Labarai

Arsenal da Man City za su kara a wasan Community Shield a gobe Lahadi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Lahadi, 16 ga watan Agusta, 2026 ne ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal za ta kara da Manchester City a wasan neman lashe kofin ƙasa, wato FA Community Shield na 2026. Hakan na zuwa ne ƙasa da mako guda da za a buɗe kakar wasannin Premier League ta ƙasar Birtaniya ta 2026/2027. Arsenal, wadda ta lashe Premier League a kakar da ta gabata, za ta kara da ƙungiyar Man City da ta lashe kofin FA Cup bayan ta doke Chelsea a watan Mayu. Ana buga wasan Community Shield ne dai a tsakanin ƙungiyar…
Read More

NFF ta fara binciken gazawar Super Falcons ta samun gurbi a gasar Kofin Duniya na 2027

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar kula Harkokin Ƙwallon Ƙafa ta Ƙasa NFF, ta kafa wani kwamiti da ta ɗora wa alhakin binciken ƙwaf akan matsalolin da suka sabbaba wa tawagogin Nijeriya na ƙasa rashin nasara musamman na gazawar Super Falcons samun gurbi a gasar Kofin Duniya na Mata ta 2027. Wannan mataki na zuwa ne jim-kaɗan da aka yi waje da Falcons a gasar Kofin ƙasashen Afirka (WAFCON) a wasan dab da na kusa da na ƙarshe da ci 1 da nema a hannun Kamaru da kuma ci 2 da 1 a wasan da Banyana Banyana ta Afirka…
Read More

Madugu ya yi wa NFF shaguɓe bayan Falcons ta gaza samun gurbin gasar Kofin Duniya na 2027

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Kocin Super Falcons ta Nijeriya, Justine Madugu ya haifar da cece-kuce bayan furta wasu kalamai na shaguɓe jim-kaɗan bayan rashin nasarar da tawagar ta yi a wasan neman gurbin shiga gasar Kofin Duniya na Mata ta 2027. Waɗannan kalamai sun haifar da alamomin tambaya kan ko kocin yana yi ne da Hukumar kula da Harkokin Ƙwallon Ƙafa ta Ƙasa (NFF) ta bayan fage ko hukumomin gudanar da wasanni ko kuma wasu masu hannu a gudanar da harkokin tawagar. A cewar Madugu: "kuna tsammanin za ku yi nasara, amma ba ku yi komai ba yayin…
Read More
Gidauniyar Mangal ta fara tantance masu lalurar fitsari domin yi masu magani kyauta a Katsina

Gidauniyar Mangal ta fara tantance masu lalurar fitsari domin yi masu magani kyauta a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gidauniyar Dahiru Bara'u Mangal ta fara aikin tantance marasa lafiyar da suka samu wannan dama, inda ake gudanar da gwaje-gwaje domin gano irin matsalar da kowanne mara lafiya ke fama da ita da kuma tantance waɗanda suke buƙatar aikin tiyata ko magani. Sama da mutane 120 ne ake sa ran za su amfana da aikin, wanda za a gudanar da shi kyauta ba tare da marasa lafiyar sun biya kuɗin magani ko aikin tiyata ba. Da yake bayyana yadda shirin yake, ɗaya daga cikin ’yan Kwamitin Amintattu na Gidauniyar Hussaini Kabir, ya bayyana cewa tun…
Read More
Gamayyar jam’iyyun siyasa takwas a Zamfara sun yi Allah wadai da taron IPAC

Gamayyar jam’iyyun siyasa takwas a Zamfara sun yi Allah wadai da taron IPAC

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Gamayyar jam'iyyun siyasa takwas a Jihar Zamfara ta nisanta kanta daga wani taron manema labarai da wasu mambobin gammayyar jam'iyyun siyasa IPAC reshen Jihar da ke ayyana kan su a matsayin shugabannin IPAC a jihar su ka yi. Da yake jawabi ga manema labarai a yau Asabar a Gusau, Ambasada Adamu Haruna Tsafe, ya ce ƙungiyar ta damu da wannan bayanin, wanda suka lura an yi shi ne da nufin cin zarafi ga manufofi da shirye-shiryen gwamnatin jihar. Gamayyar ta ƙunshi wakilan jam'iyyun siyasa na AA, NNPP, SDP, ZLP, AAC, LP, YPP da APP. A…
Read More
Zamfara: Jigo a APC ya fice daga jam’iyyar sakamakon rashin kawo ƙarshen ‘yan bindiga

