Labarai

“Ta rasu a ofishin ’yan sanda”: Yadda mutuwar jaruma Temitope Osoba ta sake tayar da hazo

“Ta rasu a ofishin ’yan sanda”: Yadda mutuwar jaruma Temitope Osoba ta sake tayar da hazo

Daga AISHA ASAS Sabon iƙirari kan mutuwar jarumar Nollywood, Temitope Osoba, ya sake jawo hankalin jama’a bayan wanda ya ce shi ne wanda za ta aura ya bayyana cewa an sanar da shi mutuwar jarumar ne a wani ofishin ’yan sanda da ke Ikorodu a Legas. Jaruma Osoba ta rasu tana da shekaru 40, kuma labarin mutuwarta ya fara yaduwa ne a ranar Laraba, 5 ga Agusta. Jarumar ta taɓa fitowa fili ta bayyana wa jama’a irin gwagwarmayar da ta yi da cutar kansa, bayan an gano tana fama da cutar kuma aka yi mata tiyata. Saboda haka, bayan rasuwarta,…
Read More
Cire tallafin mai ya ceci Nijeriya daga nauyin tiriliyan N53 — Shugaban NRS

Cire tallafin mai ya ceci Nijeriya daga nauyin tiriliyan N53 — Shugaban NRS

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Shugaban Hukumar Haraji ta Nijeriya (NRS), Zacch Adedeji, ya bayyana cire tallafin man fetur a matsayin ɗaya daga cikin mafi kyawun matakan da aka taɓa ɗauka a tarihin tattalin arzikin Nijeriya, yana mai cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya cancanci yabo saboda jajircewarsa wajen aiwatar da matakin. Adedeji ya bayyana haka ne a wata hira ta musamman da aka yi da shi a shirin Sunday Politics na gidan talabijin na Channels, inda ya kare sauye-sauyen tattalin arzikin gwamnatin Tinubu tare da cewa wasu daga cikin nasarorin da ake gani a halin yanzu sun samo asali ne…
Read More
Yadda Matatar Dangote ta sake ƙwace wa Amurka kasuwar man jiragen sama a Turai

Yadda Matatar Dangote ta sake ƙwace wa Amurka kasuwar man jiragen sama a Turai

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Matatar Mai ta Dangote ta ƙara ƙarfafa matsayinta a kasuwar makamashi ta duniya bayan da ta sake zama mafi girman mai samar da man jiragen sama ga nahiyar Turai na wata na biyu a jere, inda ta sake zarce Amurka wajen yawan kayayyakin da ake shigowa da su. A cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar a ranar Alhamis, ya bayyana cewa wannan nasarar ta sake tabbatar da irin tasirin da matatar ke ƙara samu a kasuwannin makamashi na duniya. Kamfanin ya ce, bayanan shigo da man jiragen sama na Turai, waɗanda kamfanin binciken kasuwar kayayyaki…
Read More
2027: Jam’iyyun adawa na yunƙurin haɗaka don neman ɗan takarar da zai ƙalubalanci Tinubu

2027: Jam’iyyun adawa na yunƙurin haɗaka don neman ɗan takarar da zai ƙalubalanci Tinubu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Manyan jam’iyyun adawa a Nijeriya sun fara sabunta ƙoƙarin haɗa kai domin kafa wata babbar ƙawance da za ta samar da dandali guda na siyasa da zai kalubalanci Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da Jam’iyyar APC a zaɓen Shugaban ƙasa na 2027. Sabon yunƙurin, wanda ƙungiyar G-100 ke jagoranta, na da nufin haɗa jam’iyyun African Democratic Congress (ADC), Peoples Democratic Party (PDP), Nigeria Democratic Congress (NDC), Peoples Redemption Party (PRP), Social Democratic Party (SDP) da Allied Peoples Moɓement (APM). Daga cikin ’yan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyun da aka ambata akwai Atiku Abubakar na…
Read More
Al’ummar Kano ba su tare da kalaman Sheikh Jingir – Kwankwaso

Al’ummar Kano ba su tare da kalaman Sheikh Jingir – Kwankwaso

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce kalaman da malamin addinin musulunci Sheikh Sani Yahaya Jingir ya yi na iya haifar da rarrabuwar kawuna a tsakanin al'ummar Nijeriya. A wata sanarwa da Kwankwaso ya wallafa a shafinsa na ɗ, ya jaddada cewa al'ummar Kano ba su tare da irin waɗannan kalamai na yunƙurin rarraba kawuna ba Ya ce ya damu matuƙa da kalaman da Sheikh Jingir ya yi a wani taro a Kano a ƙarshen mako. A ƙarshen makon nan ne kafar sada zumunta da ma kafafen yada labarai suka ɗauki ɗimi…
Read More

