15
Aug
Daga RABIU SANUSI a Kano Jihar Kano ta zama cibiyar wani muhimmin bincike da Cibiyar Nazarin Manufofi da Dabarun ƙasa ta Nijeriya (NIPSS) ke gudanarwa, domin tantance irin gudunmawar da jihar ke bayarwa wajen bunƙasa tattalin arzikin Nijeriya, samar da ayyukan yi da haɓaka harkokin kasuwanci. Tawagar NIPSS, wadda ta ƙunshi mahalarta Babban Darasin Gudanarwa na 48, Rukuni na ɗaya, ta fara ziyarar nazari ta tsawon mako guda a Kano, inda za ta tattauna da gwamnati, ’yan kasuwa da sauran masu ruwa da tsaki. Shugaban tawagar, mai ritaya Birgediya Janar Jimo, MNI, ya bayyana cewa binciken ya mayar da hankali…
