15
Jan
A cikin rahotonta na baya-bayan nan, Cibiyar Kula da Cututtuka ta Nijeriya ta sanar da jimillar mutane 19,228 da ake zargin sun kamu da cutar kwalara, ciki har da mutuwar mutane 466 a shekarar 2022. A ra'ayin wannan jarida, wannan lamari ne mai firgitarwa da ya kamata gwamnati ta ɗauki nauyinsa daqile shi a kowane mataki. Kwalara cuta ce da ake saurin kamuwa da ita da ta ke haifar da gudawa da amai. Ana kamuwa da ita daga najasa ta hanyar gurvataccen abinci, abin sha, da rashin tsafta, kuma yana haifar da rashin ruwa a jikin ɗan adam. Yawan masu…
