17
Aug
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Malaman jami'a da suka haɗa da masu muƙamin farfesa da wasu sama da guda 200 ne suka bar Jami'ar Kaduna KASU, bisa rashin ingancin lamuran gudanarwa da rashin aiwatar da yarjejeniyar Gwamnatin Tarayya da Ƙungiyar Malaman Jami'o'i ta Ƙasa (ASUU) ta 2025, inji reshen ƙungiyar na KASU. Rahotanni sun bayyana cewa ASUU reshen KASU ta bayar da wa'adin sati biyu ga hukumomin jami’o’i da sauran masu ruwa da tsaki da su fara aiwatar da yarjejeniyar yadda aka tsara ta, tana mai gargaɗin cewa rashin yin hakan ka iya haifar da yajiin aikin sai baba-ta-gani…
