DCP Abba Kyari: Ko ya dace ’Yan Arewa su yi koyi da ’Yan Kudu?

Daga NASIR S. GWANGWAZO

A ’yan kwanakin nan babu abin da a ke tattaunawa a Arewa da ma Kudancin Nijeriya kamar batun fallasar da ya ke faruwa a Ƙasar Amurka, wanda ya shafi ɗan Nijeriya kuma fitaccen matashin ɗan sanda, wanda ya yi matuƙar suna wajen yaƙi da aikata miyagun laifuka mai muƙamin Mataimakin Kwamishina ’Yan Sandan Nijeriya, wato DCP Abba Kyari. Badaƙalar ta samo asali ne daga binciken da Hukumar Binciken Aikata Miyagun Laifuka ta Amurka, wato FBI, ta gudanar kan fitaccen mai amfani da soshiyal midiya ɗin nan kuma ɗan asalin Nijeriya mazaunin Dubai mai suna Ramon Abbas, wanda a ka fi kira da Hushpuppi, inda binciken binciken ya nuna cewa, CSP Kyari ya na da alaƙa da shi kan wata damfara da ya tafka.

Shi dai Hushpuppi ya yi ƙaurin suna a duniya wajen tafka ta’asar damfara, musamman ta yanar gizo. Hakan ya sanya Hukumar FBI ta fara bincike a kan sa da ma dukkan mutane da ya ke ta’ammali da su, don tattara bayanai, don kama shi da kuma gurfanar da shi a gaban kuliya. Sakamakon binciken na FBI ne ya kai ga ambaton Kyari tare da sanya shi a jerin mutanen da a ke zargi aikata ha]in baki wajen tafka ta’asar. Ba Abba Kyari kaɗai wannan bincike ya sarƙo ba; har da wasu mutane uku daban.

Tun daga lokacin da fallasar ta faru a makon jiya lokacin da FBI ta gabatar da bayananta ga kotun Amurka, wanda ya nuna cewa, a cikin waɗanda ta ke tuhuma akwai CSP Kyari kuma hukumar ta nemi Nijeriya da ta bayar da shi gare ta, domin gurfana a gaban kuliya, sai kace-nace da cece-kuce suka ɓarke a fa]in Nijeriya. Bayanai sun nuna cewa, mafi yawan ’Yan Arewa ba su ji daɗin wannan lamari ba.

A taɗaice ma dai sun fito ne su na kare shi Abba Kyari, kamar yadda mafi yawan ’Yan Kudu su ka fito su na kare Nnamdi Kanu da Sunday Adeyemi, wanda a ka fi sani da Igboho. Shi dai Kanu ɗan ƙabilar Igbo daga yankin Kudu maso Gabas ne mai jagorantar rajin kafa ƙasar Biyafara, yayin da shi kuma Igboho ɗan ƙabilar Yarabawa daga Kudu maso Yamma ne mai jagorantar rajin kafa ƙasar Yarabawa.

Dukkansu su biyun, wato Igboho da Kanu, a na tuhumar su da laifin cin amanar ƙasa da assasa kisan gilla a Nijeriya. A lokacin da ’yan ƙabilarsu daga Kudu ke kare su, ’Yan Arewa na ganin laifin aikata hakan, su na masu ganin cewa, kamata ya yi a bar doka ta yi aiki a kansu. Ma’ana; idan an kama su da laifi, to a yanke mu su hukunci gwargwardon laifin da su ka aikata. Idan kuma kotu ba ta iya kama su da laifi ba, to ƙyale su. Wato dai a yi adalci kurum! Da yawan ’Yan Arewa na ganin beken ’Yan Kudu da idanunsu ya rufe, su ka kasa ganin girman irin laifukan da a ke zargin Igboho da Kanu da aikatawa. Ƙarara a na zargin ’yan waɗancan ƙabilu ko yanki da nuna tsananin son kai a kan ’ya’yansu.

A yanzu kuma katsam sai ga shi a na tuhumar ɗan Arewa, wato Kyari, da aikata wani laifi na haɗin baki da aikata ta’asar damfara. A fili ta ke cewa, mafi yawan masu kare shi ’yan yankinsa ne. Daga dukkan alamu ba su la’akari da laifin da a ke zargin sa da aikatawa, illa dai kawai ba su yarda a tuhumi nasu ba. Kamar yadda ’Yan Kudu ke kallon lamarin Kanu da Igboho a matsayin wata maƙarƙashiya, su ma ’Yan Arewa gani su ke yi ita ]in a ke yi wa Kyari, wanda a baya ya taɓa jagorantar rundunar nan ta yaƙi da aikata muyagun laifuka mai suna SARS, wacce daga baya a ka rushe ta bayan ta janyo koke-koke.

