Labarai

Tsohon ministan tsaron Ukraniya ya nemi a yi zaɓen shugaban ƙasa duk da yaƙinsu da Rasha

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tsohon Ministan Tsaron ƙasar Ukraniya, Mykhailo Fedorov ya yi kira da a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa duk da yaƙin da ke tsakanin ƙasar da Rasha, a wani yanayi da za a kira da ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen siyasa da Shugaba Volodymyr Zelenskyy zai iya fuskanta tun bayan fara yaƙin a 2022. Fedorov mai shekaru 35, ya yi wannan kira ne a wani faifan bidiyo da ya fitar a ranar Talata, inda ya ce wajibi ne ƙasar ta dawo da tsarinta na dimukraɗiyya duk da cewa ana cigaba da gwabza yaƙi tsakaninta da…
Read More

Na hannun daman Trump ya faɗi a zaɓen fidda gwanin takarar gwamnan Florida

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Yayin da masu zaɓe suka shirya maye gurbin Gwamna Ron DeSantis mai barin gado, 'yan jam'iyyar Republican sun zaɓi na hannun daman Shugaban Donald Trump, yayin da Democrat suka zaɓi wani ɗan takara daban da ya sauya jam'iyya ya bar tafiyar GOP (Republican) saboda shugaban ƙasar. Saidai kuma masu goyon bayan Democrat sun sake nuna ƙarfinsu na cigaba da samun karɓuwa bayan Rep. Angie Nixon ya lashe zaɓen fidda gwanin ɗan takarar sanata. Amma biyu daga cikin 'ya'yan majalisa na jam'iyyar da suka tsaya takara a karon fari a sababbin gundumomi sun tsallake rijiya…
Read More

‘Davido aka so halakawa’, inji ‘yan sanda kan harin ayarin motocin Gwamnan Osun

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shahararren Mawaƙin Nijeriya, David Adeleke da aka fi sani da Davido, shi ne wanda aka nufa yayin da aka farmaki ayarin motocin Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, a cewar rundunar 'yan sandan jihar. Rahotanni sun bayyana cewa jami'an tsaron da ke tsare gwamnan sun yi musayar wuta da maharan a lokacin da ya kai wa Ataoja na Osogbo ziyara a ranar Laraba. Gwamnan ya kai ziyarar ne jim-kaɗan bayan karɓar shaidar zama gwamna a ofishin Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) da ke jihar bayan sake zaɓarsa. Davido, wanda ɗa ne a gurin Adeleke, yana…
Read More
Sani Tadurga zai jagoranci yaƙin neman zaɓen jam’iyyar ADC a Kebbi

Sani Tadurga zai jagoranci yaƙin neman zaɓen jam’iyyar ADC a Kebbi

Daga JAMIL GULMA a Kebbi Jam'iyyar ADC a jihar ta tsayar da Honarabul Sani Tadurga a matsayin wanda zai jagoranci yaƙin neman zaɓen ta mai zuwa.Wannan ya biyo bayan wani zama da masu ruwa da tsaki suka gudanar a garin Birnin Kebbi ƙarƙashin jagorancin ɗan takarar kujerar gwamnan jihar Alhaji Abubakar Chika Malami SAN ranar Talatar da ta gabata.Da ya ke zantawa da wakilin Jaridar Blueprint Manhaja shugaban jam'iyyar ADC a jihar Kebbi Injiniya Sufiyanu ya bayyana cewaHonarabul Sani Tadurga wanda tsohon mataimakin kakakin majalisar dokoki ta jihar Kebbi ne kuma jigo a siyasar jihar kuma duk an amince da…
Read More
Masarautar Koko ta yaba wa Gwamna Nasir kan ƙirƙiro hakimai takwas

Masarautar Koko ta yaba wa Gwamna Nasir kan ƙirƙiro hakimai takwas

Daga JAMIL GULMA a Kebbi Masarautar Uban ƙasar Koko da ke jihar Kebbi ƙarƙashin jagorancin Alhaji Mohammed Bello Koko II ta yaba wa Gwamna Malam Nasir Idris bisa ga ƙirƙiro sababbin hakimai guda takwas daga cikin masarautar. Ya yi wannan bayanin ne a fadar sa da ke garin Koko sa'ilin da ya ke zantawa da wakilin Jaridar Blueprint Manhaja ranar Larabar da ta gabata.Basaraken ya ce, A madadin sa da ilahirin al'ummar wannan masarautar ta Koko suna miƙa godiya ga mai girma gwamna Malam Nasir Idris da kuma masarautar Gwandu bisa ga wannan gagarumin mataki na ƙara yawan hakimai a…
Read More
Majalisar dokokin Nasarawa ta tantance sabbin kwamishinoni da Gwamna Sule ya naɗa

