Labarai

Adeleke ya janye ƙarar EFCC bayan nasara a zaɓen Osun

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Wanda aka sake zaɓa a matsayin Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, ya ce ya umarci Antoni Janar na jihar da ya janye ƙarar da suka shigar akan Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta'annati EFCC, bisa rufe asusun bankin gwamnatin jihar gabanin zaɓen da aka gudanar a ranar Asabar. Adeleke ya bayyana haka ne a wata hira da gidan talabijin na Channels a ranar Lahadi, sa'o'i bayan ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar da Hukumar Zaɓe (INEC) ta yi. Yayin da aka masa tambaya kan halin batun rikicin siyasa…
Read More

‘Jagoran da babu kamarsa’, Tinubu ya taya IBB murnar cika shekara 85

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya miƙa saƙonsa na taya murna ga ɗaya daga cikin manyan ƙasa kuma tsohon shugaban mulkin soji na Nijeriya, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (mai ritaya) yayin da ya cika shekara 85 duniya a ranar 17 ga Agusta, 2026. Tinubu ya bayyana IBB a matsayin jajirtaccen jagora wanda horonsa na aikin soja ya yi gagarumin tasiri a harkar shugabancin Nijeriya bayan juyin mulkin 1985. Shugaban ya bayyana haka ne a wata takarda da ke ɗauke da sanya hannun kakakinsa Bayo Onanuga, ranar Lahadi. A cewarsa, tsohon shugaban ƙasar ya yi wa…
Read More

Davido ya yi amai ya lashe bayan goge wallafar adawar APC ta Shugaba Tinubu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shahararren mawaƙin Nijeriya, David Adeleke da aka fi sani da Davido, ya goge wasu wallafe-wallafen siyasa guda biyu a ranar Asabar 15 ga Agusta, 2026, lamarin da ya jefa masoya da masu sharhi kan harkar siyasa ƙalubalantar dalilinsa na ɗaukar matakin. A ɗaya daga cikin rubutun nasa, Davido ya bayyana cewa daga yanzu iyalansa ba za su sake goyon bayan wani ɗan takarar shugaban ƙasa ba, inda ya sanya hoton kawun nasa kuma gwamnan Jihar Osun a gefen rubutun. A wata ɗaukar fuskar salula ta nuna cewa Davido ya goge wani rubutun ya yi…
Read More

Davido ya magantu yayin da kawunsa ya lashe zaɓen Osun

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Sanannen mawaƙin Nijeriya, David Adeleke da aka fi sani da Davido, ya yi tsokaci bayan nasarar da kawunsa Ademola Adeleke ya samu na sake zama gwamnan jihar Osun. Da yake murna kan al'amarin, Davido ya yi rubutu a shafinsa na X inda ya ce: "We did it, Uncle", wato "Mun cimma nasara, Kawu". Hakan na zuwa ne bayan da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC, ta sanar da Ademola Adeleke na jam'iyyar Accord Party (AP) a matsayin wanda ya lashe zaɓen, wanda aka gudanar a ranar Asabar. Adeleke ya yi nasara ne bayan sakamakon ƙananan…
Read More
Yahaya Augie ya yaba wa gwamnan Kebbi kan zaɓen Ibrahim Augie

Yahaya Augie ya yaba wa gwamnan Kebbi kan zaɓen Ibrahim Augie

Daga JAMIL GULMA a Kebbi Shugaban ƙaramar hukumar Augie Honarabul Yahaya Muhammed Augie ya yaba wa Gwamna Nasir bisa ga zaƙulo Alhaji Ibrahim Augie a matsayin sabon mataimakin gwamnan jihar Kebbi.Ya bayyana haka ne a garin Augie mahaifar sabon ɗan takarar mataimakin gwamnan.Ya ce ba shakka gwamnan ya ɗauko mutum mai dattako da kuma sanin makamar aiki wanda ya goge. Ya bayyana cewa wannan ya nuna irin soyayya da mutuntawar sa da mutanen masarautar Argungu saboda wannan ba ta tsaya ga Ibrahim Augie ko ƙaramar hukumar Augie kaɗai ba ce.Ya kuma bayar da tabbacin goyon bayan sa tare da yin…
Read More
Nagarta ke sa a bai wa mutum sarauta – Sarkin Zabarmawan Kabi

