25
Mar
Matakin da Ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) ta yanke na tsawaita yajin aikin da ta fara har na tsawon makonni takwas, ya dagula wa ɗalibai, iyaye da kuma masu ruwa da tsaki a harkar ilimi lissafi, domin yajin aikin zai ƙara dagula al'amuran ilimi a jami'o'in ƙasar nan. Da ya ke yin biris da yadda harkar ilimi da tarbiyya ke durƙushewa a sanadin yajin aikin malaman jami’o’i, shugaban ASUU na yanzu, Farfesa Emmanuel Osodeke, wanda ya bayyana yajin aikin na watanni biyu a makon da ya gabata, ya bayar da hujjar cewa, “bayan ɗaukar rahotanni kan ayyukan da manyan jami’an gwamnati…
