Ra’ayin Manhaja

Gangamin bukukuwan Maulidi

Gangamin bukukuwan Maulidi

Al'ummar Musulmi da dama a Nijeirya sun bi sahun sauran ’yan uwansu a faɗin duniya wajen murna da zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad (Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.) Musulmai da dama sun yi amannar cewa a watan Rabiu'l Awwal, aka haifi Annabi Muhammad (SAW). A irin wannan rana ce Allah (SAW), ya yi wa halittarsa kyautar da ta fi kowacce irin kyauta daraja wato Manzon Allah SAW, kamar yadda Musulunci ya bayyana. Al'ummar Musulmai dai kan yi hidima a wannan lokaci, kamar a Nijeriya musamman a jihohin arewacin ƙasar, makarantun allo ko na Islamiyya kan shirya…
Read More
Batun Naira biliyan 13.3 da aka ware don aikin ‘yan sandan al’umma

Batun Naira biliyan 13.3 da aka ware don aikin ‘yan sandan al’umma

Sanarwar da Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya yi kan cewa, ya amince da ware Naira biliyan 13.3, don fara aikin 'yan sanda na al'umma a cikin jihohi 36 na ƙasar da Babban Birnin Tarayya Abuja yana nuna jajircewar shugaban wajen tabbatar da cewa, ya yi duk abin da ya yi alƙawarin zai aiwatar kafin ya bar gadon mulki. Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a Abuja a wani taron bita na kwanaki biyu na duba ayyukan Ministoci wanda aka shirya don tantance ci gaban da aka samu don cimma muhimman abubuwan da gwamnatinsa ta sa a gaba,…
Read More
Jan kunnen da Sanusi ya yi kan tattalin arzikin Nijeriya

Jan kunnen da Sanusi ya yi kan tattalin arzikin Nijeriya

Hasashen da tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Khalifa Muhammad Sanusi ya yi, cewa tattalin arzikin Nijeriya zai durƙushe nan ba da jimawa ba, kira ne ga manajojin tattalin arzikin ƙasa da masu tsara manufofi da su hanzarta cikin dabara don kaucewa faruwar hakan. Sanusi, ya kuma bayyana cewa, dogaro da ɗanyen man da aka ɗora kan tattalin arzikin ba shi da makoma kuma ba a nemansa a duniya baki ɗaya. Da yake jawabi a taron ƙoli na shida na masu saka hannun jari na Kaduna, bayan ƙaddamar da shirin ci gaban jihar daga 2021 zuwa 2023, don mayar da…
Read More
Kafa dokar hana kiwo barkatai da cikas da ke ciki

Kafa dokar hana kiwo barkatai da cikas da ke ciki

Kafafen yaɗa labarai sun rawaito cewa, Gwamna Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna ya yi gargaɗi game da siyasantar da rigimar hana kiwo a fili, inda ya mayar da martini kan wannan doka da cewa, ba kafa dokar ba ne abu mai muhimmanci, aiwatar da dokar ne ba zai yiwu ba. Da ya ke zantawa da manema labarai ranar Talata bayan wata ganawa da jami’an jam’iyyar APC a sakatariyar jam’iyyar ta ƙasa da ke Abuja, Gwamna El-Rufai ya ce, duk da cewa akwai buƙatar makiyaya su daina yawo da dabbobi kamar yadda suka saba, mafita ba shi ba ne kafa dokokin…
Read More
Batun ‘yan Kaduna mutum miliyan 2.1 da suke fama da matsanancin talauci

Batun ‘yan Kaduna mutum miliyan 2.1 da suke fama da matsanancin talauci

A cikin ‘yan kwanakin nan, Rijistar Jama'a ta Jihar Kaduna (RRR) da aka saki ta nuna cewa, mazauna karkara, manoma masu zaman kansu da kuma matalauta marasa ilimi a jihar sun kai 2,051,972 daga cikin iyalai 524,424 da aka rubuta a cikin Rajistar Jama'a ta Jihar, sannan kuma ga sauran yawan matalauta da gidajen marassa galihu (PVHH). Wannan, haƙiƙa labari ne mai ban tausayi na halin da qasar ke ciki. Halin da ake ciki ko shakka babu ya bayar da tabbacin shigar Gwamnatin Tarayya, don rage matsanancin talauci a Nijeriya zuwa mafi ƙaranci. Shugabar Gudanarwa na SOCU, Kwamitin tsare-tsare da…
Read More
Hatsarin kasa kaya a gefen titi

