Ra’ayin Manhaja

Ambaliyar ruwa da ƙarancin abinci a Nijeriya

Ambaliyar ruwa da ƙarancin abinci a Nijeriya

Farashin kayayyakin abinci ya yi tashin goron-zabi a Nijeriya musamman a yankin kudancin ƙasar sakamakon matsalar ambaliyar ruwa wadda ta haifar da cikas wajen safarar abincin daga arewacin ƙasar zuwa kudanci, al'amarin da ke ƙara jefa jama'a cikin halin ni-’yasu. Ambaliyar wadda ta yi sanadiyar mutuwar mutane 600 tare da raba miliyan biyu da muhallansu, ta haddasa asara ga 'yan kasuwa da ke safarar hajojinsu daga Arewa zuwa kudanci sakamakon yadda ta mamaye hanyoyin da motoci suka saba ratsawa. A cikin wata sanarwa da ta fitar a baya-bayan nan, Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi nuni da cewa, ana sa ran…
Read More
Gargaɗin yiwuwar harin ta’addanci daga Amurka da Ingila

Gargaɗin yiwuwar harin ta’addanci daga Amurka da Ingila

A ranar 23 ga Oktoba, 2022, Amurka da Birtaniya suka yi gargaɗi kan yiwuwar a kai harin ta'addanci a Abuja, Babban Birnin Tarayyar Nijeriya, musamman kan gine-ginen gwamnati, wuraren ibada da makarantu, da dai sauransu. Gwamnatin Birtaniya ɗin ta ƙara da cewa hare-haren na iya zama kan mai-uwa-da-wabi kuma zai iya shafar muradun ƙasashen yamma da ma wuraren da masu yawon buɗe ido ke ziyarta. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Nijeriya ke yaƙar masu tayar da ƙayar baya da sunan addini a yankin Arewa maso gabas, amma a watan Yuli ƙungiyar IS ta ɗauki alhakin wani samame…
Read More
Dakatar da yajin aikin ASUU

Dakatar da yajin aikin ASUU

A kwanakin baya ne Ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) ta dakatar da yajin aikin da ta kwashe watanni 8 tana yi, wanda ta fara a ranar 14 ga watan Fabrairun 2022. ASUU ta bayyana cewa ta janye yajin aikin ne biyo bayan shiga tsakani da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, Kakakin Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila, da sauran ’yan Nijeriya masu kishi ƙasa suka yi da kuma umarnin kotun ɗaukaka ƙara na neman mambobinta da su koma bakin aiki. Kotun ɗaukaka ƙara ta amince da hukuncin da ƙaramar kotun ta bayar tare da umurtar ƙungiyar ASUU da ta bi hukuncin da ƙaramar kotun…
Read More
Matsalar rashin lafiyar ƙwaƙwalwa a Nijeriya

Matsalar rashin lafiyar ƙwaƙwalwa a Nijeriya

Likitocin masu taɓin hankali a Nijeriya sun yi kira da a ɗauki matakin gaggawa don daƙile wannan mummunan matsala a ƙasar. A kiyasin su, ɗaya daga cikin ’yan Nijeriya huɗu, wato sama da miliyan 50, na fama da tavin hankali. Likitocin masu tavin hankali ne suka bayyana hakan a zaman wani viangare na ayyukan bikin Ranar Kiwon Lafiyar Ƙwaƙwalwa ta Duniya (WMHD) na 2022. Ana tunawa da WMHD kowace shekara a ranar 10 ga Oktoba don wayar da kan jama'a game da lafiyar ƙwaƙwalwa a duk faɗin duniya da kuma haxa kai don tallafawa waɗanda ke da matsalar tavin hankali.…
Read More
Nijeriya a matsayin ƙasar da ke fama da yunwa a duniya

Nijeriya a matsayin ƙasar da ke fama da yunwa a duniya

Rahotanni daga Majalisar Ɗinkin Duniya sun nuna cewa sama da mutane miliyan 113 a faɗin ƙasashe 53 ne suka fuskanci matsananciyar yunwa a shekarar da ya gabata tare da rikici, annobar sauyin yanayi da kuma matsalolin tattalin arziki wanda ke haddasa rikicin abinci. Aƙalla ’yan Nijeriya miliyan 25 ne ke fama da yunwa, yayin da mutane miliyan 9.3 ke fama da matsanancin ƙarancin abinci, dai-dai lokacin da ƙasar ke tsaka da fama da tashen-tashen hankula na masu ɗauke da makamai. Nijeriya na fuskantar rikici daga kowane ɓangare, wanda ke ke daƙile hanyoyin cigaban ƙasar. Ba wai helkwatar talauci ta duniya…
Read More
Nijeriya a 62: Har yanzu akwai jan-aiki a gaba