Zamfara: Jigo a APC ya fice daga jam’iyyar sakamakon rashin kawo ƙarshen ‘yan bindiga

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Wani fitaccen ɗan jam'iyyar APC a ƙaramar hukumar Maradun, Hon. Muhammad Bello Yakubu Bakyasuwa, ya yi murabus daga jam'iyyar nan take, yana zargin gwamnatin tarayya da sakaci da rashin tsaro a jihar Zamfara. A cikin wata wasiƙar murabus da ya aike wa shugaban APC a Dosara/Birnin Kaya Ward, Bakyasuwa ya ce shawarar da ya yanke na ƙashin kansa ne da kuma rashin gamsuwa da gwamnatin APC ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Bakyasuwa ya yi nuni da ci gaba da kai hare-hare a Zamfara, yana mai cewa ya yi murabus ne saboda gazawar gwamnatin tarayya da…
Read More

‘Yan daba sun farmaki fadar basaraken Osun gabanin zaɓen gwamna

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja An zargi wasu 'yan daba da kai farmaki a fadar Aree na Iree, Oba Muritala Oyelakin a ranar Juma'a yayin da ake ƙasa da sa'o'i 24 da fara zaɓen gwamnan Jihar Osun. Al'amarin ya faru ne da misalin ƙarfe 2 na dare, wanda ya haifar da damuwa acikin al'umma kan tsaron masarautu da masu sarauta yayin zaɓen, wanda ke gudana a yau Asabar. Basaraken, yayin ganawa da manema labarai a ranar Juma'a, ya ce maharan sun je fadar tasa ne a wasu motoci biyu masu ƙirar Sienna, inda suka yi harbe-harbe a sama kana…
Read More

Zaɓen Osun: ‘Yan sanda sun magantu kan zargin mamaye gidan kakakin majalisar dokokin jihar

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Rundunar 'Yan sanda ta sanar da cewa ba ta tabbatar da zargin da Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Osun, Adewale Egbedun ya yi ba na cewa wasu mutane masu ɗamara sun mamaye gidansa a safiyar ranar Asabar yayin da masu zaɓe ke shirin kaɗa ƙuri'a a zaɓen gwamnan jihar da ke gudana. Wannan zargi ya haifar da fargaba kan halin tsaro acikin al'ummar jihar a safiyar zaɓen, inda aka samu wasu rahotanni da suka ce kakakin ya koka da misalin karfe 6 na safe wajen yin iƙirarin wasu mutane masu ɗamara sun kewaye gidansa. Saidai…
Read More

2027: Atiku ya maka Tinubu a kotu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya maka Shugaba Bola Ahmed Tinubu a gaban Babbar Kotun Tarayya, inda yake ƙalubalantar cancantarsa ta tsaya wa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027 da ke tafe. Atiku ya kuma buƙaci kotun da ta fayyace bayani akan ko Shugaba Tinubu da jam'iyyarsa APC, sun cancanci a soke cancantarsu ta shiga zaɓen. Haka kuma, tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya zayyano Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) a matsayin ɗaya daga cikin masu kare ƙarar. Daga cikin ababen da Atiku yake ƙorafi akansu akwai zargin yin amfani da…
Read More

NAHCON ta sanya farashin kujerar Hajjin 2027 da ranar rufewa

Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya NAHCON, ta sanar da adadin farashin kujerar aikin Hajjin 2027 da aka amince da su, waɗanda suka fara daga Naira miliyan 7.56 zuwa miliyan N7.88, bisa la’akari da yankin da mahajjata za su tashi. A sanarwar da NAHCON ta fitar a ranarJuma’a, ta ce Gwamnatin Tarayya ta amince da kudaden ne bayan tattaunawa da Ƙungiyar Hukumomin Jin Daɗin Alhazai na Jihohi da kamfanonin jigilar alhazai na Saudiyya, tare da la’akari da farashin canjin kuɗi da kuma halin da farashin ayyuka ke ciki. A ƙarƙashin sabon tsarin kudaden, maniyyatan da za su tashi daga yankin Maiduguri/Yola za…
Read More