19
Jun
A ranar Talata, 14 ga Yuni, 2022, ce ta yi daidai da Ranar Bada Tallafin Jini ta Duniya (WBDD). Da farko dai an yi bikin ne a shekara ta 2005, wannan rana ta musamman ta duniya ta kasance ƙarƙashin jagorancin Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), da ƙungiyar agaji ta Red Cross da Red Crescent don gode wa waɗanda suka bada gudunmawar jininsu don ceto rayukan bil'adama ba tare da neman a biya su ba. Jaridar Blueprint Manhaja ta duba muhimmancin wannan batu na bada jini, fargabar da wasu ke bayyanawa kan wannan al'amari da kuma yadda wataƙila za a sake…
