13
Aug
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Daracktocin hukumar tsaro na farin kaya na Arewa maso Yamma da ya ƙunshi jihohi 7 sun fara gudanar da taro a Katsina domin ƙara haɗin kai da ɓullo da shirin sabbin dabarun shawo kan matsalar tsaro a yankin. A jawabin sa Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Raɗɗa ya bayyana cewa matsalar tsaro da yadda ake tunkarar matsalar a jihohin Arewa maso Yamma yakamata ya zama bai ɗaya domin haka ya yaba wa hukumar DSS da sauka shirya wannan taro mai taken haɗa kai don yaƙar ta'addanci(United against Terror). Gwamnan ya yaba wa da haɗin kai…
