Labarai

Kotu ta yi watsi da sabon belin da Nnamdi Kanu ya nema

Kotu ta yi watsi da sabon belin da Nnamdi Kanu ya nema

Daga BASHIR ISAH Babbar Kotun Tarayya da Ke Abuja ƙarƙashin jagorancin Alƙali Binta Nyako, ta yi watsi da batun belin da jagoran IPOB, Nnamdi Kanu ya kuma nema. A zaman shari'ar da kotun ta yi ranara Talata, Mai Shari'a Nyako ta ce sake neman belin da Kanu ya yi tamkar cin mutunci ne ga kotu. Ta ce, buƙatar da Kanu ɗin ya gabatar wa kotun wani yunƙuri ne na maida wa kotu hannu agogo baya kan batutuwan da an rigaya an yanke hukunci a kansu. Ta kuma tsaya kai da fata kan lallai sai Kanu ya ba da dalilin da…
Read More
Buhari ya karrama tsohon Alƙalin Alƙalai, Ibrahim Tanko da lambar yabo

Buhari ya karrama tsohon Alƙalin Alƙalai, Ibrahim Tanko da lambar yabo

Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya karrama tsohon Alƙalin Alƙalan Nijeriya wanda ya yi murabus kwanan nan, Ibrahim Tanko da lambar yabo ta ƙasa, wato GCON. Wannan ya faru ne a ranar Litinin da ta gabata a wajen taron rantsar da Jastis Olukayode Ariwoola a matsayin Muƙaddashin Alƙalin Alƙalai na Nijeriya da ya gudana a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja. Da yake jawabi a wajen taron, Buhari ya ce ya karrama Jastis Ibrahim Tanko da lambar yabon ne bisa la'akari da aiki tuƙuru da ya yi wa ƙasa a lokacin da yake riƙe da muƙamin Alƙalin Alƙalai.…
Read More
SERAP ta maka Buhari a kotu kan rashin binciken kuɗaɗen wutar lantarki

SERAP ta maka Buhari a kotu kan rashin binciken kuɗaɗen wutar lantarki

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ƙungiyar Kula da Haƙƙoƙin Zamantakewa da Tattalin Arziki (SERAP) ta shigar da ƙarar shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a gaban kotu saboda gazawarsa wajen gudanar da bincike kan zargin cewa sama da Naira Tiriliyan 11 na nufin samar da ingantaccen wutar lantarki tun shekarar 1999 an sace su, ko kuma an karkatar da su zuwa aljihun gwamnati. Biranen Nijeriya sun sha faɗawa cikin duhu yayin da aka ce na’urar wutar lantarki ta ruguje aƙalla sau uku a cikin watanni biyar, kuma sau 130 a cikin shekaru 7. A cewar Bankin Duniya, rashin ingantaccen wutar lantarki yana jawowa…
Read More
2023: APC ta musanta tara kuɗaɗe don bai wa masu kaɗa ƙuri’a

2023: APC ta musanta tara kuɗaɗe don bai wa masu kaɗa ƙuri’a

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Jam’iyyar APC mai mulki ta musanta wani rahoto da ake yaɗawa cewa, jam’iyyar na shirin tara kusan Naira Tiriliyan 6.5 don sayen ƙuri’u, da bai wa jami’an tsaro cin hanci da kuma Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) don cin zaɓen 2023. Sai dai jam’iyyar APC ta zargi jam’iyyar PDP da cewa ita ce ke da alhakin wannan jita-jita. Da ya ke mayar da martani kan zargin ta hanyar wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran jam’iyyar APC na ƙasa, Felix Morka ya sanyawa hannu a ranar Litinin a Abuja, ya bayyana takardar da aka…
Read More
Alƙalin Alƙalai, Tanko Muhammad ya yi murabus

Alƙalin Alƙalai, Tanko Muhammad ya yi murabus

Daga BASHIR ISAH Alƙalin Alƙalan Nijeriya, Mai Shari'a Tanko Muhammad, ya yi murabus daga aiki. Majiyar tashar Channels Television ta ce Jastis Muhammad ya yi murabus ne a Lahadin da ta gabata saboda dalili na rashin lafiya. Bayanai sun nuna cewa, an yi nisa da shirye-shirye don rantsar da Alƙali mafi girman muƙami a Kotun Ƙoli, wato Jatis Olukayode Ariwoola, a matsayin Alƙalin Alƙalan Nijeriya mai riƙon ƙwarya. Haka nan, bayanan sun ce nan ba daɗewa ba za a sanar da naɗin a hukumance. Kafin yin murabus, rahotanni sun tabbatar da Jastis Muhammad na fama da rashin lafiya sosai. Idan…
Read More
Mutane sun farwa limamin coci kan yi wa Ekweremadu addu’a

