Labarai

‘Yan bindiga sun sace mutum shida bayan halaka biyu a Katsina

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja An halaka mutane biyu sannan an yi garkuwa da wasu guda shida a Unguwar Aminu da ke Gundumar Kandarawa ta Ƙaramar Hukumar Bakori a Jihar Katsina. Haka kuma, wasu mazauna su huɗu sun samu raunukan harbin bindiga yayin harin, wanda ya auku a ranar Talata da dare, kamar yadda wani rahoton Daily Trust ya bayyana. Jaridar ta ce waɗanda aka halaka sune Ibrahim Sama'ila da Mashakuru Isa, inda tuni aka yi musu jana'iza a ranar Laraba kamar yadda addinin Musulunci ya tanada. Waɗanda aka sace a ɗaya gefen sun haɗa da maza uku da…
Read More
2027 lokaci ne da ya kamata ‘yan Nijeriya su saita makomar ƙasa — Obi

2027 lokaci ne da ya kamata ‘yan Nijeriya su saita makomar ƙasa — Obi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya yi kira ga ’yan Nijeriya da su saita irin alkiblar da suke son ƙasar ta bi gabanin babban zaɓen 2027. Obi ya yi kiran ne ranar Talata yayin da yake gabatar da jawabin fatan alheri a taron tattaunawar dimokuraɗiyya na gidauniyar Goodluck Jonathan na shekarar 2026, da aka gudanar a Bauchi. Ya ce ya kamata ’yan Nijeriya su fara tambayar kansu irin makomar da suke son gani a ƙasar, tare da haɗa kai wajen sauya abubuwan da suke ganin suna jefa ƙasar cikin koma…
Read More
An tsawaita wa’adin miƙa ƙudirin ’yan sandan jihohi

An tsawaita wa’adin miƙa ƙudirin ’yan sandan jihohi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Kwamitin Shugaban ƙasa kan Dokar Kafa ’Yan Sandan Jihohi ya tsawaita wa’adin karɓar takardun shawarwari da matsaya daga jama’a da masu ruwa da tsaki kan dokar da ake shirin samarwa. Kwamitin ya ce an tsawaita wa’adin ne domin bai wa ’yan Nijeriya da sauran masu ruwa da tsaki ƙarin lokaci su shirya tare da gabatar da shawarwari masu zurfi da inganci kan tsarin dokar. A cikin wata sanarwa da Shugaban Kwamitin, Femi Gbajabiamila, ya sanya wa hannu, an bayyana cewa sabon wa’adin gabatar da takardun shawarwari shi ne ƙarfe 5:00 na yamma ranar Juma’a,…
Read More
Firaministan Indiya ya gayyaci Tinubu taron shugabannin BRICS

Firaministan Indiya ya gayyaci Tinubu taron shugabannin BRICS

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Firaministan Indiya, Narendra Modi, ya gayyaci Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, zuwa taron shugabannin ƙasashen BRICS, wanda aka shirya gudanarwa a birnin New Delhi na ƙasar Indiya daga ranar 12 zuwa 13 ga Satumba. Gayyatar na zuwa ne a daidai lokacin da Indiya ke ƙoƙarin ƙara zurfafa dangantakarta da Nijeriya tare da bunƙasa haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen ƙasashen Kudancin Duniya, wato Global South. Babban Kwamishinan Indiya a Nijeriya, Abhishek Singh, ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a Abuja ranar Laraba. Singh ya ce, ana fatan Shugaba Tinubu zai jagoranci tawaga mai…
Read More

Masu haƙar ma’adinai bakwai sun rasu yayin da ƙasa ta rufta a Filato

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja 'Yan aikin haƙar ma'adinai guda bakwai sun rasa rayukansu bayan ƙasa ta haɗe da su a ƙauyen Kassa da ke Ƙaramar Hukumar Barkin Ladi ta Jihar Filato. Wani ɗan yankin mai suna Albert Ɗanlami ya shaida wa manema labarai cewa masu aikin sun haɗu da ajalinsu ne bayan da ƙasar wajen ta rufta akansu, lamarin da ya sa mazauna da sauran abokan aikinsu suka gaggauta yunƙurin ceto su. Ya ce, al'amarin ya haifar da firgici a ƙauyen yayin da mazauna suka gaggauta zuwa yankin domin bayar da agajin gaggawa kan al'amarin, inda a sanadiyyar…
Read More

Super Falcons ta rasa damar shiga gasar Kofin Duniya karo na farko a sama da shekara 30