A nan, abin da ya kamata ’Yan Arewa su gane shi ne, koda yake dai laifin da a ke tuhumar Abba Kyari da aikatawa ko kusa bai kai irin wa]anda a ke tuhumar Igboho da Kanu ba, amma laifi duka laifi ne, kuma kada ɗan Arewa ya manta da cewa, a manyan ɗabi’un da a ka fi sanin sa da shi, akwai yakana, kara da alkunya. Masana tarihi na ganin cewa, rashin son kai irin na ɗan Arewa ne ya wanzar da Nijeriya a matsayin ƙasa ɗaya, kuma ya ba ta nasarorin da ta samu ko’ina a duniya. ’Yan Arewa ne su ke iya daidaitawa tare da hukunta nasu daidai da wanda ba nasu ba.

A mulkin ɗan Arewa ne ka]ai a kan zargi Shugaban Ƙasa da fifita yankin da ba nasa ba, kamar yadda wasu ke zargin Shugaban Ƙasa na yanzu, Muhammadu Buhari, da fifita yankin Yarabawa a kan hatta yankin da ya fito na Arewa maso Yamma. Wannan ɗabi’a ta ’Yan Arewa ba dolontaka ba ce, ba kuma rashin sanin ya kamata ba ne, illa kawai matuƙar adalci da halin girma.

Kazalika, ya kamata ’Yan Arewa su gane cewa, shi DCP Kyari ba zargin sa a ke yi da aikata damfara kai-tsaye ba, a’a, a na zargin sa ne da cewa, Hushpuppi ya yi amfani da kusancinsa da shi ya sanya shi ya kama wani, wanda su ka yi damfara tare, amma ya yi kwana da kuɗin, ya hana shi Hushpuppi. Don haka ne a ke zargin ya yi amfani da alaƙarsa da Kyari ya kama ma sa shi, ya matsa shi har sai da ya fito ma sa da wasu maƙudan kuɗi, inda har ya aika wa Kyarin maƙudan kuɗi a matsayi cin hancin da rashawar aikin da ya yi ma sa.

A wajen jami’an Amurka wannan ba ƙaramin kuskure ba ne, domin na farko dai Kyari bai taɓa yin aikin ƙwarewa kan fannin damfarar yanar gizo ba, haka nan ma ba aikin da ofishinsa ya ke yi ba kenan, domin ofishinsa na kula da abin da ya shafi mayar da martani kan ayyukan ta’addanci da makamantansu ne a ƙarƙashin Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya. Don haka su ke kallon matakin da ya ɗauka na shiga cikin waccan rigima a matsayin ta yiwu ya na da hannu a irin ayyukan da Hushpuppi ya ke tafkawa. Kun ji wani tsautsayi! Shi dai DCP Kyari ya yi iƙirarin cewa, babu wani lulluɓaɓɓen abu tsakaninsa da Mista Ramon Abbas.

Za a iya cewa, a Nijeriya wannan laifi da a ke zargin Abba Kyari da aikatawa ya zama ruwan dare. Wato yin amfani da wani kusanci da ɗan sanda ba baƙon abu ba ne. Amma kash! a ƙasa irin ta Amurka lamari ne mai girman gaske! Sai dai kuma adalci ya na iya wanzuwa a shari’un ƙasar. Don haka ko da Kyari ya gurfana a gaban kotun Amurka, zai yi wahala a hukunta shi kan abin da bai aikata ba. Abin nufi a nan shi ne, adalci kaɗai zai samu. Ma’ana; kotu za ta yanke hukunci ne gwargwadon gamsassun shaidun da ta gamsu da su.

A nan, ya kamata ɗan Arewa ya sani cewa, barin aikata ƙananan laifuka wasarairai da a ka yi ne ya ke mayar da rayuwar ’Yan Nijeriya baya. Tabbas a bisa la’akari da abubuwan da a ka sani a zahiri, za a iya cewa, Malam Abba Kyari jarumin ɗan sanda ne, wanda ya ke yin iyaka ƙoƙarinsa wajen ganin ya tabbatar da cewa, ’Yan Nijeriya su na iya yin bacci mai nauyi a gidajensu, musamman yadda ya ke faɗi-tashin ganin ya kamo ’yan ta’adda da sauran masu aikata miyagub laifuka.

Amma idan har da gaske ne ya na da hannu a ƙarƙashin ƙasa kan yadda a ke cutar da mutane ta hanyar damfara a cikin gida da ƙasashen duniya a na ɓata wa Nijeriya da ’Yan Nijeriya suna a idanun duniya, yanke ma sa hukuncin da ya dace da shi, shi ne abin da zai fi amfanar hatta su kansu ’Yan Arewa, domin su ma ’Yan Nijeriya ne, kuma wataƙila hakan zai zama izina ga sauran jami’an da cin hanci da rashawa ya dabaibaye zukatansu!