Labarai

Ficewar Obi daga ADC ta kawo ƙarshen damar lashe zaɓen sa a 2027 – Fayose 

Ficewar Obi daga ADC ta kawo ƙarshen damar lashe zaɓen sa a 2027 – Fayose 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon Gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya ce matakin Peter Obi na ficewa daga jam’iyyar ADC ya kawo ƙarshen damar da yake da ita ta lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027. Fayose ya bayyana hakan ne a wata hira da gidan talabijin na TVC News, inda ya ce ‘yan adawa sun raunana damar da suke da ita ta kayar da jam’iyyar APC, bayan da suka rabu suka bi hanyoyi daban-daban. Ya ce a lokacin da manyan ‘yan adawar suka kasance cikin haɗin gwiwar ADC, suna da damar yin gagarumar hamayya da APC, amma ficewar…
Read More
Manoma 40 sun rasu bayan kwale-kwale ya kife a Sakkwato

Manoma 40 sun rasu bayan kwale-kwale ya kife a Sakkwato

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Ana fargabar mutuwar mutane sama da 40 bayan wani kwale-kwale ɗauke da manoma da ma’aikatan gona ya kife a garin Gorau, da ke ƙaramar Hukumar Goronyo a jihar Sakkwato. Rahotanni sun ce mutanen na kan hanyarsu ne zuwa gonakin shinkafa domin gudanar da ayyukan noma, musamman girbin amfanin gona, lokacin da kwale-kwalen ya kife jim kaɗan bayan tashi daga bakin ruwa. Lamarin ya jefa fasinjojin da dama cikin ruwa, inda wasu suka nutse, yayin da ake ci gaba da gudanar da aikin ceto da neman waɗanda suka ɓace. Shaidu sun bayyana cewa sama da mutane 70…
Read More

Blueprint ta karrama Gwamnan Sakkwato kan shugabanci nagari

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnan Jihar Sakkwato, Dakta Ahmad Aliyu Sakkwato, ya lashe kyautar lambar yabo ta Kamfanin Jaridun Blueprint ta 2025 kan Shugabanci nagari, Sabunta Cibiyoyi da kuma Ci-gaba Mai ɗorewa, wanda ya biyo bayan cimma nasarori wajen ƙarfafa cibiyoyin gwamnati da gyare-gyare masu kyawawan tasiri a sassan jihar da aka samu a ƙarƙashin gwamnatinsa. Kwamishinan Ƙirƙira da Tattalin Dijital, Hon. Bashar Umar Kwabo ne ya wakilci gwamnan a taron Karramawar ta Blueprint Newspapers Limited, wanda aka gudanar a babban ɗakin taro na Bola Ahmed Tinubu da ke Abuja a ranar Talata. A yayin gabatar masa da…
Read More

‘Yan bindiga sun sace uwa da ɗa bayan halaka ɗan bijilante a Kaduna

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Wasu 'yan bindiga sun halaka ɗan bijilante da kuma sace wata mata tare da ɗanta yayin wani hari da suka ƙaddamar a ƙauyen Kyauta da ke yankin Millennium City a Jihar Kaduna. Ɗan bijilanten mai suna Mustapha Baba, ya gamu da ajalinsa ne a lokacin da maharan suka harbe shi, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwarsa yayin da yake karɓar magani a Asibitin Barau Dikko Specialist da ke Kaduna. Ɗan uwansa Yuzuf Baba ne ya tabbatar da faruwar al'amarin a wani rubutu da ya wallafa a shafin Soshiyal Mediya, inda ya ce harin ya…
Read More

‘Namu ‘ya’yan fa?’, iyayen Borno sun yi wa Tinubu magiya kwana 40 da ceto ‘yan makarantar Oyo

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Iyayen ɗaliban makarantar da aka yi awon-gaba da su a Jihar Borno sun yi magiya ga Shugaba Bola Tinubu da ya shiga tsakani domin ceto 'ya'yansu, inda suka koka kan cewa yayin da aka kai kwana 40 da ceto ɗaliban Jihar Oyo, nasu sun ɗauko hanyar kaiwa kwanaki 100 a hannun masu garkuwa da su. Manhaja ta ruwaito cewa, iyayen, waɗanda suke cikin alhini, sun yi wannan koke ne a yayin hira da gidan talabijin na News Central, inda suka yi ƙalubale cewa ya aka yi 'yan Oyo suka shaƙi iskar 'yanci amma kuma…
Read More