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tarihin Nijeriya na shiga kowanne gasar Kofin Duniya ta mata tun da aka fara a 1991 ya haɗu da cikas bayan tawaga Super Falcons ta gaza samu damar shiga na 2027. A daren Alhamis wayewar Juma'a a Casablanca ne Banyana Banyana ta Afirka ta Kudu ta doke Nijeriya da ci 2 da 1, lamarin da ya sa 'yan Super Falcons ɗin suka gaza samun gurbi a gasar 2027 FIFA Women's World Cup. Da fari dai Super Falcons ta yi fatan farfaɗowa daga cire ta da aka yi a zangon wasannin dab da na kusa…
Read More

Ribaɗu ya jagoranci tawagar Nijeriya zuwa Amurka taron tattauna dabarun daƙile matsalolin tsaro

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara akan Harkar Tsaro (NSA), Nuhu Ribaɗu ya jagoranci wata tawaga da gwamnatin Nijeriya ta shirya domin zuwa ƙasar Amurka halartar taron haɗaka tsakanin ƙasashen biyu, wanda aka gudanar a Birnin Washington D.C. Zaman ya mayar da hankali ne akan haɗin kan lamuran daƙile ayyukan ta'addanci, nasarorin da aka samu zuwa yanzu da matakai na gaba da za ɗauka wajen ƙarfafa alaƙar tsaro tsakanin ƙasashen. An gudanar da taro ne a ranar Alhamis, wanda kuma ya biyo bayan ayyana Nijeriya a matsayin ƙasar da ake damuwa akanta (CPC) da…
Read More
Hukumar Hisbah ta kama wata budurwa kan zargin koyawa yara lalata a Katsina

Hukumar Hisbah ta kama wata budurwa kan zargin koyawa yara lalata a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina Hukumar Hisbah ta Jihar Katsina ta kama wata budurwa kan zargin koya wa wasu yara maza yadda zasu riƙa aikata lalata da junansu a ƙaramar hukumar Dutsinma da ke jihar Katsina. Bayanin haka na cikin wata sanarwa da hukumar Hisbah ta jihar Katsina, reshen Dutsinma ta fitar. A cewar sanarwar, hukumar ta kama wadda ake zargin bayan samun rahoton lamarin daga ofishin yankin Ƙadangaru da ke ƙaramar hukumar ta Dutsinma. Sanarwar ta ce, kwamandan Hisbah na ƙaramar hukumar Malam Shafi’u Ibrahim, ya karɓi rahoton tare da ɗaukar matakan bincike, inda jami'an hukumar P.I.H. Hamisu Sani…
Read More
Sanata Yar’adua ya yi na’am da komawar Mustapha Inuwa jam’iyyar APC a Katsina

Sanata Yar’adua ya yi na’am da komawar Mustapha Inuwa jam’iyyar APC a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Sanata Abdulaziz Musa Yar’adua mai wakiltar Katsina ta tsakiya a Majalisar Dattawa, ya bayyana farin cikinsa game da sauya shekar da tsohon sakataren gwamnatin Jihar Katsina, Dr. Mustapha Inuwa ya yi daga jam’iyyar African Democratic Congress, ADC, zuwa jam’iyyar All Progressives Congress, APC. A wata sanarwara da ya fitar, Sanatan ya bayyana dawowar Dr. Mustapha a matsayin babban karin ƙarfi ga jam’iyyar APC da kuma alamar ƙaruwar amincewar al’umma ga gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Dikko Umaru Raɗɗa. A cewarsa, "Na sami labarin dawowar babban ɗan’uwana, Dr. Mustapha Inuwa, zuwa jam’iyyar APC da…
Read More

Hukumar alhazan Kano za ta rufe karɓar kuɗin Hajjin 2027 a 25 ga Agusta yayin da ta ƙayyade farashi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Jigilar Alhazai ta Jihar Kano ta sanar da cewa Naira miliyan 7 ne ƙayyadadden farashin aikin Hajjin 2027 ga maniyyata dafa sassan jihar. Darakta-Janar na hukumar, Abubakar Ibrahim Matawalle ne ya sanar da haka a wata takarda, ranar Talata. A cewar hukumar, 25 ga watan Agusta, 2026 na nan a matsayin ranar ƙarshe ta biyan kuɗin rajistar Hajjin na 2027. "Baki ɗaya waɗanda ba su miƙa fasfo ɗinsu na ƙasa-da-ƙasa ba, su yi hakan kafin wa'adin ya cika. Kiyaye wa'adin na da muhimmanci wajen shigar da bayanai yadda ya dace da kuma tabbatar…
Read More