Labarai

Yadda Boko Haram da ISWAP ke yaƙar juna kan neman iko a Tafkin Chadi

Yadda Boko Haram da ISWAP ke yaƙar juna kan neman iko a Tafkin Chadi

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Rikicin da ya daɗe tsakanin ƙungiyar ISWAP da Boko Haram na ci gaba da sauya yanayin tsaro a yankin Arewa maso Gabashin Nijeriya. ƙungiyoyin biyu na fafatawa mai zafi domin mallakar yankuna, samun tasiri da albarkatu. Sabon artabu da aka ruwaito a ranar Juma’a, 7 ga Agusta, ya sake jawo hankali kan mummunan rikicin da ke tsakanin ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya, bayan rahotannin cewa mayaƙan ISWAP sun kai wani samame kan Bok Haram a yankin Bula Murge, cikin ƙaramar Hukumar Bama ta Jihar Borno, inda aka ce an kashe wasu manyan kwamandojin Boko Haram.…
Read More
2027: Tinubu, Atiku, Obi za su biya miliyan N150 kowanne kan allunan talla a Kuros Riba

2027: Tinubu, Atiku, Obi za su biya miliyan N150 kowanne kan allunan talla a Kuros Riba

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja ’Yan takarar shugaban ƙasa da suka haɗa da Bola Ahmed Tinubu, Atiku Abubakar da Peter Obi za su biya kuɗin Naira miliyan 150 kowanne domin kafa allunan tallan kamfen a Jihar Kuros Riba gabanin babban zaɓen 2027. Hukumar Kula da Allunan Talla da Alamu ta Jihar Kuros Riba (CRISSAA) ce ta bayyana sabon tsarin kuɗin tallan siyasa na waje da za a biya a jihar. Daraktan-Janar na hukumar, Ubong Sam, ya bayyana hakan ne yayin wani taron tattaunawa da Majalisar Shawarar Jam’iyyun Siyasa (IPAC) a Calabar, inda ya yi bayanin sabon tsarin kuɗaɗen. A…
Read More
Gwamna Yusuf ya amince da ƙarin albashi ga ma’aikatan jami’o’in Kano biyu

Gwamna Yusuf ya amince da ƙarin albashi ga ma’aikatan jami’o’in Kano biyu

Daga RABIU SANUSI a Kano Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da aiwatar da sabon tsarin ƙarin albashi ga ma’aikatan koyarwa da waɗanda ba na koyarwa ba na Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote da ke Wudil da Jami’ar Arewa maso Yamma ta Kano. An ɗauko sabon tsarin ne daga tsarin albashin da Gwamnatin Tarayya ta fara aiwatarwa a jami’o’in tarayya. Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ranar Litinin. Amincewar ta biyo bayan rahoto da shawarwarin wani kwamiti da Majalisar Zartarwar Jihar Kano ta…
Read More
Sojojin Nijeriya sun ce sun ceto fasinjoji 33 da aka sace a Zamfara

Sojojin Nijeriya sun ce sun ceto fasinjoji 33 da aka sace a Zamfara

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Rundunar sojin Najeirya ta ce dakarunta na Operation Fansan Yamma sun ceto mutum 33 da 'yanbindiga suka yi garkuwa da su a ƙaramar hukumar Tsafe da ke jihar Zamfara, bayan samun sahihan bayanai kan sace fasinjojin da ke tafiya ta yankin Magazu. Sanarwar da jami'in yaɗa labarai na rundunar, Laftanar Kanal Aliyu Danja, ya fitar ta ce sojojin tare da 'yan sanda a Tsafe sun samu bayanin lamarin ne da yammacin ranar 8 ga Agusta, 2026. Nan take dakarun suka nufi wurin da lamarin ya faru, inda suka ci karo da maharan suna tafiya…
Read More
An rushe kwamitin gudanarwar kamfanin rarraba wutar lantarki na Kaduna

An rushe kwamitin gudanarwar kamfanin rarraba wutar lantarki na Kaduna

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Nijeriya, NERC, ta rushe kwamitin gudanarwar kamfanin rarraba wutar lantarki na Kaduna Electric, sakamakon matsalar kuɗi da kuma gazawar kamfanin wajen cika wasu muhimman sharuɗɗa. NERC ta ce matakin ya fara aiki daga ranar 10 ga Agustan 2026, bisa tanade-tanaden sashe na 75 zuwa 79 na Dokar Wutar Lantarki ta shekarar 2023. Hukumar ta ce kamfanin ya tara bashin sama da naira biliyan 118.6 na wutar lantarki a watan Mayun 2026, lamarin da ya sa jimillar bashin da ke kansa ya kai kusan naira biliyan 456.5. NERC ta…
Read More

