14
Aug
Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe Kwamishinan ƙananan hukumomi na Jihar Gombe, Barista Sani Ahmad Haruna, ya yaba wa malaman tsangaya na jihar bisa goyon bayan da suka bayyana wa Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya da ɗan takarar gwamnan jihar na jam’iyyar APC, Dakta Jamilu Isiyaku Gwamna a zaɓen 2027. Kwamishinan ya bayyana hakan ne a zantawarsa da manema labarai jim kaɗan bayan kammala wani babban taro da ƙungiyar malaman tsangaya ta jihar ta gudanar, inda malaman suka bayyana aniyarsu ta mara wa Dakta Jamilu Gwamna baya tare da tabbatar masa da ƙuri’u 150,000 a zaɓen 2027. Ya ce matakin malaman na…
