Labarai

Da Tinubu ya so da na taimaka masa APC ta lashe zaɓen Osun ‘ko ta halin ƙaƙa’  — Wike

Da Tinubu ya so da na taimaka masa APC ta lashe zaɓen Osun ‘ko ta halin ƙaƙa’  — Wike

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya ce da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi amfani da cikakken tasirinsa na siyasa wajen zaɓen Gwamnan Jihar Osun, da jam’iyyar APC ta lashe zaɓen. Wike, wanda har yanzu yake cikin jam’iyyar adawa ta PDP amma yana goyon bayan gwamnatin Tinubu, ya bayyana cewa Shugaban ƙasar ya bar zaɓen ya gudana ba tare da amfani da ƙarfin Gwamnatin Tarayya wajen neman nasarar APC ba. Wike ya bayyana hakan ne yayin da yake duba wuraren da ambaliyar ruwa ta shafa a Maitama, Abuja, inda ya ce da…
Read More
Zaɓen 2027: Tinubu da Atiku ba su halarci taron sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya ba

Zaɓen 2027: Tinubu da Atiku ba su halarci taron sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya ba

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja ‘Yan takarar shugaban ƙasa da shugabannin wasu jam’iyyun siyasa sun rattaba hannu kan Yarjejeniyar Zaman Lafiya ta ƙasa domin gudanar da kamfen na zaɓen 2027 cikin lumana, tare da yin watsi da tashin hankali, kalaman ƙiyayya, yaɗa labaran ƙarya da tayar da zaune tsaye kan kabilanci ko addini. An rattaɓa hannu kan yarjejeniyar ne a ranar Talata a Abuja, ƙarƙashin jagorancin kwamitin zaman lafiya na ƙasa wato National Peace Committee (NPC) tare da haɗin gwiwar The Kukah Centre, gabanin fara kamfen ɗin zaɓen 2027 a ranar Laraba, 19 ga Agusta. Sai dai wasu manyan…
Read More
Jihar Neja ta yi gargaɗin tsagewar madatsar ruwan Kaduna da barazanar ambaliya

Jihar Neja ta yi gargaɗin tsagewar madatsar ruwan Kaduna da barazanar ambaliya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja (NSEMA) ta yi gargadi kan rahotannin samun matsala da kuma tsagewar ginin Madatsar Ruwan Kangimi da ke ƙaramar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna, tana mai cewa lalacewar madatsar na iya jefa al’ummomin da ke ƙasa cikin haɗarin ambaliya. Darakta-Janar na NSEMA, Abdullahi Arah, ya bayyana damuwar hukumar a cikin wata sanarwa, inda ya yi kira da a gaggauta gudanar da cikakken binciken fasaha kan madatsar tare da ɗaukar matakan kariya. Ya ce lamarin na buƙatar kulawa cikin gaggawa musamman ganin cewa damina na ci gaba da…
Read More
Yadda Nijeriya ta dakatar da fasfo a wasu cibiyoyi bayan shekaru 62

Yadda Nijeriya ta dakatar da fasfo a wasu cibiyoyi bayan shekaru 62

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnatin Tarayya ta dakatar da samar da fasfo a cibiyoyin Hukumar Kula da Shige da Fice ta Nijeriya (NIS) da dama, inda ta koma tsarin samar da fasfo a cibiya guda ta zamani. Ministan Harkokin Cikin Gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, ya bayyana hakan ne ranar Alhamis yayin da yake duba sabuwar Cibiyar Samar da Fasfo ta Tsakiya (Centralised Passport Personalisation Centre) da ke hedikwatar NIS a Abuja. Ministan ya ce tun bayan kafa Hukumar NIS a shekarar 1963, Nijeriya ba ta taɓa samun cibiyar samar da fasfo guda ɗaya da ke kula da samar…
Read More
2027: Tsohon Sufeton ’Yan Sanda ne zai lashe zaɓen gwamnan Nasarawa – Ali Bagio

2027: Tsohon Sufeton ’Yan Sanda ne zai lashe zaɓen gwamnan Nasarawa – Ali Bagio

Daga JOHN D. WADA a Lafiya Jibrin Ali, wanda aka fi sani da Ali Bagio, kuma babban mai goyon baya da mai tara ƙuri’u na musamman na ɗan takarar kujerar gwamnan Jihar Nasarawa a ƙarƙashin Jam’iyyar Social Democratic Party (SDP), tsohon Sufeto-Janar na ’Yan Sandan Nijeriya, Alhaji Abubakar Mohammed Adamu, ya bayyana cewa ɗan takararsu ne kaɗai zai iya lashe zaɓen gwamnan jihar da za a gudanar a shekarar 2027. Bagio ya bayyana hakan ne a Lafia, babban birnin Jihar Nasarawa, yayin wata tattaunawa ta musamman da manema labarai kwanan nan. Ya musanta rahotannin da ke cewa ɗan takarar SDP…
Read More
An fara fafata yaƙin neman zaɓen 2027

