13
Aug
Daga JAMIL GULMA a Kebbi Gwamnatin jihar Kebbi ta jaddada ƙudirin ta na kulawa da iyalan 'yan sanda da suka rasu a bakin daga yayin artabu da 'yan ta'adda a ƙaramar hukumar mulki ta Sakaba. Ya yi wannan bayanin ne jiya a fadar gwamnatin jihar yayin da ya ke karɓar baƙuncin wata tawaga daga ofishin Sufeto Janar na 'yan sandan Nijeriya Mista Olatunji Disu ƙarƙashin jagorancin mataimakin Sufeto Janar Umar Dada don jajentawa gwamnati da kuma al'ummar jihar Kebbi. Gwamna Malam Nasir Idris ya jajentawa rundunar 'yan sanda tare da bayyana cewa rayuwar su ba ta tafi a banza ba…
