18
Aug
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Kwamishinan 'Yan sandan Jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori ya gabatar da wasiƙar godiya ga Hajiya Hajara Abdullahi ta Diso Quarters da ke Ƙaramar Hukumar Gwale a jihar, yayin yaba wa ƙoƙarinta na taimaka wa al'umma musamman kan gyara ofishin 'yan sanda na Shiyyar Gwale da ta gudanar. Ya ce, wannan hoɓɓasa da Hajiya Hajara ta yi na wakiltar gagarumar gudumawa ga harkar tsaro a yankin. A cewarsa, tana bayar da tallafi ga ayyukan shiyyoyin 'yan sanda a sassan jihar da nufin inganta wuraren ayyukan jami'ai da bunƙasa lamuran hidimta wa al'umma. Da yake damƙa…