Hatsarin kasa kaya a gefen titi

Kwanan nan, Hukumar Babban Birnin Tarayya Abuja ta yi gargaɗi mai tsanani ga ‘yan kasuwa da ke da ɗabi’ar mayar da kafaɗun manyan tituna wajen baje kolin tallata kayansu da su guji irin waɗannan ayyukan da ba su dace ba, wanda hakan kuma ke ƙara haddasa cunkoson zirga-zirgar ababen hawa. Rundunar haɗin gwiwa na Minista kan Kula da zirg-zirgar ababen hawa (MTTM), ƙarƙashin jagorancin Ikharo Attah, ta yi wannan gargaɗin a madadin FCT yayin da take kan bincike a Kasuwar Nyanya, kafaɗun hanya da hanyoyin da ke yankin. Ikharo ya ce, tawagarsa ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba…
Read More
Abubuwan lura a bayanin Sarkin Musulmi kan manyan matsalolin Nijeriya

Abubuwan lura a bayanin Sarkin Musulmi kan manyan matsalolin Nijeriya

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III, ya bayyana takaicinsa ga irin yadda rashin fahimtar juna tsakanin 'yan Nijeriya ke ƙara ta’azzara, inda ya ce, wannan shi ne babban barazanar da ƙasar ke fuskanta, ya na mai cewa, don Nijeriya ta samu zaman lafiya, dole ne 'yan ƙasa su so juna. Bayanin ya na tabbatar da furucin Shugaba Muhammadu Buhari kan babbar matsalar ƙasar, sarkin yana nuni da cewa tare da fahimtar cewa, 'yan Nijeriya za su yi haƙuri da juna, domin zaman lafiya ya samu wajen zama a ƙasar. Sarkin, wanda ya yi magana a lokacin taron ƙungiyar…
Read More
Kauce wa mace-mace lokacin haihuwa

Kauce wa mace-mace lokacin haihuwa

A cikin ’yan kwanakin nan, Asusun Ba da Agajin Gaggawa na Majalisar Ɗinkin Duniya kan kula da mata da ƙananan yara (UNICEF) ya yi ƙasa sosai a ɓangaren kiwon lafiya, inda a cikin kowane minti 10 na rana, mace 'yar Nijeriya na rasa ranta sakamakon matsalolin da ke da alaƙa da juna biyu. A matsakaici, kusan mata 52,560 ke mutuwa kowace shekara yayin da suke da ciki ko lokacin haihuwa.Kimanin kashi hamsin cikin ɗari na mata masu juna biyu da yara an yi imanin za su mutu ba tare da wani dalili ba a hannun masu aikin asibiti da ba…
Read More
Kasuwanci: Matakan dawo da martabar Kano da Buhari da Ganduje ke bi

Kasuwanci: Matakan dawo da martabar Kano da Buhari da Ganduje ke bi

Ƙaddamar da aikin aikin shimfiɗa layn dogo daga Kano zuwa Kaduna, wanda Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari a kwanan nan da kuma ƙaddamar da gada mai hawa uku, wacce Gwamnatin Jihar Kano a ƙarƙashin jagorancin gwamnan jihar, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, alama ce ta yadda Buhari da Ganduje ke fafutukar ganin sun dawo da martabar Kano a idanun duniya bakiɗaya ta fuskar kasancewar ta jagabar kasuwanci a yankin Afrika ta Yamma. Layin dogon na daga cikin wani ɓangare na aikin tabbatar da shimfiɗa shi daga Kano zuwa Legas, inda a ka fara aikin shimfiɗa gadar jirgin ƙasa ta zamani daga Abuja…
Read More
Matasa da madafun iko a Nijeriya

Matasa da madafun iko a Nijeriya

Daga NASIR S. GWANGWAZO A wata hira da a ka yi da tsohon Shugaban Mulkin Soja na Nijeriya , Janar Ibrahim Badamasi Babangida mai ritaya, a cikin makon jiya lokacin bikin zagayowar ranar haihuwarsa, ya yi iƙirarin cewa, bai dace a ƙara bai wa duk mutumin da ya wuce shekara 60 a duniya da haihuwa mulkin Nijeriya a zaɓen Shugaban Ƙasa da ke tafe na 2023 ba. Kalaman nasa sun janyo cece-kuce, amma fa ababen dubawa ne ƙwarai da gaske! A Nijeriya, tarihi ya na cigaba da maimaita kansa, inda a ke mayar da matasan ƙasar saniyar ware a duk lokacin…
Read More