Majalisar dokokin Nasarawa ta tantance sabbin kwamishinoni da Gwamna Sule ya naɗa

Daga JOHN D. WADA a Lafiya Majalisar dokokin jihar Nasarawa ta tantance tare da tabbatar da sabbin kwamishinoni takwas da gwamnan jihar Injiniya Abdullahi Sule ya gabatar ma ta domin a naɗa su cikin majalisar zartarwa ta jihar. Shugaban majalisar dokokin Rt. Hon. Dr. Danladi Jatau ne ya bayyana haka yau Laraba yayin zaman majalisar a Lafiya bayan an yi tantancewar ga waɗanda aka zaɓa. Shugaban bayan ya taya su murna kan wannan naɗin da ya cancanta ya kuma buƙace su riƙa aiki da gaskiya da riƙon amana bayan an rantsar da su. Wakilin mu a jihar ya kuma ruwaito…
Read More
Gwamna Raɗɗa ya ƙaddamar da rabon hatsi ga masu buƙata ta musamman a Katsina

Gwamna Raɗɗa ya ƙaddamar da rabon hatsi ga masu buƙata ta musamman a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umar Raɗɗa ya ƙaddamar da rabon buhunan hatsi mai nauyin kilogiram 100 ga masu buƙata ta musamman da matan da suka rasa mazajen su a Jihar. Kayan abincin sun haɗa da buhunan masara ,dawa da gero buhu 30,000 kowanne. A jawabin sa Gwamna Dikko Raɗɗa ya bayyana cewa wannan tallafi ba shine na farko ba, ya ce a kwanan baya gwamnati ta tallafa wa masu sana'ar koko da ƙosai da kuma tallafin kuɗi a cikin watan azumin Ramadan. Ya ƙara da cewa gwamnatin sa ta tallafa wa mata 7,220 a…
Read More

FEC ta amince da sanya kuɗaɗen da EFCC ta ƙwato a asusun NELFUND

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Majalisar Zartarwar ta Tarayya (FEC) ta ce ta amince da sakin kuɗaɗen da Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta'annati (EFCC) ta ƙwato ga fannin ilimi ta hanyar sanya su a Asusun bayar da Lamunin Karatu na Ƙasa, NELFUND. Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa ne ya bayyana haka jim-kaɗan bayan zaman da FEC ta gudanar a ranar Laraba a Fadar Shugaban Ƙasa a Abuja, inda ya ce za a sanya kuɗaɗen ne a asusun NELFUND domin ƙarfafa masa wajen sauke nauyin da aka ɗora masa na bai wa ɗalibai aron kuɗin karatu da…
Read More

Yanzu-yanzu: Tinubu ya maye gurbin Didi Walson-Jack da Abel Enitan a matsayin sabon Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaba Bola Tinubu ya naɗa Abel Enita a matsayin sabon Shugaban Ma'aikatan Gwamnatin Tarayya, wanda zai fara a ranar 27 ga Agusta, 2026. Hakan na nufin Enitan zai maye gurbin Misis Didi Walson-Jack a muƙamin, wadda a kwanan nan za ta yi ritaya bayan cika shekaru 60, kamar yadda doka ta tsara. Enitan, wanda ɗan ainihin Jihar Osun ne, shi ne mafi girma kuma Babban Sakatare da Ma'aikatar Ma'aikatan Tarayya, wanda yake da ƙwarewa a harkar gudanarwa da kuma fahimtarsa ga ayyukan sabon nauyin da aka ɗora masa. Ya kasance a matsayin babban sakatare…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: ‘Yan bindiga sun farmaki ayarin motocin Gwamnan Osun yayin da jami’an tsaro suka daƙile harin

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Laraba wasu 'yan bindiga suka farmaki tawagar motocin da ke yi wa Gwamna Ademola Adeleke na Jihar Osun rakiya, jim-kaɗan bayan kai ziyara a fadar Ataoja na Osogbo, Oba Jimoh Oyetunji, lamarin da ya haifar da musayar wuta tsakaninsu da jami'an tsaron gwamnan. Rahotanni sun bayyana cewa, ba-takashin, wanda aka shafe tsawon mintina 12 zuwa 15, ya faru ne bayan gwamnan ya fice daga fadar basaraken, lamarin da ya jefa al'ummar yankin cikin firgici. Gwamnan ya isa fadar mai martaban ne da misalin ƙarfe 3:15 na rana a wani ayarin motoci guda…
Read More