Labarai

El-Rufa’i ya shigar da ƙarar neman diyyar biliyan N10 bayan zargin ICPC da nesanta shi da iyalansa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Lahadi tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i shigar da sabuwar ƙara akan Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ICPC, inda ya nemi a biya shi diyyar Naira biliyan 10. El-Rufa'i ya yi ƙorafin ne akan ICPC bisa zargin ta da hana shi ganawa da matarsa, Aichatou Asabe; da ɗansa, Abba El-Rufa'i yayin da yake tsare. A ƙarar, wadda lauyansa, Ubong Akpan ya shigar, El-Rufa'i ya zayyano shugaban ICPC da Antoni Janar na Ƙasa (AGF) a matsayin waɗanda aka shigar ƙara na biyu da na uku. Tsararren tsohon gwamnan, wanda ya yi…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: Arsenal ta lashe Community Shield na 2026 bayan lallasa City

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal ta yi nasarar lashe kyautar wasan Community Shield na 2026 bayan casa Manchester City da ci 3 da 0 a Cardiff, Babban Birnin ƙasar Wales. Hakan na zuwa ne ƙasa da mako guda da fara wasannin sabuwar kakar wasa ta gasar Premier League ta Birtaniya kuma ta 2026/2025. Ɗan wasa Riccardo Calafiori ne ya ba wa Arsenal damar jan ragamar wasan bayan ƙasa da minti ɗaya da take wasan a lokacin da Lewis Skelly ya gara masa ƙwallo cikin salo mai ban ƙaye. Ana tsaka da wasan ne a…
Read More

Adeleke ya jinina wa Tinubu kan sahihin zaɓe a Osun, ya sabunta goyon bayansa gare shi a zaɓen 2027

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamna Ademola Adeleke na Jihar Osun ya jinina wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa abin da ya kira da "sahihin zaɓen gwamna" da aka gudanar a jihar, yayin da ya kuma jaddada goyon bayansa ga shugaban na neman a sake zaɓar sa a karo na biyu a zaɓen 2027. Adeleke ya bayyana haka ne a ranar Lahadi jim-kaɗan bayan Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta sanar da sh ia matsayin wanda ya lashe zaɓen, wanda aka gudanar a ranar Asabar 15 ga Agusta, 2026, lamarin da ya ba shi damar koma wa kan karagar…
Read More

Yanzu-yanzu: Tinubu ya taya Adeleke murnar lashe zaɓen Osun yayin da Atiku da Obi suka ce faɗuwar APC ta nuna zaɓin al’umma

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya taya Gwamna Ademola Adeleke na Osun murna bayan sake samun nasara a zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar a jiya Asabar, yayin da 'yan ɓangaren adawa su Atiku Abubakar da Peter Obi suka bayyana sakamakon a matsayin tasirin zaɓin masu zaɓen jihar. Adeleke ya samu nasarar ne bayan samun ƙuri’a 511,067, yayin da Oyebamiji ya samu 444,815. Najeem Salaam na ADC ya samu 17,180 a zaɓen, wanda aka gudanar a faɗin ƙananan hukumomi 30 na jihar. Gwamnan ya shiga zaɓen ne a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar Accord Party bayan ficewa…
Read More

An yi wa shafin X na Hedikwatar Tsaro kutse

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hedikwatar Tsaron Nijeriya DHQ, ta tabbatar da cewa sashen sahfinta na X ya fuskanci kutsen 'yan damfara, inda ta gargaɗi al'umma da su ƙaurace wa yarda da dukkan wata sanarwa da aka ɗora a kai har sai an shawo kan al'amarin. Kakakin hedikwatar, Manjo-Janar Sama'ila Uba ne ya sanar da haka a yammacin ranar Asabar a wata takarda da ya fitar. An ruwaito cewa, an gano haka ne bayan ganin wasu wallafa na tururuwa a shafin, waɗanda suka ƙunshi bayanan harkar kirifto da ba su da alaƙa da sojojin Nijeriya. Ya ce, shafin da…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: INEC ta sanar da Adeleke na AP a matsayin wanda ya lashe zaɓen Osun