Zaɓen Osun: Adeleke ya yi wa ɗan takarar APC dukan sakwara a mazaɓarsa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja An sanar da Ademola Adeleke a matsayin wanda ya yi nasara a mazaɓarsa ta 009 da ke Abogunde/Sagba a Ƙaramar Hukumar Ede ta Arewa a zaɓen gwamnan Jihar Osun da aka gudanar ranar Asabar. A cewar sakamakon da malamar zaɓen yankin, Adebimpe Susan Dunsin ta sanar, Adeleke, wanda shi ne ɗan takarar jam'iyyar Accord Party kuma gwamna mai ci, ya samu ƙuri’a 421, wanda hakan ya sa ya yi nasarar kan sauran abokan karawarsa Ɗan takarar jam’iyyar mai mulki APC, Bola Oyebamiji, ya samu ƙura 29 kacal, yayin da na ADC, Najeem Salaam ya…
Read More

INEC ta fara ɗora sakamakon zaɓen gwamnan Osun a shafinta

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC, ta sanar da fara ɗora sakamakon zaɓen gwamnan Jihar Osun a shafinta na yanar gizo na IReV, inda tuni aka riga aka ɗora na mazaɓu guda 402 daga cikin 3,763 zuwa ƙarfe 4:03 na yammacin Asabar. Wannan adadi ya wakilci kaso 10.68 na jimillar mazaɓun ƙananan hukumomi 30 na faɗin jihar. An fara aikin ne bayan kammala zaɓe da fara tantancewa da ƙirgawa a mazaɓun sassan Osun. Shafin na IReV na bayar da dama ga al'umma, jam'iyyun siyasa, masu sanya ido da sauran masu ruwa da tsaki su yi…
Read More
’Yan jarida na iya gina ko rushe dimokuraɗiyya — Sarkin Dutse

’Yan jarida na iya gina ko rushe dimokuraɗiyya — Sarkin Dutse

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Sarkin Dutse na Jihar Jigawa, Dr Hameem Nuhu Sanusi, ya nuna damuwa kan yadda wasu mutanen da ba su da cikakken horo ko ƙwarewar aikin jarida ke kutsawa cikin sana’ar, yana mai cewa ayyukansu na lalata martabar aikin jarida. Sarkin ya bayyana hakan ne yayin da ya karɓi baƙuncin Shugaban ƙungiyar ’Yan Jarida ta Nijeriya (NUJ), Kwamared Alhassan Yahaya, tare da mambobin Majalisar Zartarwa ta ƙasa (NEC) ta ƙungiyar, waɗanda suka kai masa ziyarar ban girma a fadarsa da ke Dutse. Tawagar NUJ ta je Dutse ne domin halartar taron NEC na ƙungiyar da ake gudanarwa…
Read More
Tsohon ɗan dambe Prichard Colón ya rasu yana da shekaru 33

Tsohon ɗan dambe Prichard Colón ya rasu yana da shekaru 33

Tsohon dan damben Puerto Rico, Prichard Colón, ya rasu yana da shekaru 33, kusan shekaru 11 bayan wani mummunan faɗa da ya janyo masa zubar jini a kwakwalwa. Colón ya rasu ne ranar Alhamis, 13 ga Agusta, 2026, bayan ya shafe tsawon lokaci cikin wani yanayi na rashin cikakken sanin abin da ke faruwa a jikinsa sakamakon raunin da ya samu. Mahaifinsa kuma tsohon mai horar da shi, Richard Colón, ne ya sanar da rasuwarsa a wani saƙo da ya wallafa a Facebook. Kafin hatsarin da ya sauya rayuwarsa, Colón na daga cikin fitattun ‘yan damben da ake sa ran…
Read More
An naɗa tsohon jakadan Najeriya a Majalisar Ɗinkin Duniya uban ƙasar Besse

An naɗa tsohon jakadan Najeriya a Majalisar Ɗinkin Duniya uban ƙasar Besse

Daga MUHAMMAD SADISU ABUBAKAR Birnin Kebbi Mai martaba sarkin Gwandu Alhaji Muhammadu Iliyasu Bashar ya naɗa tsohon jakadan Najeriya a Majalisar Ɗinkin Duniya Farfesa Tijjani Muhammad Bande a matsayin Baraden Besse, uban ƙasar Besse, da ke Jihar Kebbi. Gwamnan Kebbi mai ci yanzu , Nasir Idris, tare da tsohon gwamnan jihar, Atiku Bagudu, wanda a yanzu shine ministan kasafin kuɗi da tsarin tattalin arziki, da kuma tsohon gwamnan jihar, Jakada Sa'idu Dakingari da kuma tsohon gwamnan jihar, yanzu kuma ɗan majalisar dattijai mai wakiltar Kebbi ta tsakiya, Muhammadu Adamu Alieru, sun halarci wurin bikin naɗin sarautar, wanda aka yi a…
Read More