Nijeriya a 62: Har yanzu akwai jan-aiki a gaba

Yayin da Nijeriya ke cika shekara 62 da samun ’yancin kai, abin takaici har yanzu ƙasar na fama da matsaloli da ɗimbin alƙawuran da ba a cika ba. Matsalar rashawa da cin hanci ne dai babban ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta, al’amarin da ya haifar da kusan dukkannin matsalolin da ‘yan ƙasar ke fama da su. Lokaci ya yi da za a sake yin nazari a kan hanyar da za a bi wajen samun ingantacciyar ƙasa ta dimokuraɗiyya da kuma tsara mafi kyawun hanyar cigaba. Wannan tafiya ta kasance mai wahala tun daga farko. Misali shekaru shida bayan samun ’yancin…
Read More
Ajandar ’yan takarar shugaban ƙasa

Ajandar ’yan takarar shugaban ƙasa

A ranar 28 ga Satumba, 2022 ne aka fara yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na 2023 a hukumance. Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), a baya-bayan nan, ta fitar da sunayen ’yan takara 18 da ta wanke don tsayawa takara. Sun haɗa da ’yan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC mai mulki, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu; jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar; jam'iyyar Labour Party (LP), Peter Obi; jam’iyyar New Nigerian People’s Party (NNPP), Alhaji Musa Kwankwaso da sauransu. A bayyane ya ke cewa Obi, Atiku da Tinubu ne ke kan gaba a zacen da ke tafe. Kowanne daga…
Read More
Buƙatar kafa rundunar ’yan sandan jihohi

Buƙatar kafa rundunar ’yan sandan jihohi

Bayan kwashe shekaru masu yawa, majalisar wakilan Nijeriya ta yi nisa wajen aiki a kan ƙudurin dokar da za ta halatta kafa 'yan sandan jihohi domin shawo kan matsalolin rashin tsaro da suka adabi ƙasar. Da alamu dai an kama hanyar kawo ƙarshen tirje-tirje da ma tayar da jijiyar wuya, a kan wannan batu da aka kwashe lokaci mai tsawo ana ja-in-ja a kan halaccinsa ko akasin haka. Sakamakon Matsalar tsaro da ake fama da shi a faɗin ƙasar nan, gwamnonin jihohin Arewa 19 ƙarƙashin Ƙungiyar Gwamnonin Arewa (NGF) da kuma Ƙungiyar Sarakunan Gargajiya ta Arewa (NTRC) sun yi kira…
Read More
Kusantowar yaƙin neman zaɓen 2023

Kusantowar yaƙin neman zaɓen 2023

Nan da kwanaki kaɗan za a fara gangamin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa a hukumance. Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), wacce ke da hurumin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓe, ta sanya ranar 28 ga watan Satumba domin fara gudanar da ayyukan. Zaven 2023 na da matuƙar muhimmanci ga ɗorewar dimokaraɗiyyarmu da ƙasa baki ɗaya. Tuni dai yanayin siyasa ya tashi yayin da 'yan takarar shugaban ƙasa ke yin alƙawura da yawa. Ƙasar na cikin tsaka mai wuya saboda ɗimbin ƙalubalen da ta ke ci gaba da fuskanta. Saboda ƙaruwar rashin tsaro, talauci da rashin aikin yi, an…
Read More
Shirin daƙile ta’addanci don samar da tsaro a makarantu

Shirin daƙile ta’addanci don samar da tsaro a makarantu

A kwanakin baya ne dai rahotanni suka ce gwamnatocin jihohi da hukumomin tsaro da ma’aikatu sun yanke shawarar haɗa ƙarfi da ƙarfe domin magance ta’addanci da nufin samar da ingantaccen tsaro a makarantu. Manufar ita ce a motsa masu ruwa da tsaki don ba da gudummawa ga shirin, don samar da kuɗaɗe da samar da ingantaccen ilimi a Nijeriya. Baya ga samar da tsaro a makarantu ga yara, haka kuma don a rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a Nijeriya. An fara ƙaddamar da shirin ne mai suna ‘Safe school initiative’ a ranar 7 ga Mayun 2014, don…
Read More