19
Aug
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Rundunar 'Yan sanda a Jihar Kaduna, ta umarci a fara gudanar da cikakken bincike kan wani faifan bidiyo da ya karaɗe kafafen sada zumunta, wanda yake zargin jami'an 'yan sanda suna tilasta wa masu motoci da babura ba su na goro yayin aiki a shingen bincike. Kwamishinan rundunar, Rabi'u Muhammad ne ya bayar da umarnin inda ya buƙaci a gano su waye ne daga cikin 'yan sandan aka gani a bidiyon kuma a gayyato su yayin binciken. A wata sanarwa da Kakakin rundunar, DSP Mansir Hassan ya fitar a ranar Talata, rundunar ta ce…
