19
Aug
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Mataimakin Shugaban Jami'ar Jihar Kaduna (KASU), Farfesa Abdullahi Musa, ya yi watsi da iƙirarin Ƙungiyar Malaman Jami'o'i rushen jami'ar (ASUU-KASU) na cewa sama da malamai 200 sun ajiye aikinsu kan rashin kyawun yanayin aiki, yana mai bayyana zargin a matsayin abin ruɗarwa da bai yi kama da haƙiƙanin al'amari ba. Rahotanni sun bayyana cewa, wannan faɗi-in-faɗa ta samo asli ne bayan wani taron manema labarai da ASUU-KASU ta kira, inda ta yi zargin sama da farfesoshi da lakcarori 200 sun bar aiki da jami'ar bisa rashin kyawun yanayin aiki da gazawar cika alƙawarin aiwatar…