Mutane sun farwa limamin coci kan yi wa Ekweremadu addu’a

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Wasu mutane sun bayyana rashin jin daɗinsu kan yadda limamin coci, Johnson Suleman ya yi wa Ekweremadu da matarsa addu’ar Allah ya kuɓutar da su, inda suka yi ta cece-kuce a Manhajar Tuwita. Rundunar ’yan sandan birnin Landan ta kama tsohon mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Ike Ekweremadu tare da matarsa Beatrice bisa zargin haɗa baki da juna na safarar sassan jikin wani yaro. Ekweremadus ya buƙaci ƙodar yaron ga ɗiyarsu, Sonia, wacce ke fama da matsalar ƙoda. Da ya ke mayar da martani ga labarin, Suleman ya rubuta a shafinsa na Tuwita cewa, “an ji labarin…
Read More
Na yi kuskuren ɗaukar Atiku a matsayin mataimakina a 1999 – Obasanjo

Na yi kuskuren ɗaukar Atiku a matsayin mataimakina a 1999 – Obasanjo

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon Shugaban Nijeriya, Cif Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa ɗaya daga cikin kurakuran da ya tafka a rayuwarsa shi ne zaɓar mataimaki a 1999. Obasanjon ya bayyana haka ne a yayin da yake amsa tambayoyi a wani taro na wasu ɗalibai a Abeokuta da ke Jihar Ogun, ranar Asabar 25 ga Yuni, 2022, kamar yadda jaridar Intelregion ta ruwaito. Obasanjo dai shi ne ya yi nasara a zaɓen Shugaban Nijeriya a shekarun 1999 da 2003, inda Atiku Abubakar ya zama mataimakinsa. "Ba zan ce bana kuskure ba, na yi su da yawa," inji Obasanjo.…
Read More
Tsaro: Gwamnatin Zamfara ta buƙaci alummar jihar su ɗauki makamai don kare kai

Tsaro: Gwamnatin Zamfara ta buƙaci alummar jihar su ɗauki makamai don kare kai

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Biyo bayan ƙaruwar ‘yan fashi da makami a Jihar Zamfara, gwamnatin jihar ta umurci mutane da su shirya tare da samun bindigogi domin kare kansu daga ‘yan bindigar. Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da aka raba wa jaridar Blueprint Sunday, mai ɗauke da sa hannun Kwamishinan Yaɗa Labaran Jihar, Ibrahim Dosara. A cewar sanarwar, gwamnati ta umurci kwamishinan ‘yan sandan jihar da ya bayar da lasisi ga duk wanda ya cancanta da kuma buƙatar samun irin waɗannan bindigogi domin kare kansu. “Gwamnati a shirye ta ke ta bai wa mutane dama musamman…
Read More
An shawarci Mahajjatan Nijeriya su kasance jakadu nagari a ƙasa mai tsarki

An shawarci Mahajjatan Nijeriya su kasance jakadu nagari a ƙasa mai tsarki

Daga DAUDA USMAN a Legas An shawarci al'ummar Musulmin Nijeriya musamman maniyyata aikin Hajjin bana da su zama jakadu nagari yayin gudanar da aikin Hajji a ƙasa maitsarki. Sarkin Fawan Ƙaramar Hukumar Amuwo Odofin dake cikin garin Legas, Alhaji Usaini Iliyasu shi ne ya yi wannan kiran yayin da yake zantawa da wakilinmu a ofishinsa da ke cikin kasuwar Amuwo Odofin, sa'ilin da yake yin sallama da wasu mahauta masu niyyar tafiya aikin Hajjin bana. Usaini ya cigaba da cewa a sakamakon waɗansu maniyyata 'yan Nijeriya suna haɗa gudu da susar katara wajen zuwa ƙasa mai tsarki domin su sauke…
Read More