‘In sha Allahu hakan ba zai faru ba’: Fadar Shugaban Ƙasa ta yi wa Atiku martani kan alƙawarin dawo da tallafin fetur a 2027

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Fadar Shugaban Ƙasa ta caccaki kalaman ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar na cewa zai mayar da tallafin fetur idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban Nijeriya a 2027. Mai taimaka wa Shugaba Bola Tinubu kan Sadarwa da Wayar da Kan Al'umma, Sunday Dare a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, ya bayyana shirin Atikun a matsayin yunƙurin kwaɗaitar da 'yan Nijeriya domin su zaɓe shi. A 'yan kwanakin nan ne dai ɗan takarar na ADC ya ci alwashin maido da tallafin fetur matuƙar ya lashe zaɓen 2027, wanda…
Read More

HOTO MAI MAGANA: Gwamna Adeleke ya gabatar wa Tinubu shaidar lashe zaɓe a Abuja

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Talata Gwamna Ademola Adeleke ya gabatar wa Shugaba Bola Tinubu shaidar lashe zaɓe bayan nasara da ya samu a zaɓen gwamnan Jihar Osun da aka gudanar a ranar 15 ga Agusta. Adeleke tare da wasu jiga-jigan jam'iyyar Accord Party ne suka kai wa Tinubu ziyara a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja da misalin ƙarfe 5:25 na yamma domin nuna godiyarsu ga shugaban kan yadda aka gudanar da zaɓen bisa tsarin doka. Mai taimaka wa Shugaban Ƙasa, Dada Olusegun, ya ce Adeleke ne ya jagoranci tawagar domin yaba wa shugaban ƙasar kan…
Read More

DSS ta yi gargaɗin ‘yan ta’adda na shirin kai farmaki manyan makarantu a Sakkwato

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Tsaro ta Farin kaya (DSS) reshen Jihar Sakkwato, ta nuna damuwa kan wani rahoton leƙen asiri da ke nuna cewa 'yan ta'adda da ƙungiyoyin 'yan bindiga na shirin ƙaddamar da wasu hare-hare a manyan makarantu da ke faɗin jihar, inda ɗalibai, malamai, sauran ma'aikata da iyalansu suna cikin halin haɗarin a yi garkuwa da su. DSS ta fitar da saƙon ankararwar ne a wata takarda mai ɗauke da 18 ga Agusta, 2026, wadda ta gabatar ga gwamnatin Jihar Sakkwato kuma da aka sanya wa hannu a madadin daraktan tsaron jihar. A saƙon, mai…
Read More

Tsohon ministan tsaron Ukraniya ya nemi a yi zaɓen shugaban ƙasa duk da yaƙinsu da Rasha

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tsohon Ministan Tsaron ƙasar Ukraniya, Mykhailo Fedorov ya yi kira da a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa duk da yaƙin da ke tsakanin ƙasar da Rasha, a wani yanayi da za a kira da ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen siyasa da Shugaba Volodymyr Zelenskyy zai iya fuskanta tun bayan fara yaƙin a 2022. Fedorov mai shekaru 35, ya yi wannan kira ne a wani faifan bidiyo da ya fitar a ranar Talata, inda ya ce wajibi ne ƙasar ta dawo da tsarinta na dimukraɗiyya duk da cewa ana cigaba da gwabza yaƙi tsakaninta da…
Read More

Na hannun daman Trump ya faɗi a zaɓen fidda gwanin takarar gwamnan Florida

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Yayin da masu zaɓe suka shirya maye gurbin Gwamna Ron DeSantis mai barin gado, 'yan jam'iyyar Republican sun zaɓi na hannun daman Shugaban Donald Trump, yayin da Democrat suka zaɓi wani ɗan takara daban da ya sauya jam'iyya ya bar tafiyar GOP (Republican) saboda shugaban ƙasar. Saidai kuma masu goyon bayan Democrat sun sake nuna ƙarfinsu na cigaba da samun karɓuwa bayan Rep. Angie Nixon ya lashe zaɓen fidda gwanin ɗan takarar sanata. Amma biyu daga cikin 'ya'yan majalisa na jam'iyyar da suka tsaya takara a karon fari a sababbin gundumomi sun tsallake rijiya…
Read More