31
Dec
Kamar dai yadda kowa ya sani ne cewa, akwai matuƙar gayar muhimmanci ga Gwamnatin Nijeriya ta sake duba batun bunƙasa harkokin noma a ƙasar nan, duba da rawar da ɓangaren ke takawa wajen ci gaban tattalin arzikin ƙasa da samar da wadataccen abinci. Ayyukan noma su ne ginshiƙi kuma babbar hanyar da za ta iya jure kowace irin kwaramniya ga ci gaban ƙasa tare da al’ummarta baki ɗqaya. Noma babbar abu ce a Nijeriya, ana ma kallon cewa ita ce sana’ar da ta fi kowace sana’a muhimmanci, wacce idan babu ita rayuwar ma sam-sam ba za ta yiwuwa ba. Haka…