‘Yan bindiga sun halaka matafiya tara a Neja

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja 'Yan sanda sun gano wasu gawarwaki na mutane guda tara waɗanda ake zargin 'yan bindiga ne suka halaka su a akan hanyar Wawa zuwa Lumma da ke Ƙaramar Hukumar Borgu ta Jihar Neja. Kamfanin Dillancin Labarai (NAN) ya ruwaito cewa jami'an 'yan sanda da sojoji da aka tura yankin sakamakon aun labarin ne suka gano a ranar Talata. Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar wa NAN a Minna cewajami'an tsaron sun kwashe gawarwakin daga wurin, yayin da aka ƙara tsaurara ayyukan sintiri da bincika wuraren da ake zargin 'yan bindiga…
Read More
Gwamna Bala ya buƙaci sojoji su kafa sabuwar bataliya a Alƙaleri

Gwamna Bala ya buƙaci sojoji su kafa sabuwar bataliya a Alƙaleri

Daga MUAZU HARDAWA a Bauchi Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed, ya buƙaci Rundunar Sojin Nijeriya ta kafa ƙarin sansanonin sojoji na musamman a wasu yankunan jihar da ke fama da matsalar rashin tsaro, domin dakile ayyukan ’yan bindiga da sauran masu aikata laifuka da suka addabi al’umma. Musamman, gwamnan ya buƙaci kafa bataliya ta musamman a yankin Alkaleri, yana mai cewa ’yan bindiga na fitowa daga dazuzzukan yankin dauke da makamai tare da amfani da motoci masu yawa wajen gudanar da ayyukansu. Ya ce muhimmancin yankin ya ƙara kasancewa ne saboda dazuzzukan Alkaleri suna da kusanci da wasu…
Read More
Gwamnatin Kano ta ware filaye ga matasa 1,000 daga ƙananan hukumomi 44

Gwamnatin Kano ta ware filaye ga matasa 1,000 daga ƙananan hukumomi 44

Daga RABIU SANUSI a Kano Gwamnatin Jihar Kano ta ware filaye ga matasa 1,000 daga ƙananan hukumomi 44 na jihar, a wani muhimmin shiri da aka tsara domin ƙarfafa matasa, bunƙasa mallakar gidaje, samar da dukiya da kuma ba su damar samun makoma mai inganci. Da yake wakiltar Gwamna Abba Kabir Yusuf wajen rabon takardun filayen a Coronation Hall da ke Gidan Gwamnati a Kano, Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Farouk Umar Ibrahim, ya ce shirin ya nuna ƙudurin gwamnatin na samar wa matasa kadarori da damar dogaro da kansu ta fuskar tattalin arziki. Gwamna Yusuf ya bayyana cewa makomar Kano…
Read More
Nijeriya na buƙatar haɗin kai yanzu fiye da kowane lokaci – Idris

Nijeriya na buƙatar haɗin kai yanzu fiye da kowane lokaci – Idris

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, ya yi kira ga ’yan Nijeriya da su ɗaukaka tunaninsu sama da bambance-bambancen addini, ƙabila da siyasa, tare da haɗa kai wajen yaƙi da rashin tsaro da sauran ƙalubalen da ke fuskantar ƙasar. Idris ya yi wannan kiran ne ranar Talata a Abuja, yayin wani taron ƙasa da ƙasa mai taken “Bambance-bambance da Zaman Lafiyar Al’umma: Haɗin Gwiwa don Kyakkyawar Makoma”, wanda ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iƙamatus Sunnah (JIBWIS) ta shirya tare da haɗin gwiwar ƙungiyar ƙasashen Musulmi ta Duniya. Ministan ya ce bambance-bambancen…
Read More
Zaɓen Osun: Disu ya haramta wa Amotekun da sauran rundunonin tsaro shiga aikin tsaro a ranar zaɓe

Zaɓen Osun: Disu ya haramta wa Amotekun da sauran rundunonin tsaro shiga aikin tsaro a ranar zaɓe

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Sufeto-Janar  na ’Yan Sandan Nijeriya, IGP Olatunji Disu, ya haramta wa Rundunar Tsaron Yammacin Nijeriya, wato Amotekun, da sauran kungiyoyin tsaro na sa-kai da kamfanonin tsaro masu zaman kansu shiga ayyukan tabbatar da tsaron zaben gwamnan Jihar Osun da za a gudanar ranar Asabar. Haka kuma, IGP Disu ya sake jaddada haramcin amfani da jami’an tsaro dauke da makamai, masu taimaka wa ’yan siyasa da sauran mutanen da ba su da izinin yin hakan wajen raka ’yan siyasa ko manyan baki zuwa rumfunan zabe da cibiyoyin tattara sakamako a ranar zabe. A cikin wata…
Read More