Sakamakon Jarrabawar JAMB da barazanar ilimi a Nijeriya

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja

Kwanan nan ne Hukumar Kula da Shirya Jarrabawar Shiga Manyan makarantu a Nijeriya (JAMB) ta saki sakamakon jarrabawar ɗalibai na zangon 2020/2021, sakamakon da ya ja hankali kuma ya ɗaga hankali a faɗin ƙasar, saboda yadda ɗalibai suka faɗi warwas a jarrabawar.

Sakamakon jarrabawar ya nuna cewa, a cikin ɗalibai 6,944,368 da suka zauna jarrabawar, guda 973,384 ne kacal suka tsallake shingen shiga jami’a. Hakan ya na nuni da cewa, kashi 14 cikin 100 ne kacal suka haye maki 180 da hukumar ta gindaya a matsayin shingen da ɗalibi zai haye, kafin ya samu damar shiga jami’o’in ƙasar. Haka na nufin cewa, adadin ɗalibai har guda 5,970,984 sun fa]i warwas a jarrabawar kenan, wanda adadin ya zo daidai da kashi 86 cikin 100 na baki]ayan adadin ɗaliban da suka zauna jarrabawar. Babu ko shakka wannan ba ƙaramin tashin hankali ba ne ga duk ƙasar da ta san me ta ke yi!

Duk da cewa, bayan sakin sakamakon jarrabawar, an yi ta samun cece-kuce tsakanin ɗaliban da suka zauna jarrabawar da ita Hukumar JAMB, wacce suka zarga da canja manhajar tsare-tsaren kwasa-kwasan da za a zauna jarrabawar a kai. To, amma hukumar ta fito ta na mai ƙaryata zargin, inda ta dawo da laifin ta ɗora shi kan yaran.

To, amma ko ma dai mene ne dalilin faruwar wannan al’amari, hakan ya na nufin cewa, Nijeriya na fuskantar barazana da mummunan rikici a fannin ilimin ƙasar, rikicin da an daɗe a na hasashen faruwarsa. Babbar matsalar ita ce, duk ƙasar da ta ke fuskantar matsalar harkokin ilimi, hakan ’yar manuniya ce da ke nuna cewa, akwai yiwuwar za a samu tarin matasa da ba su zuwa makaranta, kamar yadda Hukumar Yara ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta sanar da cewa, sama da yara miliyan 10 ne ba su zuwa makaranta a Nijeriya.

A matakin rayuwa, daga yara sai matasa, sannan tsofaffi. Idan har yara miliyan 10 ba su zuwa makaranta a yanzu, to ana sa ran nan da shekara 10 masu zuwa za a samu zunzurutun matasa miliyan 10 da ba su je makaranta ba kenan.

Idan za a iya samun matasa miliyan 10 cur tsantsar jahilai a ƙasa, to babu makawa rashin aikin yi sai ya ta’azzara, talauci sai ya yi ƙamari, wanda hakan zai kai su ga shiga aikata ayyukan laifuka tun daga ƙanana har zuwa gunduma-gunduman laifuka.

Bugu da ƙari, za a iya yin amfani da su wajen aikata ko waɗanne irin miyagun laifuka kama daga na siyasa zuwa na addini zuwa na tattalin arziki ko ma na ta’addanci, domin za su fi sauƙin sarrafawa ga masu mugun nufi.

Bugu da ƙari, kafin ma a kai wancan lokaci ba na shekara 10 masu zuwa, faɗuwar jarrabawar na nuni da taɓarɓarewar harkokin ilimin ƙasar. Idan ba a yi taka-tsantsan ba an tashi an farka, matasan da za su rasa ci gaban karatu, za su iya zama ƙasurguman masu aikata laifuka nan gaba kaɗan.

Yanayin yadda ayyukan aikata laifuka suke ta’azzara a ƙasar yana gwada cewa, an so a makaro, inda hatta Gwamnan Jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, a kwanan nan ya yi iƙirarin cewa, aikata laifuka ya kai minsharrin a faɗin Nijeriya. Ita ma Al}alin Alƙalan Jihar Bauchi, Mai Shari’a Hajiya Rabi’a Umar, ta yi wani hannunka mai sanda kan yadda ta ke fargabar bisa yadda yara ƙananan ke yawaita aikata laifuka.

Kada mu manta, waɗannan gogaggun mutane guda biyu su na riƙe da muƙaman da za su iya sanin abubuwa da yawa, waɗanda ba kowa ne zai iya ganin su ba. Gwamna mai ci ya na riƙa karɓar rahoton tsaro a kullum, ita kuma alƙali a kowacce rana a na kawo shari’u daban-daban gabatna masu nasaba da aikata laifuka.

Abin lura a nan shi ne, ba kasafai masu riƙe da irin waɗannan muƙamai ke fitar da bayanan da su ka samu ba a bainar jama’a. A mafi yawan lokuta su na iya fitar da wani kaso mai matuƙar ƙaranci ne daga abin da su ka sani. To, idan har ka ji su na yin bayani na tsaro irin wannan, haƙiƙa za a iya cewa, ba ƙaramin kai wa minsharrin al’amarin ya yi ba, idan mu ka bi ta bakin Ganduje.

Don haka wajibi ne a yi la’akari da fannin ilimi, a tashi tsaye wajen ceto shi, domin ya na da alaƙa matsalolin yanzu da waɗanda