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC, ta sanar da Gwamna mai ci, Ademola Adeleke a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan Jihar Osun, bayan doke abokin karawarsa na jam'iyyar APC, Bola Oyebamiji. Baturen zaɓen jihar ne ya sanar da Adeleke na Accord Party a matsayin wanda ya samu nasara a zaɓen a safiyar yau Lahadi bayan kammala zaɓen a jiya Asabar a ƙananan hukumomi 30 na faɗin jihar. Oyebamiji, wanda shi ne tsohon kwamishinan kuɗin jihar, shi ya zo na biyu, yayin da Najeem Salaam na jam'iyyar ADC ya zo na uku. Jimillar jam'iyyun siyasa…
Read More
Jagoran Iran ya naɗa sabbin shugabannin soji

Jagoran Iran ya naɗa sabbin shugabannin soji

Jagoran Iran, Mojtaba Khamenei, ya naɗa manyan hafsoshin sojin ƙasar guda biyu a wasu muƙamai masu matukar muhimmanci, yayin da ƙasar ke ci gaba da fuskantar matsin lambar tsaro da rikicin soja a yankin Gabas ta Tsakiya. A cikin sanarwar da ofishinsa ya fitar ranar Litinin, Khamenei ya naɗa Manjo Janar Ali Abdollahi a matsayin sabon shugaban hafsoshin rundunar sojin Iran, yayin da Birgediya Janar Ahmad Vahidi ya zama sabon kwamandan rundunar Islamic Revolutionary Guard Corps (IRGC). Kafin naɗin nasa, Abdollahi shi ne shugaban hedikwatar Khatam al-Anbiya ta tsakiya, wata babbar cibiyar rundunar sojin Iran da ke da alhakin haɗa…
Read More
Kotun Syria ta yanke wa tsohon shugaban ƙasar Bashar Assad hukuncin kisa

Kotun Syria ta yanke wa tsohon shugaban ƙasar Bashar Assad hukuncin kisa

Kotun hukunta manyan laifuka da ke Damascus, babban birnin Syria, ta yanke wa tsohon shugaban kasar, Bashar al-Assad, hukuncin kisa kan laifukan da aka danganta da yaƙin basasar ƙasar. Kotun ta same shi da laifin kisan gilla da aka shirya tun da wuri, tare da ɗora masa alhakin amfani da hukumomin gwamnati wajen aikata laifukan yaƙi da laifukan cin zarafin bil’adama. An yanke hukuncin ne ba tare da Assad ya halarta ba, domin tun bayan kifar da gwamnatinsa a watan Disambar 2024 ya tsere zuwa Rasha, inda ya samu mafaka. Hukuncin ya kasance na musamman a tarihin Syria bayan faɗuwar…
Read More
Mutane 14 sun mutu bayan rushewar wani wurin haƙar ma’adinai a Afirka ta Kudu

Mutane 14 sun mutu bayan rushewar wani wurin haƙar ma’adinai a Afirka ta Kudu

Aƙalla mutane 14 da ake zargin masu hakar ma’adinai ne ba bisa ka’ida ba sun mutu, yayin da wasu takwas suka jikkata bayan wani tsohon wurin hakar ma’adinai ya rushe a Afirka ta Kudu. Lamarin ya faru ne a daren Litinin a kusa da Rustenburg, da ke lardin North West na ƙasar, a lokacin da mutanen ke aikin neman wasu karafa daga cikin tarkacen wani tsohon wurin hakar ma’adinai. Kwamishinan ’yan sandan lardin, Arthur Peter Adams, ya ce har yanzu ba a san adadin mutanen da ka iya kasancewa a ƙarƙashin tarkacen ba. Ya ce jami’an ceto na ci gaba…
Read More
Matashi ya hau saman asibiti yana kwaikwayon Mala’ikan Mutuwa don tsorata marasa lafiya

Matashi ya hau saman asibiti yana kwaikwayon Mala’ikan Mutuwa don tsorata marasa lafiya

Wasu abubuwan da ke faruwa a duniyar nan kan kasance masu ban mamaki har su sa mutum ya tsaya yana tambayar kansa yadda aka yi abin ya faru. A wannan makon, wani matashi a Wales ya jawo hankalin jama’a bayan ya hau saman wani asibiti sanye da baƙaƙen kaya masu kama da na Ma'ikan Mutuwa, wato ‘Grim Reaper’, abin da ya firgita wasu daga cikin marasa lafiya da ma’aikatan asibitin. Amma abin da ya ƙara sanya lamarin zama abin mamaki shi ne yadda matashin ya musanta cewa yana kwaikwayon Mala’ikan Mutuwa, yana cewa a maimakon haka, yana kwaikwayon wani tsuntsu…
Read More