An fara fafata yaƙin neman zaɓen 2027

*’Yan takara sun rattaɓa hannu kan yarjejeniyar lumana *Ya kamata kamfen ya zama gasa, ba yaƙi ba – Amupitan Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasar Nijeriya na 2027 ya fara ne a hukumance ranar Laraba, 19 ga Agusta, kamar yadda jadawalin da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) ta tanada ya nuna. Sai dai duk da fara wa’adin yaƙin neman zaɓen, manyan jam’iyyun siyasar ƙasar ba su nuna gaggawar fara gangamin neman ƙuri’u ba, yayin da wasu daga cikinsu ke ci gaba da shirye-shiryen kafa kwamitocin yaƙin neman zaɓe da tsara dabarunsu. Rahotanni sun nuna…
Read More
Majalisar zartarwa ta amince da ƙudirin cire laifin yunƙurin kashe kai daga cikin laifukan Nijeriya

Majalisar zartarwa ta amince da ƙudirin cire laifin yunƙurin kashe kai daga cikin laifukan Nijeriya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Majalisar Zartarwar Tarayya (FEC) ta amince da yin gyara ga Dokar Lafiyar ƙwaƙwalwa ta ƙasa domin cire yunƙurin kashe kai daga cikin laifukan da doka ke hukuntawa a Nijeriya. Ministan Lafiya da Jinƙai, Farfesa Ali Pate, ne ya bayyana hakan bayan taron FEC da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya jagoranta a Abuja ranar Laraba. Ya ce ƙudirin gyaran dokar, wanda za a miƙa wa Majalisar ƙasa domin ta yi masa duba da kuma zartar da shi, zai sauya yadda ake kallon mutanen da suka yi yunƙurin kashe kansu, daga hukunta su zuwa ba su…
Read More
Yadda na ƙi yarda Tinubu ya zama mataimakina — Atiku

Yadda na ƙi yarda Tinubu ya zama mataimakina — Atiku

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayyana yadda ya ƙi amincewa da buƙatar tsohon Gwamnan Legas, Bola Ahmed Tinubu, na zama abokin takararsa a matsayin mataimakin shugaban ƙasa, yana mai cewa bai amince da tikitin Musulmi da Musulmi ba saboda yana ganin hakan bai dace da muradun Nijeriya ba. Atiku ya bayyana hakan ne a cikin wata hira da aka yi da shi da harshen Hausa, wadda aka wallafa a shafin ɗ. Ya ce bayan ya samu tikitin takarar shugaban ƙasa, wasu dattawa biyar da suka haɗa da Tom Ikimi da Bisi Akande,…
Read More
Mata sun yi zanga-zanga kan kashe mutane 24 a Mangu

Mata sun yi zanga-zanga kan kashe mutane 24 a Mangu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wasu mata daga al’ummar Bin-Per da ke gundumar Kombun, ƙaramar hukumar Mangu a Jihar Filato, sun gudanar da zanga-zangar lumana kan kisan mutane 24 da wasu ’yan bindiga suka yi a yankin. Matan sun ratsa cikin al’ummar rike da ganyaye a kawunansu, yayin da suke alhinin waɗanda aka kashe tare da kira ga gwamnati da ta ɗauki matakan gaggawa domin kare rayukan jama’a daga sake fuskantar hare-hare. Zanga-zangar ta biyo bayan wani hari da ’yan bindiga suka kai wa al’ummar cikin dare, inda rahotanni suka ce sun shiga gidaje tare da kashe mazauna yankin.…
Read More
Yadda ‘yan siyasar Abuja suka jawo wa APC faɗuwa zaɓe a Osun — Gwamna Sule

Yadda ‘yan siyasar Abuja suka jawo wa APC faɗuwa zaɓe a Osun — Gwamna Sule

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamna Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa ya danganta rashin nasarar jam’iyyar APC a zaɓen gwamnan Jihar Osun da wasu daga cikin ’yan siyasar Abuja, yana mai cewa tsoma bakinsu ya taimaka wajen haifar da sakamakon. Gwamna Sule ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin da yake gabatar da takardun amincewar Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) ga ’yan takarar APC na kujerar gwamna da Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa a Lafia, babban birnin jihar. Sule ya ce da ba don tsoma bakin wasu ’yan siyasar Abuja ba, da APC ba ta rasa…
Read More