum Udi daga jihar Ribas. Tabbatar da waɗanda aka naɗa ya biyo bayan tsauraran matakan tantancewa na tsawon sa'o'i huɗu…
Read More
Ta raba harshenta biyu don ɗanɗana Pepsi da Koka-kola lokaci guda

Ta raba harshenta biyu don ɗanɗana Pepsi da Koka-kola lokaci guda

Wata mawaƙiya mai suna Brianna Mary Shihadeh mai sha’awar gyaran jiki wadda ta raba harshenta biyu ta bayyana yadda za ta iya ɗanɗana abubuwa biyu daban-daban a lokaci guda.Hakan dai ya sa mutane suka yi mamakin irin fasaharta wajen bambance ɗanɗano da harshenta da ta raba. A kwanakin nan ta bar mutane cikin mamaki bayan ta ɗanɗana ruwan lemon biyu a lokaci guda, inda ta sa rabin harshenta a cikin kowane kofin gilashi. Bayan da aka wallafa bidiyon Brianna Manhajar TikTok wanda ya ɗauki hankalin jama’a sosai, Brianna, wacce ke zaune a Kudancin Jihar Kalifoniya a Amurka, bidiyonta ya samu…
Read More
Sabon Alƙalin Alƙalai, Ariwoola: Mutumin da ya soma makaranta bayan shekara ɗaya da haihuwa?

Sabon Alƙalin Alƙalai, Ariwoola: Mutumin da ya soma makaranta bayan shekara ɗaya da haihuwa?

Daga BASHIR ISAH 'Yan Nijeriya ci gaba da ce-ce-ku-ce da kuma nuna mamaki kan lamarin shekarar haihuwa da ta soma makaranta kamar yadda ya shafi sabon Alƙalin Alƙalai na ƙasa, Jastis Olukayode Ariwoola. Jim kaɗan bayan rantsar da shi a matsayin muƙaddashin Alƙalin Alƙalai, takardun bayanin kai da Ariwoola ya miƙa sun nuna an haife shi ne ran 22 ga Agustan 1958 a Jihar Oyo sannan ya fara makarantar firamari a 1959, wato bayan shekara ɗaya tak da haihuwansa ke nan. Kazalika, takardun nasa sun nuna ya halarci Muslim Modern School daga 1968 zuwa 1969, kana ya tafi sakandaren Ansar-Ud-Deen…
Read More
An yanke mata hukuncin zama gidan yari bisa yaɗa bidiyon tsaraicin tsohon mijinta

An yanke mata hukuncin zama gidan yari bisa yaɗa bidiyon tsaraicin tsohon mijinta

Wata kotun majistare da ke zamanta a Ƙaramar Hukumar Minjibir a Jihar Kano ta tasa ƙeyar wata mata ’yar shekara 22 zuwa gidan gyaran hali sakamakon yaɗa bidiyon tsiraici na tsohon mijinta a kafar manhajar WhatsApp.  Mai gabatar da ƙara ya shaida wa kotun cewa, laifin ya saɓa wa sashe na 392 na kundin laifuffuka. Yayin da ta ke mayar da martani kan tuhumar, matar da ake zargin, Nafisa Lawan, ta shaida wa kotun cewa ta sanya bidiyon ne a ɓangaren ‘status’ kuma yadda tsohon mijinta ne kaɗai zai gani, don haka babu wanda ya kalli bidiyon sai shi. Ta…
Read More
Kotu ta wanke shi bayan shekaru 91 da aiwatar masa hukuncin kisa

Kotu ta wanke shi bayan shekaru 91 da aiwatar masa hukuncin kisa

Wani matashin baƙar fata kuma Ba-Amurke da aka yanke wa hukuncin kisa a shekarar 1931 saboda kisan wata farar fata, wata kotu a Pennsylvania ta wanke shi a wannan makon, bayan shafe shekaru da dama 'yar uwarsa ɗaya tilo tana bibiya. Wani alƙali farar fata ne ya yanke wa Alexander McClay Williams mai shekaru 16 a lokacin hukunci cikin sa'o'i huɗu kacal, kuma ya kasance mafi ƙarancin shekaru da tava yankewa hukuncin kisa a jihar ta gabashin Amurka. Amma bayan shekaru 91, wani alƙali ya yi watsi da ƙarar kuma ya bayyana Williams ba shi da wani laifi. ’Yar uwar…
Read More