15
Aug
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina 'Yan sanda sun daƙile yunƙurin hare haren 'yan bindiga da satar mutane a ƙauyen Fulalawa da ke ƙaramar hukumar Musawa a Jihar Katsina. A wata sanarwa jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sanda a Katsina DSP Abubakar Sadiq Aliyu,ya ce bayan samun bayanan sirri cewar 'yan bindiga ɗauke da manyan makamai sun Kai hari har da satar mutane a ƙauyen Fulalawa,nan take 'yan sanda da taimakon jami'an tsaro na CWC suka fara ɓarin wuta da ya tilastawa 'yan bindigan ja da baya,wasu a cikin su ana zargi sun gudu suna ɗauke da manyan raunuka.…
