30
Apr
Ga waɗanda ke yawan kiran a yi yaƙi a Nijeriya su kalli abinda ke faruwa a Sudan. Tun a ƙarshen makon da ta gabata ne tashe-tashen hankula suka ɓarke a Sudan. Ƙarar harbe-harbe a Khartoum babban birnin Sudan da jirage masu saukar ungulu sun yi ta harba makamai a wuraren zaman jama'a, tsawon ƙarshen mako ana gwabza ƙazamin faɗa tsakanin sojoji da dakarun sa-kai. Asalin faɗan shi ne rikicin da ya daɗe ana takun-saka tsakanin manyan hukumomin soja biyu na ƙasar. Wato asalin sojin Sudan wadda ita ce rundunar soja ta gwamnatin ƙasa baki ɗaya, sai kuma rundunar sa kai…
