06
Nov
A ranar 23 ga Oktoba, 2022, Amurka da Birtaniya suka yi gargaɗi kan yiwuwar a kai harin ta'addanci a Abuja, Babban Birnin Tarayyar Nijeriya, musamman kan gine-ginen gwamnati, wuraren ibada da makarantu, da dai sauransu. Gwamnatin Birtaniya ɗin ta ƙara da cewa hare-haren na iya zama kan mai-uwa-da-wabi kuma zai iya shafar muradun ƙasashen yamma da ma wuraren da masu yawon buɗe ido ke ziyarta. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Nijeriya ke yaƙar masu tayar da ƙayar baya da sunan addini a yankin Arewa maso gabas, amma a watan Yuli ƙungiyar IS ta ɗauki alhakin wani samame…
