Ra’ayin Manhaja

Yaƙi da cutar mantuwa a Nijeriya

Yaƙi da cutar mantuwa a Nijeriya

Wani bincike na masana ya nuna cewa ’yan Nijeriya na cikin waɗanda suka fi fama da ciwon mantuwa a duniya. Ciwon mantuwa da ake kira ‘dementia’ na ɗaya daga cikin cututukan da ke barazana ga lafiyar bil’adama a duniya. Wata ƙungiyar da ta gudanar da binciken mai suna 'Alzheimer’s Disease International' ta ce, sama da mutum miliyan 40 ke fama da cutar a duniya ba tare da sun sani ba. Binciken ya kiyasta cewa kashi 75 cikin 100 na ɗauke da cutar ba tare da sun sani ba, kuma waɗannan alqaluma sun fi yawa a ƙasashen Nijeriya da Indiya da…
Read More
Magance matsalar rashin tsaro a Filato da sauran jihohi

Magance matsalar rashin tsaro a Filato da sauran jihohi

A kwanakin baya ne Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci jami’an tsaro da su gaggauta gurfanar da waɗanda suka aikata kisan gilla a wasu sassan jihohin Filato da Binuwai. Shugaban ya kuma bayyana tashe-tashen hankula a jihohin biyu a matsayin abin takaici. Baya ga haka, ya kamata jami’an tsaro su dakatar da tashe-tashen hankula a yankin Arewa maso Yamma da Kudu maso Gabas da sauran sassan ƙasar nan. Mummunan hare-haren da aka kai a Jihohin Filato da Binuwai sun haddasa asarar rayuka da lalata gidaje. Tun a ranar 15 ga watan Mayu ne aka fara zubar da jini a…
Read More
Buƙatuwar a dawo da kwalejojin horar da malamai

Buƙatuwar a dawo da kwalejojin horar da malamai

Akwai karin maganar Hausawa da ke cewa ‘kowa ya tuna bara, to bai ji daɗin bana ba.’ Mun kawo wannan karin magana ne saboda batun da mu ke son yin magana a kai, duk da mun taɓa dogon rubutu a kansa a watannin baya, wanda ya shafi harkar ilimi a ƙasar nan, musamman a nan Arewaci. A wancan rubutun mun kawo bayanai masu ilimantarwa game da yadda harkar ilimin Firamare ke neman taɓarɓarewa a Arewacin ƙasar nan, inda muka nuna cewa ba wani abu ba ne ya jawo haka illa watsi da gwamnatocinmu suka yi da Kwalejojin horar da Malamai,…
Read More
Matsalar matsananciyar yunwa a Nijeriya

Matsalar matsananciyar yunwa a Nijeriya

An yi hasashen cewa 'yan Nijeriya miliyan 25 na iya fuskantar matsananciyar yunwa tsakanin watan Yuni zuwa Agustan 2023 (lokacin bazara) idan ba a ɗauki matakan gaggawa ba don magance matsalar. Mutane dai na ganin cewa, tsadar man fetur ne babban ummul kaba'sin tsadar abinci da ake fama da ita a Nijeriya, wanda hakan zai saka al'ummma da dama cikin matsananciyar yunwa. Asusun kula da ƙananan yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) ya nakalto Cadre Harmonise a watan Oktoba na shekarar 2022, wani bincike na abinci mai gina jiki ƙarƙashin jagorancin gwamnati da Majalisar Ɗinkin Duniya, yana mai nuni da…
Read More
Ranar yaƙi da cutar Sikila a Nijeriya

Ranar yaƙi da cutar Sikila a Nijeriya

A Nijeriya, an ware ranar 19 ga watan Yunin kowace shekara domin tunawa da ranar cutar sikila ta duniya. Ana bikin ranar ne don wayar da kan jama'a na duniya kowace shekara da nufin havaka ilimin jama'a da fahimtar cutar sikila da ƙalubalen da marasa lafiyar da danginsu da masu kula da su ke fuskanta. Kafin mu san ya cutar ta ke, dole mu fara sanin yadda ake kamuwa da ita. Jini wanda ake gani a zahiri idan mutum ya ji ciwo ko kuma ya yanke jikinsa yana ɗauke da abubuwa iri daban–daban, kamar su 'plasma', 'Red Blood Cells' (RBC),…
Read More
Ƙaddamar da majalisa ta goma da ƙalubalen da ke gabanta