Nagarta ke sa a bai wa mutum sarauta – Sarkin Zabarmawan Kabi

Daga JAMIL GULMA a Kebbi Sarkin Zabarmawan Kabi Honarabul Sama'ila Abdulmumini Kamba (Ganda) tsohon kakakin majalisar dokoki ta jihar Kebbi ya bayyana cewa nagarta ce sanya a bai wa mutum sarauta.Ya yi wannan bayanin ne jim kaɗan bayan kammala naɗin sa a matsayin Kakakin Gwandu a fadar Sarkin Gwandu ƙarshen makon nan lokacin da ya ke zantawa da manema labarai. Alhaji Sama'ila Ganda ya ce na farko dai ya yi aiki da mai martaba Sarkin Kabin Argungu a baya wanda kuma basaraken ya ga irin ƙoƙarin da ya ke yi a wajen aiki da kuma fafutukar da ya ke yi…
Read More
Ƙirƙiro masarautu ke janyo mutane kusa da gwamnati – Garba Zarummai

Ƙirƙiro masarautu ke janyo mutane kusa da gwamnati – Garba Zarummai

Daga JAMIL GULMA a Kebbi Sabon Uban ƙasar Shiko Alhaji Garba Zarummai Fana ya bayyana ƙirƙiro masarautu a matsayin wata hanya ta kusantar al'umma ga gwamnati.Ya bayyana haka ne lokacin da ya ke zantawa da wakilin Jaridar Blueprint Manhaja a garin Fana. Sabon basaraken ya bayyana cewa sanin kowa ne yanzu akwai yawan al'umma saɓanin inda aka fito saboda haka akwai buƙatar al'ummar da a ke jagoranci su kusanci hukumomi tun kama daga masarautu zuwa gwamnati. Ya kuma yi kira ga hakiman sa da limamai da ke yankin masarautar sa da su ba shi goyon baya domin samun nasara a…
Read More

Babban ɗan Ganduje ya koma APC bayan watanni uku da shiga NDC ta Kwankwaso

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Abdulaziz Umar Ganduje, wato ɗan tsohon gwamnan Jihar Kano kuma tsohon Shugaban Jam'iyyar APC na Ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya koma jam'iyyar bayan ficewa daga NDC. Abdulaziz ya koma APC a hukumance ne a Gundumarsa ta Ganduje da ke Ƙaramar Hukumar Dawakin Tofa a ranar Lahadi, inda ya karɓi katinsa na zama mamba. An ga yadda wasu jami'an jam'iyya da magoya baya suka halarci wajen sauya sheƙar, matakin da ake gani a matsayin jaddada biyayyarsa ga tsarin APC a Kano. Da fari Abdulaziz ya shiga jam'iyyar NDC tare da yankar tikitin shiga takarar kujerar…
Read More

NAHCON ta ankarar da al’umma kan ‘yan damfara masu siyar da kujerun Hajjin 2027

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya NAHCON, ta nuna damuwa bisa ayyukan wasu ɓata-gari da ke yi mata sojan-gona wajen damfarar mutane ta hanyar karɓar kuɗaɗe daga masu aikin jigila da maniyyata da sunan samun kujerar Hajjin 2027 kai-tsaye. A wata sanarwa da ta fitar a Abuja a ranar Lahadi, NAHCON ta yi gargaɗin cewa babu wani mutum, wakili, jami'in jigila ko ɗan shiga tsakani da ta amince wa karɓar kuɗi, kuɗin wakilci ko ƙarin wani kuɗi don mallaka, tabbatarwa ko bayar da kujerun hajji. Hukumar ta ce, ana gudanar da aikin raba kujeru ne bisa…
Read More