Ƙaddamar da majalisa ta goma da ƙalubalen da ke gabanta

A ranar 13 ga watan Juni, 2023, ne aka rantsar da Majalisar Dokokin Tarayya ta 10 a Abuja, tare da zaɓen sabon Shugaban Majalisar Dattajai da Kakakin Majalisar Wakilai bayan fafatawa mai zafi a takarar waɗannan muƙamai. A Majalisar Dattijai, Sanata Godswill Akpabio ne ya samu nasarar lashe zaɓen zama shugaban majalisar inda ya kayar da abokin takararsa Abdul'Azizi Yari. Nan ta ke kuma aka rantsar da shi. Sanata Ali Ndume na cikin waɗanda suka goyi bayan zaɓen Sanata Akpabio. Hakazalika, Honarabul Tajudeen Abbas wanda shi ne zaɓin jamiyyar APC, ya zama Kakakin Majalisar Wakilai ta 10. Majalisar Dokokin ta…
Read More
Nijeriya na cikin ƙasashe 12 mafi cigaba a Afirika

Nijeriya na cikin ƙasashe 12 mafi cigaba a Afirika

Wani rahoto na baya-bayan nan da Insider Monkey ta fitar ya nuna cewa, Nijeriya ba ta cikin jerin ƙasashe 12 da suka fi samun ci gaba a nahiyar Afirka. A cewar rahoton mai taken, “Ƙasashe 12 Mafi Cigaba a Afirka”, Afirka na ɗaya daga cikin nahiyoyin da suka fi arziki a duniya wajen samar da albarkatun ƙasa. Abin ban mamaki kuma, nahiyar na ɗaya daga cikin yankuna mafi ƙarancin ci gaba a duniya. Ƙasashen da suka shiga jerin sun yi amfani da albarkatun ƙasarsu wajen inganta tattalin arzikinsu. Irin waxannan ƙasashe su ne; Ghana, Zimbabwe, Masar, Maroko, Afirka ta Kudu,…
Read More
Ajandar sabuwar gwamnatin Nijeriya

Ajandar sabuwar gwamnatin Nijeriya

Ranar 29 ga watan Mayu, rana ce da aka daɗe ana jira na ficewar gwamnatin Muhammadu Buhari da kuma bikin rantsar da Bola Ahmed Tinubu. Ana ta muhawarar ko gwamnatin da shugaban qasa Muhammadu Buhari ya jagoranta ta cika alƙawuran da ta ɗauka ko akasinta. Duk da ma dai gwamnatin ta yi ƙoƙarin kawo sauyi a fannonin ababen more rayuwa, kama daga gadar Neja ta Biyu zuwa aikin titin jirgin ƙasa da gina tituna. Akwai tabbacin cewa gwamnatin Bola Tinubu za ta yi fama da tattalin arziki mara kyau, ƙasa mai rabe-raben kawuna da kuma tsarin tsaro mai sarƙaƙiya. Abin…
Read More
Batun ƙarin albashin likitoci

Batun ƙarin albashin likitoci

Buƙatar da likitoci suka yi na neman a ninka masu albashinsu ninki biyu, ya sake dawo batun yanayin aikin likitoci a Nijeriya. Likitocin sun ɗora buƙatarsu kan taɓarɓarewar tattalin arzikin ƙasar. Wannan ya haɗa da ƙarancin darajar Naira da illar da ta ke yi wajen tsadar rayuwa a ƙasar. Sun koka da cewa, duk da cewa an yi yarjejeniya da gwamnati don sake duba tsarin albashin da ake biyansu (CONMESS), wanda aka yi nazari a baya sama da shekaru 10 da suka wuce, gwamnati ta kasa magance matsalar. Don haka sun ba gwamnati wa'adin makonni biyu don magance buqatunsu ko…
Read More
Batun bautar da ƙananan yara a Nijeriya

Batun bautar da ƙananan yara a Nijeriya

Akwai wani al'amari mai matuƙar tayar da hankali da ban tausayi kan yadda ake amfani da yara masu ƙananan shekaru maza da mata don yin aiki ko bauta a gidaje da sauran wurare da suka haɗa da shaguna, otel-otel, wuraren kwana na manyan makarantu ko ɗakunan kwanan ɗalibai a jami’o’i. Akasarin yaran ’yan ƙasa da shekaru 15 ne kuma ana ɗaukarsu ne da nufin yin aikace-aikacen da suka haɗa da shara, wanke-wanke, wanki, goge-goge, ɗebo ruwa da rainon jarirai da kula da yayayyun yara da makamantansu. Mafi yawan yaran ana kawo su cikin birni daga ƙauyuka lokaci zuwa lokaci, ta…
Read More